Daudar Gora Book 1 Page 120
Tunda al’amarin nan ya faru babu wanda zai ce yaji koda motsinsa a masarautar hatta hadiman dake zagaye da sashen nasa. Har masu dafa abinci da amintacen hadiminsa dakan iya ganinsa ko kai masa saƙo ma ba ganin nasa suke ba.
Abinci kuwa yanda suka shirya haka suke kwashesa. Amma hakan baisa sun gajiya ba kasancewar aikinsu ne. Yau ma kamar kullum sun tsaftato ko’ina sun kuma bajesa da ƙamshi mai taɓa kuzarin mai shaƙa. Bayan an haɗa abincinsa da duk a kwanakin nan yanda ake shiryashi haka suke zuwa su kwashe duk suka koma hawa na uku da shine dai wajen zamansu, sai amintacen hadiminsa da kawai ke da lasisin zama a hawa na karshen ne yay zaman gadin abincin gudun samun matsala duk da babu wani mahaluki a zahiri daya isa ketowa har nan ya saka wani abin cutarwa da ake tsoro
Kusan ƙarfe takwas abinda hadimin bai zaton gani ko tsammani ba yay matuƙar kidimashi. Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed ne da suka kwashe kusan kwanaki takwas batare da sanyashi a idonsu ba ke tunkaro falon cikin takun ƙasaita da izza. Cikin rawar jiki da ruɗani hadimin ya zube a ƙasa bakinsa har rawa yake wajen miƙa gaisuwa. Kamar yanda ya saba kai kawai ya ɗan jinjina batare da damuwa da hadimin ya gani ko bai gani ba ya gittashi ya wuce. Hadimin ya ɗan lumshe ido da zuƙar daddaɗan kamshin shugaban nasa yana mai sauke ajiyar zuciya a ƙasan maƙoshi.
Tajwar Eshaan da baima san yanayi ba a hankali ya kai zaune cikin kujera ya harɗe ƙafafu cikin salon zama irin na sarakan da suka isa. Sai a lokacin hadimin ya zaburo ya sake zubewa gabansa.
“Ya shugabana ko ana bukatar shayi?”.
Kansa kawai ya ɗan jinjina alamar eh yana kauda fuskar sa gefe. Da sauri hadimin da ke satar kallonsa ta gefen ido ya miƙe, haɗaɗɗen daning table ɗin mai cike da kayan breakfast ya nufa, cikin abinda baifi mintuna biyu ba ya dawo ɗauke da ƙaramin tray da butar shayi a samansa. A ɗan tebirin gaban kukerar da yake zaune ya ajiye. Ya tsiyaya shayin a ƙaramin kofin. Baya yaja sosai kansa a ƙasa cikin ƙanƙan da kai yace, “An kammala ya shugabana”.
Baiyi magana ba, bai kuma motsa ba har bayan wasu mintunan biyu. Bayan ya kai shayin bakinsa kusan sau biyu ya ɗan dubi hadimin dake tsaye kai a risine ya sake kauda kai. Maganace a bakinsa, amma sai da ya sake jan wasu sakkani kafin ya furta ta a fisge.
Tambaya mafi rikitarwa, mamaki, al’ajabi harma da ruɗaki ga duk wanda ya jita a bakin da ba’ayi tunani ko tsammani ba ce ta riski hadimin. Falon ya shiga waw-wai-gawa cikin tsumar jiki. Tabbas shine dai akaima tambayar ba wani ba. Sai duk ya sake ruɗewa ba shiri ya zube ƙasa akan guyawunsa. “Kariyar UBANGIJI da ingantacciyar lafiya su kasance ga shugabana, abubuwa da yawa sun faru marasa daɗin faɗi da sauraren ji. Sai dai ban san wanne ake bukatar na isar ba”.
Tamkar ma bashine ya buƙaci jin ba, tsahon wasu mintuna da zasu iya kai huɗu ya sake amsawa ciki-ciki.
“Komai”.
Kai hadimin ya jinjina yana mai sake ƙan-ƙan da kai, ya fara zayyano komai tiryan-tiryan tun daga randa aka ɗauke Iffah sashen har zuwa yau ɗin nan da yake gabansa. Ya kare da faɗin, “Idan na faɗi abinda ba shi shugabana ke buƙatar ji ba ina mai neman afuwa”