Daudar Gora Book 1 Page 48
Zaune take hakimce kamar ko yaushe cikin kwalliya mai matukar ɗaukar idanu. Ga wani sihirtaccen ƙamshi mai ratsa zuciyar duk wani mai shaƙa na tashi. Shi kansa falon kamshinsa na musamman ne. Gefenta na dama Jasrah ce itama cikin kwalliyar, zuwanta kenan sashen sakamakon aiken data samu daga ƴar uwar tata. (Itama dai Jasrah anan cikin masarautar take aure, tana kuma auren ƙanin marigayi Tajwar Haysam ne da suke uba ɗaya. Dan kamar yanda Tajwar Haysam suke su huɗu a ɗakinsu suna kuma da ƴan uba har su kusan tara, sai dai mata sunfi yawa a ciki. Su tarannan kuma ƴaƴan mata uku ne. Mijin Jasrah shine babba a cikin ƴaƴan amaryar Tajwar Haysam da ake kira Ameera Aasfah a masarautar. Mace ce mai kirki da sanin ya kamata, jininsu kuma yay matuƙar haɗuwa da Malikat Haseena. Dan idan ka gansu bazaka taɓa ɗauka kishiyoyi bane a sanda tana raye. Yaranta biyune ita kacal, Miran Arshaan shine babba, shine kuma ɗa na takwas a wajen Tajwar Abdul-majeed, a maza kuma na uku, shine mijin Jasrah a yanzu, sai ƙanwarsa Daneen Fu’ada, a yanzu haka tana aure itama. Ƙaunar dake tsakanin Malikat Haseena da Ameera Aasfah yasa shaƙuwa sosai a tsakanin ƴaƴansu, hakan yasa Tajwar Haysam ke kallon Miran Arshaan tamkar ƙaninsa Miran Nayyar daya rasa, shine ma da kansa ya aura masa Jasrah. Wannan kenan, ALLAH yasa kun gane🥱).
“Akia kince nazo amma kin kasa cewa komai? Wani abun ya sake faruwa ne?”.
Numfashi Malikat Bushirat ta sauke a hankali tana kallon ƴar uwar tata da takema kallo tamkar first born ɗin ta. Kamar bazatai magana ba sai kuma ta nisa cike da kasaita. “Komai bai sake faruwa ba, sai dai ina gudun sake faruwar. Sanin kanki ne Jasrah ba lallai kosu waye su haƙura ba dan yarinyar nan ta kuɓuta a yanzun, sannan ma bayan ita akwai sauran yaran biyu da har yanzu fargaba ta hanamu kaisu turakar Saifulmalik. Kin san kuma rashin kai su zuwa nan da ɗan lokaci sai kinji an fara kace-nace”.
“Hakane Akia. Amma ke mikike son cewa?”.
“Zancen dai ɗaya ne shine inajin tsoro, na biyu kuma da gaske yarinyar nan ta shiga raina fiye da duk matan da aka kawo gidan nan matsayin Zawjata-almilk”.
“Wlhy nima har cikin rai yarinyar ta shiga raina. Gata da tarbiyya daga ganinta, sannan itace mafi ƙanƙanta a duk matan na Son”.
“Wannan yana ɗaya daga cikin abinda ya sake jan hankalina a kanta Jasrah, shiyyasa yanzu da wani tunani yazo min nace bara nai shawara da ke. Shin kina ganin naima Mamma (Malikat Haseena) magana gobe idan ALLAH ya kaimu da Saifulmalik zaije gaisheta a kusanta shi da yarinyar nan suga juna? Sai nake ganin hakan zai canja wani babban al’amari da masu mana yankan baya ke ƙullawa. Tunda kinga dai duk matansa sai an kaisu turaka yake da damar ganinsu kamar yanda kowa yasan dokar kenan ga duk Zawjata-almilk tun ƙarnin baya”.
“Eh gaskiya kuma wannan tunani ne mai ƙyau Akia inhar Mamma zata amince ɗin. Dan Kinga muma a karan kammu wata hanya ce da zamu fuskanci wani abu akan shi kansa..”
“Wannan gaskiya ne. Dan da gaske Jasrah a yanzu har shi kansa zuciyata rawa take ga al’amarinsa, dan abinda ke faruwa dole ne kowa ya zama abin zargi har mu kammu, ke nama takaice miki zance ni kaina yanzu ban yarda da kaina ba”.
Murmushi Jasrah tai har haƙoranta na bayyana. Tace, “Kai Akia kinada abin dariya wlhy wani lokacin. To inke baki yarda da kanki ba mu kuma dawa zamu yarda kenan?. Kawai dai inaji a jikina koma minene ya kusa zuwa ƙarshe ta silar yarinyar nan tunda har ALLAH ya fara nuna musu iyakarsu suka gaza cin nasara a harin farko da suka kai mata. Yanzu dai bamu da lokaci, ki tattauna da Mamma ɗin kawai. Hukuncin data yanke sai mu karɓa kawai”.
Malikat Bushirat ta jinjina kai kaunar ƴar uwar tata na sake ratsata. Koba komai idan ta tattauna da ita takanji sanyi a ranta…….
“Wai nikam ɗazu ina ƙoƙarin shiga fada naga kamar motarki ta gitta, kinje wani waje ne?”
Shayin da take ƙoƙarin zuba masa ta karasa tare da miƙa masa. Sai da ya amsa ta koma ta zauna tana mai ɗan ɗage kafaɗunta. “Kaima kasan fita ta bata wuce wajen Akia ai Abu Harith, wlhy itace fa tai min kiran gaggawa shine ka ganni na fitan. Amma lafiya kuwa har irin wannan lokacin kuna a fada?”.
“Uhm to lafiya lau za’ace, anyi baƙin bazata ne kawai ga Shahan-shan ya rigada ya shige kuma. Dole mu mukai zaman tarbarsu. Amma kiran gaggawa wata matsalar ne ta sake faruwa? Ko jikin Zawjata-almilk ɗinne dai?”.
“No akan dai wadda ake cikine. Jikinta kuma Alhamdullah, idan ma ka ganta yanzu bazakace wani abu ya faru ba. Kawai dai Akia ce ke ganin ya kamata idan Shahan-shan yaje gaida Mamma gobe idan ALLAH ya kaimu Zawjata-almilk ta ziyarcesa ko hakan zai kawo wani sauyi kan abinda har yanzu muka kasa sanin kansa”.
“Amma baƙwa ganin hakan wani ganganci ne? Sannan dokace fa Shahan-shan baya ganin matansa sai a turaka”.
“Eh muma mun duba wannan ɗin, dan haka ma bamu wani yanke shawara ba akace sai an sanarma Mamma. Amma kai ya kake gani akan hakan. Abu Harith wlhy Akia na bani tausayi matuƙa, a yanzu har takai da kanta itama zarginsa take shi yake ɓarnar nan”.