Daudar Gora Book 2 Page 154
Ya arrahaman! Bawan ALLAH dama kana raye? Amma ka sakani a rudani.
“Nasan zan saka kowama a rudani, sai dai wannan ranar ita naita rokon UBANGIJI zuwanta gareni kafin ya dauki rayuwata dan na cika wasiyyar mahaifina. Duk da burina ya cika na dawowar Fhareedah cikin zuri’ar mahaifiyarta a dalilin aure”.
Kowa zubama Iffah idanu yayi, kamar yanda itama take kallon Kaka jikinta na dan rawa. Malikat Bushirat ma wani irin bugawa kirjinta keyi, hakama Daneen Ammarah da Babiy. Cikin rawar baki data harshe Babiy ya ce, “Baba na kasa fahimtar komai”.
“Yanzu zan fahimtar da kai dama duk wanda ke anan. Kamar yanda Daneen Ammarah ta fada an aura mata miji kuma an saka ya saketa a sati biyu bisa umarnin mushirikar dake katantanwa da ikon wanna gida. Ba kowa bane wanda aka aura matan nan face Zayyan in Abbas. Zayyan dai da ne ga wani aminina da zan iya cewa ma ya zama jinina. Dan tunda muka taso babu abinda ke rabani da Abbas. Hatta aure an mana a rana guda ne, hakama haihuwar yaranmu tana zuwane a kusa da kusa. Sai dai shi nashi basa zama sai akan Zayyan. Sana’ar gidan su Abbas dinka kayan doki ne, dan haka ita ya gada ita kuma yake yi tunda yasan kansa, wannan dalilinne ya sani koyo a wajensa, danni gidanmu abinda na tashi naga anayi bana ra’ayinsa. Mahaifina babban mutumne mai bada magani sannan yana cire kowadanne irin aljanu a jikin mutum duk taurarin kansu. Ni kuma sai nake ganin kamar wani abun akwai kauce hanya, dan haka naki yarda na dingayi duk da tunda na taso yanayi a gabana na kuma san magunguna da sirrika kala-kala. Mukan dinka kayan doki ni da Abbas mu kawosu cikin Dahab City, anan ne muka hadu da wani bawan ALLAH da yay sanadin fara kawo wadan nan kaya namu cikin masarautar nan. A duk sanda muka kawo akan bamu kudinmu ne gaba daya, sai ma yazamindai mun dinka din nan kawai muke kawowa. A haka muka cigaba da rayuwa har shekarun yayanmu suka kawo girma, iyayrnmu suka bamu shawarar hada yaranmu aure. Munko yi farin ciki da shawarar, babu bata lokaci aka sha bikin Jumayma da Zayyan. ALLAH ya azurtasu da haihuwar fari da wuri, ta biyu ma haka, hakama ta uku. Zuwa sannan idan mun dinka kayan doki duk wanda zai o kawowa yakan taho ne da Zayyan da shine kadai keda sha’awar irin sana’ar tamu. Sauran yarana biyu maza kuwa suna nasu aikinne da sukafi so suma. A wata rana data kasance nine zan kawokayan da muka dinka masarautar a cikin azi sai na tashi da ciwo na zazzabi, dan haka Abbas ya amsa suka tafi kaiwa tare da Zayyan. Basufi awa takwas da tafiya ba sai gashi ya dawo min yana kuka. Hankalina tashe na tarbesa da tambayar lafiya. Bai boyen komai ba ya sanar min wai amma Zayyan aure da diyar Shahan- shan, cikin mamaki nace aure kuma? Wane irin aurene haka kamar auren kaza? Kuma da yar Shahan-shan guda anya kuwa?. Ya tabbatar min hakane, amma yanaji a jikinsa akwai dalili mai karfi nayin hakan dan yaji wasu yan samari da basu wuce sa’an Zayyan din ba na labari. Nan ya zayyane min komai dake faruwa ni da baba. Na lallashesa da kwantar masa da hankali na shirya a boye naje masarautar bisa umarnin mahaifina. Anan nake jiyo komai dama asalin dalilin hadin auren. Hankalina ya tashi dan na fahimci babban al’amari ne kam gashi ance Shahan-shan ma baya kasar shi da uwargidansa da Miran mai jiran gado. Kannensa ne da wannan aika-aikar. Na koma gida cikin damuwa mukai zaman jiran tsammani, tun muna irga kwanaki harya koma sati har sati biyu. anar kwatsam sai ga Zayyan ya dawo mana. Duk mun tarbesa da tambayoyin yaya akai ya kubuta. A take ya zayyane mana komai yana hawaye. Murmushi mahaifina dake kwance yana jiyya yayi, sai dai baice komai ba, sai daga baya 22:58