Daudar Gora Book 1 Page 29
A wani irin matuƙar hargitse Diwa ta ɗago tana duban ta, jikinta har wani karkarwa yake. “R….ran…ki ya daɗe w…w..wan nan ai ba hurumina bane”.
Iffah data kafeta da idanu ko ƙyaftawa batayi ta janyesu a hankali tana mai miƙewa abinta batare da tace komai ba. Da sauri Diwa ta ƙara gurfana a gabanta tana hurwa. “Ranki ya daɗe dan ALLAH karkice bazakici komai ba, dan komai anan umarnine”.
Bata zauna ɗin ba, ba kuma tace komai ba. Sai ma ɗakin da suka fito data nufa zuciyarta cike da nauyi. Batafi zaman mintuna biyarba wasu mata da batako musu kallo biyu ba suka iso da wata hamshaƙiyar riga mai kamar alƙyabba daga Malikat. Tare da umarnin tafiya da ita. Batai musu ba, dan a nata tunanin Malikat Bushirat suke nufi, sai dai zuciyarta ta kasa nutsuwa. Addu’a ta shiga ambato a zuciyarta har suka kammala saka mata ƙawatacciyar rigar alƙyabar mai tsananin ado da ɗaukar idanu, zasu kunna mata turaren wuta da suka shigo da shi a burner tai saurin dakatar da su.
Kallon juna sukai, kafin ɗaya tai saurin faɗin cikin ƙanƙan da kai, “Ya Zawjata-almilki wannan umarnine daga Malikat”.
Yamutsa fuska Iffah tai tana mai kallonta, kallo irin na wannan bata san wacece autar Babiy ba ta ɗauke kai. A karon farko tun shigowarta gidan tai magana da harshen ƙarfin zuciya ta ajiye rauninta a gefe. “Ni kuma wannan umarnina ne bana buƙata. Sai kumuje umarni na gaba”.
Babu wanda a cikinsu baiji yayi sumar wucin gadi ba. Sai dai wani irin kwarjininta da jin shakkarta ya gama ɗarsuwa a zukatansu lokaci guda.. Iffah dake jin jininta na wani irin tsitstsinkewa ta sake dubansu da niyyar magana, tamkar wadda aka jefa da narkakken ƙarfe taji yafff! A ƙirjinta. Da sauri ta dafe ƙirjin tana mai rumtse idanunta. Rawar da jikinta ya farayi ya sata zubewa ƙasa tana mai ƙoƙarin ambaton sunan ALLAH, amma hakan ya gagara, dan tamkar an naɗe zuciyartane da harshenta a lokaci guda……
Har rige-rigen fita hadiman nan sukeyi jikinsu na matuƙar rawa. Diwa dake zaune a falo tana jiran fitowarsu ta miƙe da sauri tana tambayar lafiya? Babu wanda ya saurareta a cikinsu suka fice. Hankalintane ya tashi, tai kamar zata bisu sai kuma ta fasa ta nufi ɗakin da Iffah take. Wani irin mugun bugawa ƙirjinta yay damm. Innalillahi….. ta shiga ambata dayin kan Iffah dake ta faman juye-juye a ƙasa, cikin ƙanƙanin lokaci ta jiƙe sharkaf da zufa tamkar an watsa mata ruwa koma an tsamota a ciki. Harta kusa kai hannu kanta sai kuma taja baya da sauri cikin tsoro. Ina bai kamataba, matsayinta na hadima hanunta ya taɓa Zawjata-almilki. A daburce tai waje da nufin isar da saƙo ga Malikat Bushirat duk da bata da tabbacin samun iso cikin sauƙi……..✍
Cikin ƙanƙanin lokaci labarin abinda ke faruwa da Zawjata-almilki ta uku ya gama gauraye daular ruman. A take ko’ina yay tsit sai ƙus-ƙus da maganar ido kawai. Sauran Zawjata-almilki kuwa guda biyu dake gidan dama kafin kawo Iffah tuni sun sake shiga tsantsar tashin hankalin da yafi wanda suke ciki. Su dai dama rayuwa suke cikin jiran
tsammanin isowar mutuwarsu. Ko lokacin da aka sanar musu sake ɗaura auren Tajwar da wata matar tsantsar tausayin kansune kawai ya baibayesu, yanzu kam jin halin da matar da aka kawo jiya take ciki ya tabbatar musu suma mutuwarsu tunkarosu take sakeyi kenan……
Duk wata tuhumar data dace akan hadima Jaza da sauran hadimai biyu da sukaje ɗakin Iffah suma da aka gano anyi amma sunƙi faɗar gaskiyar wanda ya sakasu, sai cewa suke Diwa ce. Yayinda Diwa ke rantsuwa da ALLAH tana kuka akan ƙarya suke mata ita bata san komai ba. Iya jigatuwa sun jigatu har takai numfashi da ƙyar sukeyi saboda azabartawar da ake musu. Sanin rayuwarsu akafi buƙata a yanzu sama da mutuwarsu yasa hadiman kurkukun dake a cikin daular ruman tsagaita musu. Amintaccen hadimin Malikat Bushirat ya koma ya sanar mata halin da ake ciki. Shiru kamar bazatace komaiba. Sai kuma ta dubi Jasrah da har yanzu ke tare da ita ta ɗauke kanta.
Jasrah data fahimci mi ƴar uwar tata ke nufi takai dubanta ga hadimin. “Ghazi! A cigaba da tsaurara musu tsaro har zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu”.
“ALLAH ya ƙara miki lafiya an gama”. Ya faɗa da tsantsar girmamawa yana mai rissinawa da gyara takobin hanunsa ya fice…….
Tun Iffah na iya motsa jikinta da furta kalmar bakinta har hakan ya gagara numfashinta ya fara neman barin jikinta. Ga dai masu magani mata rufe a kanta mazan na daga waje suna haɗo duk abinda ya dace amma babu alamar wani canji sai ma ƙwaɓewa da komai ke nemanyi. Tun ana ƙirga awannin iya shawo kan matsalar har komai ya fara firgita kowa. Daular ruman tayi tsitt babu mai ƙwaƙwaran motsi a cikinta. Sautin fitar kiran salla ma dan ya zama dolene. Koda aka idar da salla ma sake komawa zaman jigum-jigum akayi domin kuwa abinda bai taɓa faruwa a tarihin masarautar bane ya faru. Tajwar Eshaan bai fito sallar zuhur ba yau. Hakama da la’asar. Magrib ma ta shiga babu wanda yaji motsinsa. Zuwa lokacin kuma akan Iffah an zubama sarautar ALLAH idone wadda ta girma ta ɗaukaka.
Dan kuwa tana a shimfiɗene jiki duk ya ɗashe tamkar wadda ta ƙone gurin yay ja kafin ya tashi. Kaɗan-kaɗan numfashinta ke fita wanda shine kawai ya tabbatar da tana a raye bata mutu ba. Masu magani kowa yayi iya iyawarsa sun koma gefe ana jiran ikon ALLAH kuma. Ana idar da sallar la’asar Malikat Bushirat ta bada izinin maida Iffah sashenta…..