Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 51

Sponsored links

Sosai fitinar yarinyar nan ke bashi mamaki, a fuska bazaka taɓa tunanin halayyarta ba, dan tanada suffar mutane masu sanyin hali da rashin son yawan magana ma, sai dai inta buɗe baki ko kanari albarka ya kada ita. Rigimarta ta musamman ce sama da duk ta wani rigimamme da ya sani a tsayin rayuwarsa. Lips ɗinsa ya ɗan laɓe cike da sake tsuke fuska magana can ƙasan maƙoshi a fisge ya furta, “Akwai phone a side drawer, zaki iya magana da Mammy game da abubuwan buƙatarki, idan kuma zaki online shopping ne da kanki fine. Da akwai card tare da ita” ya ƙare maganar yana ɗan matsawa ga table ɗin dake ɗauke da takardun da bata san na minene ba ya ɗauka pen. Ɗan rubutu yay a takarda ya tako har gabanta ya ajiye batare da ya sake cewa komai ba ya juya zai bar ɗakin.

“Jazakallahu khairan”.

Ta faɗa a hankali, lumshe idanu yay batare da yace komai ba ya cigaba da tafiyarsa. Kamar wadda aka tsikara ta miƙe zumbur. Kaɗan ya rage tai tuntuɓe da lallausan carpet ɗin gaban gadon ALLAH dai ya bata sa’ar tsallakewa ta cimmasa. Yana ƙoƙarin ɗaura hannunsa kan handle ɗin ƙofar sai ganinta yay a gabansa kamar wata aljana. Mar-mar ta ɗan yi da idanunta tana motsa pink lips ɗinta a marairaice. “Indai fita ta wuce iya nan sashenka ka haƙura kar kayi Pleaseee”.

 

Idanunsa ya tsura mata da wani irin kallo da ta kasa bama fassara, dole ta risinar da nata tana ɗan wasa da bazar veil ɗin abayar jikinta da tai mata matuƙar ƙyau kasancewar blue black. Itama dai tashi tai kawai ta ganta bata san daga ina ba, amma tasan dai shine ya ajiye kamar yanda ya ajiye mata jiya. Idanun ya sauke a hankali kan hanun nata fari tas da babu wani datti a ƙunbunan suma. Kamar bazai ce komai ba sai kuma ya sake maida idanunsa kan fuskarta a fisge ya furta, “Akan wane dalili?”.

Baki ta ɗan turo kaɗan, ta ce, “Kawai”.

“Kawai?”.

Ya maimaita a sigar tambaya da wata irin muryar jinjina wautar ta. Kallonta ya cigaba da yi cike da nazari.. Tsintar kanta tai da jin ƙafafunta na rawa, dan idanunsa kaifafa da ya tsareta da su ji take suna sagar da ɗan sauran ƙwarin gwiwar tata. A hankali ta motsa da nufin barin wajen ya tareta da hannunsa. A marairaice ta ɗago tana dubansa kamar zata fasa kuka, sai kuma ta sake maida idanun ta risinar tana ɗan ƙara tura baki dan yaƙi daina kallon nata..

Idanun ya ɗan lumshe da sake buɗewa a kanta, a wata irin ƙaramar muryar da inba kusa da su kake bazaka taɓa sanin yana magana ba ya ce, “Kin san a gaban wa kike kuwa?”..

Kasa daurewa tai sai da ta ɗago ido ta ɗan kallesa, babu shiri ta sake maidawa da sauri. Amma gudun kar yaga gazawar tata sai cewa tai, “Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed. Shahan-shan ɗin ƙasar ruman mana”. Ta bashi amsa tana ƙwaɓe fuska babu ko gargada a harshenta balle muryarta..

 

Mutuwar tsaye yay na mamaki, ya lumshe idanunsa a hankali, shi yau shi Eshaan ƙaramar yarinyar nan ke ambaton sunansa babu ko gargada a harshenta ko nuna shakkarsa balle akai ga tsoro a gabansa ido cikin ido. Abune da bai taɓa jinsa ba sai a bakin mahaifiyarsa ko kakarsa. Suma ɗin akan jima baiji sun ambata ɗin ba. (Kai wannan yarinya zata halaka shi)

“Kada fa kace nayi rashin kunya kasa a ɓatar da ni ban gama cika burina ba, tunda ai dai kai ka tambayeni ko”. Ta faɗa tana mai langaɓar da kai idanunta na ɗan cikowa da ƙwalla na shagwaɓa da katse masa tunani da muryar nan tata mai ingiza bugun zuciyarsa kamar tasan mi yake tunani.

Komai baice mata ba, duk da yanda take kallonsa a kaikaice. Ya dai ɗan matsa gabanta yana cigaba da kallon ta kawai har tsawon wasu mintuna yanda tai kamar wata ƴar baby na bashi dariya a ƙasan zuciya. Sai kuma ya janye tare da ɗan matsawa da ga jikin nata da ya matso a zahiri babu ma alamar yasan minene murmushi. Aiko sai gata tana jan ajiyar zuciya. Basarwa yay kamar baijita ba.

“Miye burin naki?”.

Kalmar ta fito da ga harshensa a ɗan fisge tamkar wanda akaima dole. Batare da ta yarda ta kallesa ba ta ce, “Suna da yawa, muhimmai a cikinsu dai yanzu duk sun shafeka”.

Wani kallo da ke nuna alamar ni ɗin yay mata. Tako ɗaga masa kanta idanunta na ɗan cikowa da hawaye tana ƙiƙƙifatasu. A raunane kamar ba ita ba ta ce, “Ina son sanin halin da Iyayena ke ciki duk da an sanar min ka halaka su. Ina son sanin wanene Ajmaal?. Ina son idasa tabbatar da masu fuska biyun daular ruman wa duniya koda ni bazan iya wanke kaina ga kowa ba”.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button