Daudar Gora Book 1 Page 85
A cikin farin cikin daya goge duk wani damuwarta a wannan yini ta fito hadimanta na take mata baya ɗauke da ɗirka-ɗirkan littafan da ta ɗebo. A yanzu ɗin ma dai tako ina hadimai faman zubewa suke domin girmamawa a gareta harta isa sashenta data basu umarnin su kaita saɓanin sashen Shahan-shan daya kamata ace ta koma tunda a ƙa’ida sati guda zatayi kamar yanda Malikat Haseena ta sanar da Tajwar Eshaan. Iffah kam da ba zama akai aka faɗa mata komai na ƙa’idojin ba haka kawai taji bata bukatar komawa zaman takura da zuciyarta ta ayyana mata rashin amfaninsa. Shi dai wanda aka kaita dominsa ko kallo bata ishesa ba, hasalima baya kallonta da suffar da suka miƙata garesan kai tsaye. Yo dole ta faɗi haka, tunda wane mijin ƙwarai ne zai jefama matarsa kalmar tambaya ta ita (wacece?) Bayan da saninsa aka kai sadakinsa domin aurota. Bazata iya ɗaukar waɗan nan abubuwan ba, dan bama abinda ya kawota nan ɗin ba kenan tun fil’azal. A ganinta kuma ba sai dole an kaita garesa an ƙaskantar da ita ba, zatabi hanyoyin daya dace na haɗuwa da shi har lokacin da zata cika ɓoyayyen burinta….
Da wannan tunanin suka ƙarasa sabon sashen nata. Tabbas ta jinjinama ƙoƙarin su, dan ko makaho ya laluba yasan wannan sashen yayma wanda aka kaita fintinkau a komai duk da shima wancan ɗin dai ba baya bane a tsaruwar. Ta ɗan sauke numfashi da kaiwa zaune bisa ɗaya daga cikin lumbutsa-lumbutsan kujerun da aka shirya falon da su bakinta ɗauke da bismillah. Suma dai hadiman nata bayan sun ajiye litattafan a saman Centre table a gabanta suka zube. Taja tsahon mintuna goma tana mai nazarinsu kafin ta ɗan sauke numfashi da miƙewa.
“Ina buƙatar zama da duk wanda zai kasance da Ni a wannan sashen zuwa anjima”.
Cike da girmamawa duk suka amsa mata kawunansu a ƙasa. Ta ƙara jan numfashi ta fesar batare data farga da salon izzar da yay kutse ga al’amarin ta na yanzu ba ta kai dubanta ga agogon falon. “Muna da sauran lokaci yanzu da zai ishemu zagaya sashen kafin na shige salla”.
Anan ma sun amsa mata ɗinne da girmamawa. Batare da ta sake cewa komai ba tai gaba duk suka miƙe suna take mata baya. A yanzu ma dai wadda ta jagorancesu zuwa books room ce ke mata bayanin sashen da tsarinsa yanda ya kamata. Cike da gamsuwa batare data furta komai ba koda so ɗaya take gyaɗa mata kai. Sashen ya ƙunsa abubuwa masu yawa da zaman lissafinsa zai zama ɓata lokaci da cinye mana page, bayan sun kammala zaga ko’ina Iffah ta shiga bedroom ɗin da zuciyarta tafi aminta da shi matsayin master bedroom ɗin ta.
Mamaki ya kamata lokacin da taci karo da guntuwar takarda a saman duvet ɗin saman gadon. _Ibnati wannan ɗakin ki tabbar ya kasance ɗakin sirrinki, shiyyasa nasa a shirya miji duk wani abu na buƙatar ki._ takardar ta ɗan juya tana mai jan numfashi da fesarwa. Sai kuma ta saki murmushi dan ta fahimci saƙon na Daneen Ammarah ne. Wayarta ta ɗauka a ɗan gaggauce ta aika mata saƙo. Sannan ta nufi bayi gabatar da al’wala…….
Tun bayan faruwar komai daya shige ɗaya daga cikin ɗakunan barcinsa bai sake fitowa ba sai yanzu a cikin shirin zuwa Masallaci. Sau ɗaya ya ɗagama hadiman dake zube ƙasa a dalilin fitowarsa hannu ya fice. Da kallon ƙasan ido duk suka bisa, kowa da abinda zuciyarsa ke ayyana masa game da shi…
Bayan idar da sallar isha’i bai samu damar shigowa ba yay zaman ganawa da Aamin sa su biyu da suka buƙaci hakan. (Miran Jasim da Miran Arshaan). Miran Arshaan shi yafi jansa a jiki tun fil’azal, sannan kuma kamar yafi kusanci garesa ta bangarorin biyu kasancewarsa miji ga Khaalti (Aunt) ɗinsa da yake kallo tamkar yaya. Shima dai Miran Jasim ɗin bai taɓa nuna masa wani abu mara kyau ba a zahirin rayuwa, a komai ma da zai taso yakan bada ƙarfinsa wajen karesu ne ga kowa koda a fada ne. Waɗannan hallayya tasu ya sashi ɗaukar yarda ya basu har yakan iya tattauna wasu abubuwa da suka shafi mulkinsa, sai dai abinda duk ya shafesa a karan kansa duk yanda zasu so sani baya taɓa basu fuskar hakan dan ko’a zahiri kowa na masa kallon mutum mai wuyar sha’ani, bahagon mai bauɗaɗɗen hali da zurfin ciki ne.
Bayan ficewar hadimin daya gama hidimar zuba shayi a gaban kowannensu ya fice Miran Jasim ya fara katse shirun dan yasan in zasu kwashe awa ɗaya a wajen Tajwar Eshaan bazai sake tofa komai ba bayan gaisuwar da yay musu. “Abni nasan zakai mamakin wannan zaman namu, sai dai a dubi da abinda ya faru ɗazun ba abin mamaki bane. Abinda ya faru ɗazun ya matuƙar Kona mana zuciya, dan bazamu taɓa so a aibantaka ba muna ji muna gani kodan amanar da Haysam Akhi ya barmana taka. Akwai wasu abubuwan da yawa daya kamata dama mu tattauna da kai kafin wannan ɗin, amma a yanzu kamar wannan ɗin ne importent”.
“Hakane Jasim Akhi”. Miran Arshaan ya karɓe fuskarsa na nuna tsantsar damuwa. Ya cigaba da faɗin, Abni lokaci yayi da nake ganin ya dace wasu a cikin iyayen nan namu dake zaman fadanci ya kamata su huta ƴaƴayensu su karɓesu. Duba da kai matashi ne, a koda yaushe ra’ayinka da hangenka zai cigaba da zama banbanci ne da nasun. Koda yake su a gare sun ma ba haka bane, dan haka mahaifinka yasha gwagwarmaya matuƙa da su a yayin nasa mulkin. Amma kai mi kake gani akan hakan?”.
Shiru babu alamar Tajwar Eshaan zai tanka, sai ma cigaba da kurɓar shayinsa yake cike da ƙasaita idanunsa akan television dake aiki a falon…….