Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 129

Sponsored links

A gajiye tibis ta shigo sashen, yana zaune a falo harde kamshinsa ya karade falon. Da sauri amintaccensa da ke gefen kafafunsa zaune da ga kasa yana ware masa wasu takardu da suka barbaza ya sake kasa da

kansa yana gaisheta.Da hannu ta amsa masa idonta akan zakinta da ke mata kallon kasan ido ta yanda ita kawai ke fahimtar hakan. A hankali ya motsa lips dinsa ya Bama amintaccensa umarnin tafiya. Zaram kuwa ya mike dan dama abinda yake jira kenan. Saboda a yanzu kam shigowarsa wannan falon sai da notis saboda yanda iyayen gidan nasa ke manne da juna akoda yaushe suna baje kolinsu yanda suka gadama. Shifa har mamaki yake da jin anya kuwa ba’a samu canji da ga Shahan- shan din nasu ba zuwa waninsa. Shifa yasan abinda yake gani kawai.

 

A hankali ya bude mata hannayensa alamar tazo garesa idanunsa kyam akan kyakykyawar fuskar ta dake a shagwabe kamar zata saki kuka. Kafada tadan noke tana tura baki, sai kuma ta fara takawa a hankali zata wucesa, a hankali ya riko hanunta da dan murmushin iya lips din nan nasa. Gaba dayanta ya jawo ta fado jikinsa. Wani irin sakin ajiyar zuciya sukai a tare.Tare da rungume junansu tsam-tsam kamar masu tsoron a rabasu.

“Kai ne na daban a cikin daban ai Zakina”. Ta fad itama tana sakar masa manya-manyan sumba a kan kirji. Sai kuma ta dago kanta suka zubama juna ido cike da kewar juna kamar ba da safe suka rabu ba. Cikin motsa lips dinsa da kyar ya ce” “Kin gaji ko?”.

Kanta ta jinjina masa tana marairaice fuska, sai kuma takai hanunta kan kyakykywar fuskarsa tana shafa kwantaccen gashin wajen dan tana matukar son sa. “Amma tunda aikin lada ne banajin gajiyar”. Dan sumbatar lips dinta yay a fisge ya ce, “Da gaske?”

Ta fada cikin fari da kashe masa ido daya.Murmushi ya dan saki da lakace mata hanci, sai kuma ya maida bakin nasa kan nata ya shiga bata kyakykyawar sumba, ba’ a barta a baya ba ta shiga taimaka masa cike da nuna kwarewar haddace dukkan karatunsa. Kafin akai wani dogon labari gaba daya yanayinsa ya canja. Dan shifa Tajwar Eshaan bai san wani yaren dandani haukaci ba. In har aka fara sai an kai karshe.Sannanake iya samun kansa dari bisa dari kuma dalibar tasa da alama dai irinsa ce, dan zuwa yanzu duk da ta kasa zama mai juriyar mika wuya yanda yake so saboda rashin sabo tana kokarta kamantawa musamman a bashi hadin kai a duk sanda yace kule takance cas. Da ga baya kuma ta dawo tana masa raki da shagwaba, Shiko yay ta mata murmushin miskilancin nan na..

Bayan sun samu daidaito ta lallabasa yay mata kiran su Babiy, sun jima suna hirarsu dan a yanzu kullum ne sai ta saka ya kira mata su, sai dai kuma duk sanda za’ai wayar yana dakin, bai kuma taba yarda shi sun gansa ba ko tayi wata magana a kansa, tayi-tayi ya barta suna gaisawarsu ita bazatace komai a kansa ba yaki bata damar hakan, ya dai yarda ya kira mata su su gaisa suma jima suna hira yana da ga gefenta yana saurare da jin komai.

L

Bayan sallar magriba ta samu sakon kiran Malikat Bushirat da ga wajensa. Dama dai suna da shirin zuwa mata sallama, dan insha ALLAHU ana kai azumin farko a gobe zuwa dare jirginsu zai daga zuwa Saudiyya. Sanin abinda ta kullama ranta tace ya barta to ta fara vin gaba yazo da ga baya tunda zaije ya ma Malikat Haseenat ma sallamar, ita kuma da safe Insha ALLAHU sai tayoma su Malikat Haseenat din sallama. Bai wani kawo komai a ransa ba yace taje, dama yana bukatar yin magana mai muhimmanci da Mammah din kuma akantane baya kuma bukatar taji.

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button