Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 22

Sponsored links

Washe gari data kasance safiyar laraba da misalin ƙarfe biyar na yamma sai ga manyan baƙi daga masarauta ruman. Baƙi masu ban mamaki, dan kuwa wasu manya ne a cikin dattijai masu faɗa aji a daular ruman. Sannan iyaye ga Shahan-shan ta ɓangaren jini makusanta sosai ga mahaifinsa. Tamburan masarauta da ɗunbin tawagar hadimai da jibga-jibgan motoci da suka ƙoshi ne suka tabbatarma da jama’ar anguwa dama maƙwaftan anguwar wace tawagace. Tuni mutane suka fara ƴar rige-rigen fitowa daga gidajensu bama idanunsu abinci.

Sun tarbesu bisa jagoranci Kaka daya tsara komai tare da shimfiɗa kakkauran gargaɗi ga su Babiy. Bayan an musu masauki a cikin lambun Babiy ta ɓangaren garden ɗin da yayi domin farin ciki ga iyalansa aka cika musu gabansu da ƴaƴan itatuwa duk da babu tunanin ko zasu ci. Babiy, Kaka, da wasu dattijai biyu, ɗaya ta ɓangaren Babiy, ɗaya ta ɓangaren Ummu ɗan uwa ga kaka kenan suka zauna da su. Sun miƙa gaisuwa a garesu cikin mutuntawa da nuna tabbacin su ɗin masu ƙarfin iko ne a garesu talakawan ƙasan ruman. Hakan yayima dattijan matuƙar daɗi da yabama su Kaka. Dan haka suma suka nuna mutuntawa a garesu da basu ƙarfi matsayin waɗanda sukazo neman iri wajensu. Hakan ya ɗan bama su kaka mamaki amma sai babu wanda ya nuna. Sun gabatar da buƙatarsu, tare da bada duk wani abu na al’adar aure da ƙasar ruman ta tanada ninki wanda akanyi sau goma. Hakan sai ya ƙara firgita Babiy da bashi tabbacin yanda za’a salwantar da rayuwar ƴarsa ɗaya tilo data rage masa zai zama ƙololuwar girma fiye da ƴan uwanta kenan. To inbaice hakaba mizaice, dan dukiyar da suka kawo kawai tamafi ƙarfin ma sayen Iffah idan sayarwar zaiyi. Bai samu damar cewa wani abu ba, yadai cigaba da kukan zucinsa yabar su Kaka dayin abinda ya dace.

 

 

A wannan zama aka ƙarƙare komai har ranar ɗaurin aure dama inda za’a ɗaura auren. Daga haka sukai addu’a suka tafi bayan an shigo da tarin kayayyakin da sukazo da shi. Daga Babiy har Ummu tagumi kawai sukai suna kallon kayan da aka baza a tsakar gida. Hakama Hanash da dattijan nan guda biyu da sai gobe zasu koma tare da kaka. Kaka kuwa na gefe zaune abinsa tamkar baima san mike faruwa ba a gidan. Yayinda Iffah ke can ƙuryar ɗakin Ummu kwance cikin zazzaɓi data yini da shi…..

Washe gari su kaka suka wuce batare daya sake cewa uffan ga su Babiy ba akan komai. Yadai gargaɗi Babiy akan karya kuskura yace zai yi wani yunƙuri. Ya kuma sakasu killace dukkan kayan da aka kawo daga masarauta…..

Tamkar da gayya cikin kanƙanin lokaci gari ya ɗauka Shahan-shan zai yi aure, alamu kuma sun nuna ana shiryama auren da shiri na musamman duk da amaryar bata kasance ƴar kowa ba. Hasalima ahalinta nada tabon Shahan-shan a dalilin salwantar ƴaƴansu biyu kafin ita. Dukkanin waɗan nan ƙananun magana na faruwane a bakunan mutane da ƙaramar murya, yayinda a kafafen ƴaɗa labarai da fejikan yaɗa zumunta babu mai iya ɗaga murya yayin faɗa sai fatan alkairi kawai. Mutane sun sake samun tabbacin wannan aure na musammne daya sha banban dana baya sakamakon fara shelarsa a kafafen yaɗa labarai domin gayyatar manya-manyan ƙasar kamar kowane Tajwar da jama’ar majalissarsa da talakawan garinsa. Da yanda ake wasu ƴan gyare-gyare a daular ruman wai duk na tarbar zuwan ranar ɗaurin aure ne. Humm abin faɗa taf bakunan mutane sai dai babu damar faɗar. Idan kuma suke ganin zasu sami wani ƙarin bayani an toshesa dan babu mai ikon shiga gidan Babiy a halin yanzu kasancewar zagaye yake da dakaru tako ina, acewarsu suna bama *_Zawjata-almilki_* tsaro ne. A cikin gidan kuma babu mai fita hatta da Hanash dake zuwa babbar makaranta…

 

A haka kwanakin biki da suka rage suka cigaba da shurawa batare da wadda ake iƙirarin zama amaryar ta sake tada kai ta dubi wani abu daya shafi auren nata ba koda da kallo. Ta dake matuƙa tamkar ba itaba, hatta da ciwon dake cinta a tsaitsaye taki bada damar da su Ummu zasu fahimta. Ta ƙeƙashe idanunta ƙam ta hana hawaye zuba daga cikinsu. Ta tattare gaba ɗaya hankalinta ta maida ga rubuce-rubuce da babu wanda ya fahimci na minene a gidan, dan bata bari kowa ya duba mata shi. Sai dai ga duk mai hankali a duba ɗaya da zai mata zai fahimci tana cikin matsananciyar damuwa, mai busar da zuciyar mai ita da zai iya aikata komai da zai iya zama komai akan komai

Kamar ko yaushe yau ma bayan ta kammala ayyukan gidan da take taimakawa Ummu da su ɗaki ta koma tana kukan zuci daya zame mata abokin rayuwa. A idaniyarta kam babu alamar ɗigon hawaye, sai dai raɗaɗin wanda ke kwaranya a zuciya ya maida launin idanunta sirkin ja har kana iya ganin jijiyoyi a cikinsa. Duƙufe take akan littafinta tanata rubutu da sakin ajiyar zuciya akai-akai. Ummu data shigo ɗakin takai zaune a kusa da ita tana mai tsurawa rubutun idanu na wasu sakanni.

“Ibnati!”.

Karan farko Iffah ta ɗago ta kalla Ummu duk da tun shigowarta ta jita sarai. Wani irin miskilin murmushi ta saki tare da maida kanta a hankali ta duƙar..

“Kina ganin laifinmu ko?”.

Cak ta tsaya da rubutun data cigaba, sai kuma ta saki murmushi. Tsahon sakkani uku kafin ta ɗago ta dubi Ummu. Ta ɗan girgiza kanta da ajiye biron hanunta. “Ummuna idan har zanyi zargin wani akan wannan al’amarin to kaina ya dace na zarga. Ku ɗin nagartattun iyayene abin alfaharin kowane irin ɗa. Ni ya dace nazo muku da wannan maganar, domin nice na saka zukatanku a damuwa da ɗunbin fargaba. Na tabbata a kowane sakan, a kowane minti, a kowane awa, a kowane kwana na waɗan nan kwanakin kunayinsa ne cike da fargabar shuɗewarsu da gabatowar su. Kuyi haƙuri ku ƙara haƙuri ku gafarceni. Koda baku faɗamin ba, baku faɗama duniya ba nasan irin raɗaɗin da kukeji a zukatanku domin nima makamancinsa nakeji. Sai dai ina muku albishir Ummuna, koda zakuyi kuka a wannan gaɓar bazakuyi irin na baya ba. Na muku alƙawarin kukan ku zai kasance tare da dariyarkune a lokaci guda. Dan ruhina sai ya amso muku diyyar su Nina Arfa kafin yabar gangar jikina. A duk randa saƙon mutuwata zai riskeku insha ALLAHU zai riskekune tare da na mutuwar azzalumai. Dan haka ina roƙonku kar kuyi baƙin ciki a wannan karon, zaku sadaukar da ruhin da zaije muku yaƙin neman ƴancin kai ne ku da al’ummar ƙasar ruman…..”

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button