Daudar Gora Book 2 Page 54
Cak numfashinsa ya tsaya da ga kaikawon da yake a ƙirjinsa. Kalmar *_a matsayin MATARKA_* ɗin nan tafi kowacce matuƙar ratsasa har tsakkiyar kai fiye da komai data faɗa, duk da suma sauran kalaman nasa nada wani muhimmanci da nasu tasirin. Amma a zahiri bai ko motsa ba,
yana dai kallonta ne a ƙasan ido kamar ya samu wani television. Shiru na tsawon wasu sakanni kamar masu sauraren saukar ruwan saman, sai kuma ya ɗago kaifafan idanunsa dai-dai da ɗago nata itama, cikin kallon ido cikin ido da wata sarƙaƙaƙƙiyar muryar da fitarta bai canja taushin ainahin muryarsa mai sanyi da nutsuwa ba ya furta, “Mi kika sani game da ni? A bayan burin da kika shigo da shi masarauta ta?”.
Kamar bazata motsa ba sai kuma ta motsa lips ɗin ta a hankali. Daurewa tai bata nuna ko gezau ba, itama ta zuba nata idanun da yanayinsu ke wani irin canja kala-kala maisa tsigar jikinsa tashi cikin nasa da ƙyau. Tai ɗan murmushi mai sanyi da ya nema ɗauke fitar numfashinsa a baɗininsa, janyewa tai gefe kaɗan fuskarta har lokacin da murmushin, “Sanin wani abu game da kai abu ne mai wahalar gaske ga baƙon zaman wannan gidan. Sai dai kai da kanka ya kamata ka duƙufa sanin komai a kanka, idan kuma ka sani ka ke shanyewa ka tuna kai shugaba ne. Haƙƙoƙin biliyoyin mutane ne a ƙarƙashinka, idan ka tauye ɗaya da gangan sai ALLAH ya tambayeka koda da ƙwayar zarra ne, inaji a raina kai ba mutum bane irin mutanen da tunaninsu ke a takure waje guda, in har bakai kake aikata laifin da mafiya al’ummar ƙasar nan ke kallonka da shi ba na tabbata kasan masu aikata wasu a ciki koda kaɗan ne, dan inba haka ba banga dalilin da zaisa su dinga farautar rayuwarka ba irin haka a matsayinsu na makusantanka”.
(Ya arrahaman) ya faɗa a zuciyarsa. Karo na farko ana faɗa masa gaskiyar da kowa ke shakkar tunkararsa a kanta hatta da wanda suke sama da shi a shekaru. Amma gashi yarinya ƙaramar da a haihuwar kaji ya haifeta yau tana jaddada masa shi ɗin wanene. Tsarge masa komai take a yanda ya jima yana buƙatar ji daga bakin wani koda mahaifiyarsa ne. Magana mafi dukan zuciyarsa itace ta ƙarshe. Ana farautar rayuwarsa kuma makusantansa. Yes ya jima da sanin wasu a makusantan sa na bibiyar rayuwarsa, kuma mahaifinsa ya fargar da shi hakan tun yana raye, amma a yau sai yaji kalmar daga bakinta ta sake girma matuƙa garesa. Kallonta yake cikin ido a wani irin yanayin da ke neman sarƙe fitar numfashinsa. Muryarsa a wani irin sanyaye ya furta, “Sune suka baki guba ki bani?”.
Shiru kamar bazatace komai ba, sai kuma ta ɗago ta ɗan kallesa. (To Miya rage kuma? Ai bataga amfanin cigaba da ɓoye masa ba) dan haka kai tsaye kawai ta jinjina masa kanta. “Ni nasan baka buƙatar sai na maimaita komai, domin ban ɓoye komai a zamana gidan nan ga Ajmaal ba, hatta randa nake neman dafin macizai ido rufe na sanar masa, shiyyasa har yanzu zuciyata taƙi daina mamakin miyasa kasha madarar tunda har kaga saƙon kuma…”
Wani murmushi ne ya nema suɓuce masa a hankali, sai dai bai yarda ya bayyana akan fuskarsa ba ya hadiye kayansa yana mai lumshe idanunsa da launinsu ya canja baki ɗaya. Kamar bazai tanka ba sai kuma ya sake buɗe idanunsa ya sauke a kanta cikin wani irin kasalallen kallo da ya tilastata rissinar da nata.
“A ranar banga saƙonki ba dan bana cikin ƙasar nan”.
Ɗagowa tai da sauri ta dubesa. Idanunta a ware cikin rawar harshe ta ce, “Kamar ya baka cikin ƙasar nan? Bayan matarka an mata kisan gilla a tsakanin, hakama tsohon da kowa ke tabbatar da jayayyar da yay da kai ce tasa ka ɓaddashi. Kana nufin kuma da gaske kai ne Ajmaal ɗin dai?”.