Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 44

Sponsored links

Iffah na ganin ta fice ta sauke ajiyar zuciya, addu’a tai ta rufe Alkur’anin ta mike, kofar taje ta sanyama key bayan ta leƙa babu kowa a corridor ɗin. Ta ɗan jingina da ƙofar tana mai ambaton “Alhamdullah” da sakin ɓoyayyen murmushi. Cikin sassarfa tabar jikin ƙofar zuwa ga akwatinta, ta buɗe tare da ɗakko wayar Arfa da takardar da Malam Fawzan ya bata. Number da aka rubuta ta kwashe a wayar, ta haye tsakkiyar gadon ta kwanta tare da jan lallausan bargon ta shige ciki har kanta sannan tai dailing number. Gaba ɗaya a kage take da zumuɗin a ɗauka. Dan haka take bin sautin shigar kiran da zuciyarta. Sai dai harta yanke ba’a ɗaga ɗin ba. Kira ta sake yi, nan ma dai shiru, bata gajiya ba ta cigaba da kira har fin sau goma kafin a ɗaga a karo kusan na goma sha biyar. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tamkar wadda aka tsamo daga cikin ƙanƙara. Sai kuma tai saurin faɗin, “Assalamu alaikum”.

“Wa’ake nema?”.

Aka faɗa daga can maimakon amsa sallamar tata. Da lafiya lafiya ne sai tayi mitar ƙin amsa sallamar, amma sai tai saurin faɗin, “Sir Ajmaal”

Wayar ta janye a kunenta ta tashi zaune ta ɗauka takardar, number dai dake a jikice dai-dai batai mistake ba. Sake maida wayar tai kunne aranta tana faɗin (bara naga ƙarshen ku dai) ta sake amsawa da “Sir Ajmaal”.

“Kin saɓa lamba”.

Aka bata amsa da yanke wayar lokaci guda batare da anjira cewar ta ba……

Kasancewar Abu Zainab suruki ga barrister cikin sauƙi suka samu ganinsa ta hanyar kiran waya. Har office yasa masinjansa daya fita yay musu iso ya shiga da su. Ganin lafiyayyen office ɗin nasa dama hukumar tasu ya sake tabbatar ma da Kaka babbane gaskiya. Sun gaisa cikin nuna sanayya shi da Abu Zainab. Ya kuma gaida Kaka da girmamawa kasancewar tsoho dama zai iya haifarsa. Basu saurari lemo da aka kawo musu ba Abu Zainab ya shiga masa bayani dalla-dalla. Sai da ya gama tsaf Barrister Abdallah dake rubuta wa ya ajiye biron yana jinjina kansa. Kaka ya fuskanta cikin son ƙarin bayani….

“Baba kaima kasan shi Dawood ɗin kenan?”.

“Tabbas na sanshi yaro. Hasalima ga gidan mahaifin shi Muhammad Zayyanu gana mahaifin Dawood. Sannan ta ɓangaren mahaifiyata ma munada alaƙar jini da mahaifin nasa. Shine kuma yay sanadin zuwan Muhammad Zayyanu garin nan, shi kuma Muhammad Zayyanu ya koya masa noman zuma daya gada ga mahaifinsa”.

“Eh lallai sanayya ce babba kam. Sai dai kuma inaga ya kamata nasan miya rabasu? Dan yanzu hujjojin hanunmu sune zasu taimaka mana wajen kubutar da su saboda wannan case ne babba kuma da alama shiryayye”

“To nidai kai tsaye banace ga abinda ya zama sanadin rabuwar kawunan nasu ba. Dan shi Muhammad Zayyanu mutum ne mai zurfin ciki da rashin kwaramniya. Amma dai lokacin da naga bana ganinsu tare na tambayesa ko akwai matsala? Shi da abokin nasa. Sai ya sanar min shi dai a saninsa bai masa komai ba ya janye daga jikinsa, ya kuma bisa ya bisa babu adadi danya faɗa masa amma yaƙi, daga karshe ma ya tattare kayansa da iyalinsa sukabar anguwar, bai kuma sake ganinsa ba har watanni sunja a lokacin. Na bashi shawarar ya ƙara nemansa dai, da muka sake haɗuwa na tambayesa sai yace ai yama bincika yabar gari. Iyakar abinda na sani kenan gaskiya”.

“Shi kuma Dawood ɗin baka sake ganinsa ba kaima?”.

“Eh to gaskiya ban sake ganinsa ba. Dan ko’a rasuwar mahaifinsa sai wai-wai mukaji yazo yay gaisuwa ya tafi kawai. Daga nan kuma dai bamu sake jin ɗuriyar tasa ba dan dama mahaifiyarsa bata raye tuni”.

Barrister dake faman kaɗa kai ya sake ajiye bironsa. “Uhhm yanzu to inaga mataki na biyu shine musan wane station suke. Ko kuma inda ita matar tasa take”.

Cikin damuwa Abu Zainab yace, “Munje inda muke tunanin samun nata bamu sameta ba. Sai dai an ambata mana sunan wanda ya saida gidan ga wanda ke ciki yanzu”.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button