Daudar Gora Book 2 Page 23
(Fitinanniyar yarinyar nan zata sa su binne ni a tsakkiyar ƙasata) ya faɗa a zuciyarsa yana mai lumshe idanunsa da ke bin lips ɗinta da kallon ƙasa-ƙasa, murmushi da ke neman suɓuce masa ya haɗiye a zahiri acan ƙasan zuciyarsa kuwa yinsa yake. Wanda bai sani ba sai ya ɗauka idanun nasa a lumshe suke, ga fuskarsa cike da barazana mai saka ruɗani ga duk wanda zai iya dubansa saboda yanda ya ɗaureta tamau…..
Kusan kowa sai da ya ɗauke numfashi a falon. Zukatansu kam na wata irin duka kamar ganguna, kalaman Iffah basu da banbanci da saukar nakiya a tsakkiyar kasuwar da bazaka iya banbance akan kanka ta fashe ba ko makwafcinka dan tsabar ruɗani. Cikin rashin yarda da kai aka shiga kallon kallo, kowa tsoron fara tankawa yake ko yin ƙwaƙwƙwaran motsin da zargi zai iya sauka a kansa. (Kun san mai kaza a aljihu fa baya jimirin asss). Malikat Ashwaq ta ɗan juya idanunta cikin ɓacin rai zatai magana da sauri Ameera Danish-Ara ta danne mata yatsun hannu tana mai haɗiyar yawu da ƙarfi. Shiru tai ta haɗiye abinda yake shirin suɓuce mata. Hakama Malikat Bushirat duk da kalaman Iffah sun daketa da ƙayatar da ita sai take jin kamar wani makircine yarinyar ke son ƙullawa domin kufcewa hukunci. Itama yunƙurawar tai zatai magana Daneen Ammarah ta girgiza mata kai da sauri.
Sayeed Hanifud-Din da gaba ɗaya shima yay mutuwar tsaye da waɗan nan kalamai na Zawjata-almilk da babu ɗar ko shakku na tsoro a idanunta duk da raunin dake tattare da yanayinta, jiki a sanyaye ya maida dubansa ga Shahan-shan. Babu alamar zaice wani abu har tsawon wasu mintuna da tashin hankalin duk wani wanda ke a falon ke sake bayyana. Sai da ya mula dan kansa yay gyaran murya. Cike da nutsuwa da ƙasaitar data zama ado ga sanyinsa ya ɗan sake dubanta da kallon da ke tada mata tsigar jiki a duk sanda ya yinsa. (Kinfa kife fuska tunda kin ɓallo min ruwa) a zahiri kam sai ya sake gyara gilashin fuskarsa kaɗan. “A bisa baƙon al’amarin da ya shigo a wannan shari’a bisa furucin wadda ake tuhuma, zamu ɗage wannan zama har zuwa nan da kwanaki uku. Za’a sake tsaurara tsaro ga wadda ake tuhuma fiye da da. Roƙon sakin wasu bai karɓu ba. Idan kuma da mai buƙatar cewa wani abu kotu na saurarensa”.
Shiru kowa ya kasa cewa komai, da alama wasu sun tsargu da tunanin cewar tasu zata iya zama talala musamman a sanin kaifin basira da sukaima Shahan-shan ɗin nasu. Hannun da yaga an ɗaga ya bi da kallo har ya sauke idanunsa kan kakar tasa, hakama duk wanda ke’a falon kallon nata yake. Malikat Haseenat ta jinjina kanta cike da dattako bayan kotu ta bata izinin maganar data nuna bukatar yi. A ladabce tai ƙasa da idanunta. “Muna godiya da wannan adalci na adalin shugabanmu, muna kuma roƙo a bisa adalcin wannan kotu ta bamu belin wadda ake tuhuma kodan kare lafiyarta da ranta da za’a iya nema a koda yaushe a dalilin furucin ta, babu yanda za’ai masu waɗan nan laifukan da ta ankarar su koma gefe su naɗe hannun zaman jiran a bankaɗosu batare da yunƙurin cuta mata ba”.
Nanma shiru kamar bazai amsa ba, bayan shuɗewar wasu mintuna kuma sai ya motsa. “Kotu ta gamsu da roƙon, sai dai bazata iya bada belin wadda ake tuhuma ba har sai an samo wani haske koda ƙanƙani ne da ga abinda ta faɗa ɗin. Za’a iya sake nema a zama na gaba”.
Daga haka ya miƙe abinsa cike da ƙasaita yana takun nan nasa na izza da bajinta. Dole kowa yay ƙasa da kansa har sai da ya fice sannan kowa ya ɗago. Iffah da ke jin ana kallonta ta ɗan ɗago kanta, ilai kuwa idanun Miran Arshaan da Miran Jasim ta gani na kallonta kamar zasu faɗo. Wani irin shegen makirin murmushi da ya nema wantsalo zukatansu waje ta saki tana mai kanne musu ido ɗaya da musu wani irin salo da yatsunta uku ta ɗauke kanta. Dan jam’ian dake tsare da ita sun zo tafiya da ita za’a maidata kurku