Daudar Gora Book 1 Page 35
“Ya take yanzun?”.
Tambayar da take son jin tun ɗazu daga bakinsa ta fito tamkar an fisgota. Idanunta ta ɗan kafe kansa, amma sai ya kauda kai gefe kamar bashi ya buƙaci ji ba. Taja numfashi ta fesar, itama batare data sake cewa komai ba ta cigaba da nazartar sa. Kusan mintuna uku tsakani sannan ta nisa…
“Ban san mikafi buƙatar ji ba. Sauƙin ko akasin sa. Amma dai zan iya cewa muna jiran ikon UBANGIJI ne”.
Shiru babu alamar zai sake cewa komai, itama bata sake cewar ba. Kansa ya ɗan risinar gefe bayan ɗan kallon gefen idanu da yay mata. Miƙewa Malikat Bushirat tayi, ya bita da kallo harta isa bakin ƙofa sai kuma ta juyo, “Ina jin tsoron ace alaƙar da maƙiyanmu ke alaƙantawa da kai ta zam haka take Saiful-mulk”
Kansa ya ɗauke gefe, itama sai ta ɗauke nata kan daga garesa tana danne lips ɗinta da haƙori. Shiru kusan na minti ɗaya, ita bata fitaba ita bata juyo ba, shi kuma bai amsa mata ba bai kuma motsa ba, sai kawai ta buɗe ƙofar zata fice.
“A huta lafiya”.
Ya faɗa dai-dai tana ficewa. Bayan kusan minti uku da fitarta ya furzar da nannauyar iska, miƙewa yay hannayensa goye da bayansa ya fara tattaki zuwa gaban window ta saitin inda zai iya hangota. Dai-dai kuwa hadimanta dake zaman jiranta na zagayeta. Duk da nisan da sukema idanunsa bai bar wajen ba har sai da yaga ta shige sashenta da tawagar hadimanta.. Wani irin ƙasaitaccen murmushi ya saki da lumshe idanu, sai kuma ya buɗe cike da isa yana mai barin windown ya shige ƙofar daya fito ɗazun….
Lafiyayyen bedroom ne mai ɗauke da kayan more rayuwa irin nasu na manya. Ƙamshi dai kam ba’a magana dan Tajwar Eshaan ko gonar turare haka ta gansa ta bari saboda yanda yake wanka da shi a duk motsinsa, son ƙamshi da zama cikinsa tamkar al’adarsu ce data zama dole ga talaka da mai kuɗi, sai dai banbancin tsada da ƙamshi ya banbanta maka wanene tare da kai. Amma dai-dai da banɗakin jinin Ruman ko shagon sai da kaya a kasuwa ka shiga saika san kazo ƙasar ƙamshi, duniya ta sansu da wannan tun shekaru aru-aru, dan suna a sahun farko na ƙasashen dake yin turare, yana kuma ɗaya daga cikin tattalin arziƙinsu dake shigar musu da kuɗi da bayyanasu a ko’ina suka shiga a duniya. Zaune ya kai a kujerar dake ɗan gefe ta jikin window, ya kai bayansa kwance a kujerar, tare da kwantar da kansa ya kalli sama ya lumshe idanunsa. Daga ƙasa ƙafafunsa a harɗe, hannayensa duk biyu akan hanun kujerar ya ɗan fara lila kansa. Sai da ya ɗauki tsahon mintuna ashirin a haka dan zakama iya ɗauka barci yake yi kafin ya buɗe idanunsa da suka kaɗa sukai jajur, zaune ya tashi da ƙyau, ya kai hannu drawer’n dake gefen kujerar ya buɗe, ƙaramar waya ƙirar nokia ya ɗakko. Danne-danne yay tare da kaiwa kunnensa yana wani yamutsa fuska. Bugu ɗaya kuwa aka ɗaga daga can, cikin bada umarni da ƙarfin ikon ya furta..
“A kawar da ukun bana buƙatarsu. Haɗuwa, da lokaci zaizo a saƙo”.
Ya janye wayar daga kunnensa da dafe kansa yana cizar lips ɗinsa a lokaci guda fuskarsa babu alamar ɗigon wasa ko sassauci a cikinta sai razani mai ban tsoro da saka firgicin ga duk wanda zai iya ganinsa a hakan……….