Daudar Gora Book 2 Page 100
Shima da ke zaman kallonta duk dahankalinsa nakan waya ne a zahiri sai ya shirya tattarawa ya bar dakin, dan ya tabbata idan fingilar rigar barcinta ya dagata sama kadan cikin sa’a ya iya ganin abinda yake son ga Hoton wajen ya dauka da waya ya maida mara rigar a yanda take ya mike yana sauke ajiyar zuciya. Dan ya tabbata ido biyu bazata yarda yay hakan ba cikin sauki, maybe ma tafassarashi da wani abu daban…
Maimakon shiga wani dakin barcin ya kwanta karamin falonsa na hutawa dake rukunin dakun barcin ya shiga, agogo ya kalla, ganin sha biyu ta dan gota kadan ya dauke kai. Wayar dake gefensa ta landline ya dan daddana, batare daya dauka yakai kunne ba harta shiga ta yanke.Cikin abinda baifi mintuna biyar ba sai ga amintaccensa da butar shayi. A saman lips ya amsa sallamarsa batare daya dago ko motsa daga abinda yake ba. Koda ya gaisheshi ma bai ko amsa ba, ya dai daga masa hannu kawai, shiko bai damuba ya ajiye komai yanda ya dace ya zuba masa a karamin cup yasa yar zuma kadan dan yasan baima cika shan wannan shayin da komai a ciki ba. Bayan ya kammala cikin girmamawa kansa a risine ya ce, “Ko akwai abinda shugabana ke bukata?”. Yaja kusan minti daya da rabi sannan ya daga masa hannu. Duk wani yaren jiki da Tajwar Eshaan zai yi magana da shi hadimin nan ya haddacesa, dan haka cikin risinar da kai ya furta, “A huta lafiya, ALLAH ya kareka da kariyarsa”. Daga haka ya fice…
Duk da barcin dake cikin idanunsa tattaresa yay ya ajiye gefe guda ya tattara dukan hankalinsa kan littattafan da Malikat Haseenat tabashi. Inda zuciyarsa ke zallon zuwa kawai ya nufa bayan ya dan karanta tarihin mafarin komai. Babu bambanci da
wanda Mammah ta bashi, dan haka ya ajiye gefe da burin sai ya nutsu zaiyi komai daki-daki. Bai san adadin shekarunta ba, amma sai ya kiyasta da adadin shekarun da yake kallonta da su. Yaci karo da kusan hudu da yay dai-dai da hasashensa, a ciki uku na mata daya na namiji, gefe ya maida na namijin, ya dauka wayarsa yana kallon natan da na sauran matan uku kozai dace da wanda zasuyi dai-dai. Wani irin masifar harbawa zuciyarsa tayi gain tambari na karshe bashi da banbanci da natan. Bayanin dake kasan tambarin na tabbatar da dashi aka haifeta, a duk ma wanda aka haifa a tsakanin lokacin ita kadaice wadda aka haifa da shi sauran duk yimusu shi akayi. An haifi mai tamarin a daren ranar juma’a 22 a shekarar 2003 uku ga wata.Sai dai ita kuma ta rasu ne bayan haihuwarta da kwana uku. Wani irin kai hannu yay saman kansa ya yamutsa sumarsa yana ambaton sunan ALLAH. Ya akai haka? Ta yaya ma? Idan har ya tabbata ita din ce ya akai take raye bayan ance kuma ta mutu? Idan kuma wadan can dinne Iyayenta tayaya suka bar masarautar ma?bata mutum ba suka boyeta sukace ta muturn? Kai ina akwai dai abinda ya kamata ya sani, farkoma shekarunta ita. Sannan sanin asalin iyayenta.Lokaci yayi da zaisa a maidosu kasar ruman.
**
Kanta sara mata yake da cio mai azaba. Ga wani irin ja da idanunta sukai. Kofar da suka fita kawai ta tsurama ido tamkar suna a wajen har kusan awanni uku bayan fitarsu. Sosai take jin kuna mai radadi a zuciyarta. Har yanzu ta kasa yarda a ido biyu take, ta kasa yarda a zahiri komai ke faruwa, ta kasa yarda ita ta-kurya wata ta tsaya a gabanta tai mata wannan in kashir.Ta kasa yarda ita ta kurya yau wani ke tabbatar mata yasan itace silar mutuwar matan danta. Ta kasa yarda, ta kasa yarda da komai.