Daudar Gora Book 1 Page 94
A ɓangaren Barrister kamar yanda mutanen can suka sanar masa hakance ta faru. Sunyi amfani da kamannin da mutane suka daɗe da sanin sunayi, wanda shine ma tushen zamowarsu abokai, aikinsu kuma ya maidasu aminai. Sai dai muryarsu ta banbanta da wasu abubuwa na ɗi’ar yau da kullum. Akan wannan ne mutanen suka bashi training na dole dalilin barazana da sukai masa akan iyalinsa dama kashe Barrister Akeem ɗin da yake gudun cin amana. Bayan kimtsawarsa da shiga irin ta Barrister Akeem da bashi wasu bayanai akan aikin da zai musun suka bashi key ɗin motar Barrister Akeem. Sun sanar masa dukkan motsinsa akan idonsu ne, kuskure ɗaya akan ganganci fansar rayuwar ɗaya daga cikin ahalinsa ne kona Barrister Akeem. Dole Barrister ya kwantar da hankalinsa dan ya fahimci mutanen sunfi ƙarfinsa, gashi koba komai yana buƙatar kuɓuta kodan tarin ayyukan dake gabansa musamman akan aikin da ayanzu ya tasa a gaba da alƙawarin cika alƙawari.
Su da kansu suka bashi address ɗin inda zaije, yayinda ya hau titi kuma sai ya fahimci suna biye da shi a mashina wasu a mota. Ya ɗan rumtse idanu da jan kakkauran numfashi ya fesar lokacin da ya gama dai-daita parking a inda suka umarcesa zuwa. Sai da ya karanto addu’ar neman ɗauki ga ALLAH sannan ya fito riƙe da brefcase ɗin Barrister Akeem a hannu. Ƙaton gidan ya ɗan ƙarema kallo kafin ya nufi inda suke sanar masa yabi ta hanyar bluetooth ɗin kunnensa. Kansa kawai yaɗan gyaɗa tamkar yana gabansu ya nufi ƙofar……
A cikin masarauta kam kusan ƙarfe tara da wasu mintuna labari mai razanarwa na rashin ganin Sayeed Khairul-Bashar (Aami gasu Miran Arshaan. Kaka kuma ga Tajwar Eshaan. Shine wanda yay maganar jiya a ɗakin tattaunawa bayan tashin Tajwar Eshaan). Zancen rashin ganin nasa ya fito ne daga iyalansa, da farko an ɗauka yana cikin masarautar ne dan sun tabbatar daga sallar asuba bai dawo ba. Amma ganin har lokacin shigarsa gida ya wuce ƴaƴansa kuma sun bincika a inda suke tunanin ganinsa amma babu shi sai suka fitar da maganar. A take sojojin gidan masu bada tsaro dama hadimai suka bazu lungu da saƙo amma babu alamar hakan. Anbi diddigin wasu daga cikin cctv footage amma fitowarsa kawai aka gani daga sashen nasa babu komawarsa. Hakan ya matuƙar bama kowa mamaki da ɗaure kai. Dan ta ko’ina masu tsaron ƙofofi sun tabbatar basuga fitarsaba sukam. Gashi kuma an duba lungu da saƙo na gidan amma babu wata alamarsa…..
Lokacin da labarin rashin ganin Sayeed Khairul-Bashar ya iso kunnen Miran Jasim da Miran Arshaan dake tare kallon juna sukai, sai kuma duk suka kauda kawuna suna murmushi. Cikin son basar da zancen Miran Jasim ya cigaba da magana kan zancen da Miran Arshaan ya kawo masa dangane da Iffah
“Lallai wannan yarinyar hatsabibiya ce, aini tun isowar labarin kasancewarta raye a safiyar jiya al’amarin ta kemun kai kawo. Zancen ka na yanzu kuma ya sake tabbatar min da shirinta ta shigo masarautar nan.”
“To ai ta tara ta samu, dan dama mu irinta muke nema”. Cewar Miran Arshaan yana ɗan murmushi.
Miran Jasim ya jinjina kai shima yana murmushin nasa na izza da ƙasaita. “Hakane kam ta kawo kanta inda ake jirace da zuwanta. Dan kam zamu sauke ƙuruciyar dake izata a tunanin yin rawa da bazarta dake ɗawainiya da ita. Zata ƙarasa mana aikinmu cikin sauƙi batare da ita kanta tasan a cikin tarko take ba”.
Nan ma murmushi Miran Arshaan yay idonsa akan ɗan uwan nasa. “Zuwa yaushe aikinmu zai fara?”.
Miran Jasim ya ɗan ɗage kafaɗa da taɓe baki. “Bazai ɗauka lokaci ba. Sai dai muna bukatar wani point ne dole”.
“Wanda yake hannunmu fa?”.
Cewar Miran Arshaan da mamaki.
“Kai wannan bashi da wani ƙarfin da zaiyi tasiri ita a gareta, duk da dai zai iya zama kamar share mana fage ne. Zaren da nake ganin zamu ja ya kaimu gareta ɗaya ne, duk da dai har yanzu babu wani shaida dangane da tsallakewarta itama. Amma zamu yi amfani da damar, a wannan karonma matarka ce zata mana aikin”.
“A wannan gaɓar fa ya kamata mu canja salo, Jasrah nada matuƙar wayo, kar yawan bugar cikinta fa yasa ta fara fahimtar wani abu”.
“Sai idan kaine ka bada ƙofar hakan Arshaan. Shekara nawa muna amfani da itan bata fahimtaba sai yanzu. Ka dai kawai ka kasance mai lura”.
Kai kawai Miran Arshaan ya jinjina batare daya ce komai ba……