Daudar Gora Book 2 Page 122
(Yarinyar nan sai ta kasheni zata huta) ya fada a zuciyarsa dake faman bugawa da sauri-sauri cikin kaikawo. A hankali ya janye hannayensa dake sarrafa lap-top din ya daura na damar kan nata dake cigaba da shafa fuskarsa. Rikesa yay yana kokarin son gain ya janye amma sai tai wani irin juyi ta maida fuskarta saitin cikinsa ta sakalo dayan hanun nata a bayansa ta kankamesa.
‘”Kasheni kawai ki huta” ya fada cikin subutar harshe jikinsa na saki gaba daya Iffah da bata fahimci ita mima yake nufin ba ta kyalkyale da siririyar dariya har yana jin dumin numfashinta a kan Fatar cikinsa. Ita a nata shirmen kankamesan da tai ne yaji zafi. “dan na kasheka dawa zan zauna?”. Ta fada cikin dariyar tana kara cusa kanta jikinsa. Dole ya ajiye lap- top din ya kai kwance tare da dagota gaba dayanta ta hau saman jikinsa. Fuskarsa take kallo cike da dakewa kamar yanda shima yake kallon tata idanunsa a shanye. “Miyasa baki son a zauna lafiya?”. Ya fada a hankali yana sake kankance idanunsa cikin nata. Idanun ta juya tana shagwabe fuska da dan cuna masa lips dinta. “Toni mi nayi? In dai zuwa wajen Jaddah ne ai nace kayi hakuri”.
Dariya maganar ta bashi amma sai ya gimtse baiyi ba, ya dan tabe baki da tsatstsareta kaifafan idanunsa. Cikin dan dage gira
“Har na kai ki?”.
“Hu’um, ni a suwa kuma, kana kallon kanka a mirror kuwa da kyau?. Badan kar ace nayi karya ba sai nace kafi kowa kyau a kasar ruman”. Harga ALLAH ta bashi matukar dariya yanda ta fadi maganar cike da yarinta, yayinda zuciyar sa tai wani irin shiga farin ciki, domin kuwa bawai yafi kowa kyau din bane kamar yanda ta fada a zahirance, ya fahimci ta fara caukar karatunsa son sa ya fara shiga zuciyarta. Domin abinda kake so ne kawai kake ma kallon kasancewarsa a sama dana kowa. Shi kansa duk da yasan akwai kyawawan da suka fita ganinta yake samada kowa saboda kawai ita kadai yake so,kyawuntane kawai ke kayatar da shi. Bai fahimci murmushi yake ba sai da yaga yanda ta kura masa ido. Ya dan waro idanun waje alamar miye kuma, ita kuma sai ta girgiza masa kai tana murmushi da dan kauda idonta dake cikin nashi.”Murmushi na maka kyau, gashi kuma baka son yi”.
Hannayensa duk biyu ya doro a saman bayanta ya sake matso da ita ta kwanto jikinsa sosai, fuskarsu ta koma gab-gab har hancinsu na gogar na juna. “A komai k ta dabbance my sohaa”.
Ta fada tana dan sumbatar lips dinsa, sai tai saurin jan jikinta zata sauka dan sai da tai babban kokari wajen masa kiss din, amma kunya take ji. A hankali ya rikota bayan ya fisgo numfashinsa da ya nema kufcewa da kyar.Mirginasu yay suka koma saman hannayensu suna fuskantar juna, batare da jiran wani abu ba ya manne lips dinsu waje guda..
Babu alamar wasa tattare da shi, da ga tsayen da yake a kofa yana dubanta a yatsine ya ce,”Kifadi abinda zaki fada ina jinki, dan bazan wuce minti ashirin ba anan”.
Rai bace Ameera Haifah ke duba Miran Arshaan mai maganar, tai karamar kwafa da tabe baki,” Arshaan kenan, idan kana ganin Kanada mafitar da zata iya kwabemin ne ma,dan har da kai sai dai ka shirya mu duka zata kwabe Dar harda kai, idan har ban tsira ba da ga yarda ka maida Jasim kaima zan bude maka aiki ne. Zan kuma tabbatar maka na fika iya makirci dan mace sunana idan ka manta”.
“hhhhahh! Ni kike tunanin zaki iya budema aiki Haifah? to ina baki shawarar fita a hanyata da ga yau, in ba hakaba why zan kasheki na binne gawarki a cikin masarautar nan kuma na kashe banza”.
“Oh really? To Dan ALLAH ko zaka gwada ne? Nace ko zaka gwada kashenin muga!!!”.
Tai maganar cikin tsananin hargowa tana wani hahhankada kirji a gabansa. Wani irin tafarfasa yaji zuciyarsa nayi, dama a wuya yake, a fusace ya kaima wuyanta wani irin shegen shaka na tashin hankali. Cikin kankanin lokaci manyan idanunta suka sake yowa waje ruku-ruku, ga kakarin mutuwa da ta fara da mutsu-mutsun ganin ta fisge hannunsa da ga kan wuyanta. Sai dai kuma hakan ya gagara, dan karfinsu ba daya ba. Tafiya ya dingayi da ita cikin rufewar ido har jikin bango, ya kara matse wuyan da karfi tare da wajigata ya buga kanta jikin bango. Wata irin wahalalliyar kara ta fasa da ta jawo hankalin Jasrah dake daki kwance ta farka tana nemansa, dan su suna’a falon baki ne kasancewar cikin shigar badda kama Ameera Haifah tazo a nufin bako tasa amintaccensa imata iso saboda baya daga mata waya yanzun. Sai da yazo yaga itace. Gaba daya idon Miran Arshaan da alama ya rufe, dan tuni ya sake jijigata ya buga a bango, jini ko ya samu hanya ya balle.