Daudar Gora Book 2 Page 149
Iffah kam wani shegen murmushi ta saki da har sai da ya bayyana farare hakwaranta.
Ganin kukan Miran Jasim bana karewa bane ga lokaci nata tafiya Sayeed Hanifud-Din ya gyara tsaiwarsa da fuskantarsa. “Shin ko Jasim na da wani abin cewa ne haka?”. Kuka Miran Jasim ya sake fashewa da shi da fadin, “Tabbas nine mai abin cewa, na kumayi alkawarin fadin duk abinda ake bukatar jiNda ga gareni, domin nayi nadama, nayi nadama matuka akan biyema Arshaan da mahaifiyarsa da tawa, Dan komai ya faro asaline da ga su….”
Ba Arshaan kawai ba, hatta Malikat Haseenat zura masa ido kawai tai, dan kowa yasan wacece mahaifiyar Arshaan. Mace ce mai kirki da kyawawan halaye. Haka kuma mahaifiyar shi Miran Jasim din. Mace ce mai mugun hali da son kanta, duk wanda ya kwana ya tashi a masarautar kuma ya san mahaifiyar Jasim din da ta Arshaan basa ma zama inuwa daya. Amma dai bara aji mi jasim din yazo da shi. Kuka ya cigaba da yi wiwi kafin ya nisa da cigaba da fadin, “Nasan a zahirance kowa zai ce iyayenmu mata basa shiri da juna ne, sai dai abin ba haka bane. A boye su din aminai ne matuka, dan mahaifiyar Arshaan ta shiga jikin Mammah (Malikat Haseenat) ne kawai danta dinga zakulo musu sirrikanta tana kawo musu. Burinsu shine muyi mulki, tare da mallake dukiyar Abbu (Tajwar Abdul-majeed) gaba daya, dan sun san Haysam ne zai gaje komai tunda shine babba. Sunta kulla-kullar gain mun halaka Haysam tun ma muna yara amma hakan bai kasance ba, dan haka suka yanke shawarar uwa ta kashe Abbu da Haysam tun a wancan lokacin.
Miran Arshaan ya fada cikin karaji da fashewa da kuka yana kaima Miran Jasim duka. Dan fa shi duk lalacewarsa yana son uwarsa, kuma yasan sam bata taba saka kanta a cikin wanna al’amarin ba, koshi bai fito da maitarsa a fili ta son mulki ba sai bayan mutuwarta. Da kyar aka rabasu, har Miran Arshaan ya jima Miran Jasim ciwo da farce a fuska. Rumtse idoNkawai Shahan-shan yayi cikin kunar zuciya. Sai da kotun ta lafa da kananun magana da ta dauka sannan aka sake bama Miran Jasim damar ci gaba da magana. Kafin yace komai Miran Arshaan ya tare da fadin, “Ba gaskiya ya shirya fada ba, dan haka ni wihy zan fadi komai, na kuma bada damar bayan duk na gama fada a bibiyi recording din nan namu dan baiyi dai-dai da abinda zan fada ba amun duk hukuncin da ya dace. Dan da ya tozarta mahaifiyata da ke kwance a cikin kabari da mata kazafi akan abinda bata aikata ba gara na fadi gaskiya koda ace itace karshena. Abinda ya fara fada ya faru amma a iya shi da mahaifiyarsa ne banda Ummi na, shi da kansa ya bani wanna labarin a randa muka yarda zamu hade kai domin yakar dan uwanmu Haysam. Dunkulewar tamu kuma ta samo asaline kan ima diyar Hifzur-rahaman fade da mukai ta mutu, muka bizne gawarta a cikin masarautar nan batare da sanin kowa ba ranar bikin al’ada. Tabbas mune muka aikata ni da shi, kuma duk neman da akai taima yarinyar har zuwa wannan shekarun da kowa ke tunanin saceta akai ko bata tai a bikin al’ada ba haka bane ba. Bayan mun dunkule mun shiga yakin gain bayan Haysam tako ina amma bamuci nasara ba. Muna a cikin wannan yakinne kuma yazo mana da zancen yin murabus ya daura dansa. Hankalinmu ya tashi matuka, a lokacin muka bazama neman bokaye kwararru da suka iya aiki, har muka had da boka Barbushi. Boka Barbushi ya mana alkawarin taimaka mana, da kuma tabbatar mana kashe Haysam da dansa. Munji dadi matuka tare da kasancewa cikin farin ciki mara musaltuwa, dan haka muka ware akai bikin nadinsa kamar babu komai a ranmu. Sai dai kuma mi, a randa Barbushi ya bamu gubar da zamu zubama Haysam sai muka iske Haysam ba’a cikin hayyacinsa ba. Shi kadai a daki yana ta aman jini da kiran sunan Eshaan da Mammah. Ganinmu yasa ya fara kiranmu akan mu taimakesa mu kira masa su, amma sai mukai fitowarmu mamaki fal zukatanmu, duk da ta wani bangaren murna muke zai mutu. Mun garzaya wajen boka Barbushi muka sanar masa komai, nan fa take shima ya shiga mamaki jin bama mukai da basa tamu gubarba. Gubar ya amsa ya ce mana muje mu dawo washe gari zai bincika, dan tabbas bayan mu akwai mai farautar rayuwar Haysam din. Gabanin asubahi muka dawo cikin masarauta, sai muka iske ALLAH yay masa rasuwa ma. Muni farin ciki, sai dai zukatanmu sun karkata da son gano wanene keda irin burinmu, domin mu a ganinmu dole ne shima mu kaudashi dan karya zame mana matsala idan shima burinsa yin mulkinne. Abinda fa zai baku mamaki a duk hadin kan nan namu muma bawai muna kaunar juna bane. Mu dikanmu burinmu shine muga bayan juna idan mun kauda Haysam da dansa. Abinda ya kara rikita lissafinmu mutuwar matan Eshaan guda biyu a washe garin mutuwar Haysam, babufa shiri muka koma wajen Barbushi.