Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 115

Sponsored links

(Kaga ibilishiyar yarinya) ya ayyana a zuciyarsa. A zahiri kam sai yay gyaran murya cike da dattako yana kallon Miran Arshaan da shima ke sauraren komai. “Wato Ibnati duk yanda zan miki bayani a wayar nan ba lallai ki fahimta ba. Amma zan tura miki lokaci da adireshi mu haɗu zai fi”.

Jimmm Iffah tayi kamar mai shakku, sai kuma ta nisa cikin gyaɗa kai tace, “Okay babu damuwa ina jira”. Daga haka sukai sallama kowa ransa na masa kaikawo…

Cikin ƴar dariya Miran Arshaan yace, “Amma shegiyar yarinyar nan fa da zata samu dama a masarautar nan ba ƙaramin hatsabibiya za’ai ba. Kaji murya cauy-cauy bata ko tsallaken kalma ga shegen wayo”.

 

“Shiyyasa dolene tana kammala aikin nan a kaudata kawai, ai tunda har tana da ƙarfin halin shigowa masarautar nan da ƙudiri irin na kashe Shahan-shan dama nasan zamuga fiye da hakan tattare da ita. Irin waɗan nan yaran masu taurin zuciya a cikin mata basu da yawa, amma kuma kasancewar su mata ga mai mulki ba karamin ƙara samun power bane. Badan-badan ba babu abinda zai hanani tabbatar da ita abokiyar tafiyata. Dama yarinyar ga shegen ƙyau da ƙira tamkar ita ta zana kanta…”

 

Ƙaramar dariya Miran Arshaan yay idonsa akan ɗan uwan nasa. “Wato dai Jasim Akh har yanzu bazaka canja ba, na ɗauka tuni ka jingine batun son matan nan naka kodan kujerar da ke gab da zama taka”.

 

“Bazaka gane bane Arshaan Akh”. Miran Jasim ya faɗa yana tasa ƴar dariyar shima da komawa jikin kujera ya lafe ƙyaƙyƙyawar surar Iffah da bata wuce sa’ar autarsa ba na masa kaikawo. Shima dai Miran Arshaan ɗin hakance a ransa, dan tun randa suka haɗu da Iffah a wajen wasan takobi da Tajwar Eshaan yarinyar ta kasa barin ransa. Duk da dai shi yanzu kam ya ɗan rage bin mata tun aurensa da Jasrah.

 

Humm masu karatu Bara na ɗan tsakura muku wata gulma dai karna wuce. (A baya ƙiyayyar ƴan ɗakin su Miran Jasim da Miran Arshaan a bayyane take fiye data ƴan ɗakinsu Tajwar Haysam (mahaifin Tajwar Eshaan kenan) amma a wasu shekaru bayan hawa mulkin Tajwar Haysam sai aka wayi gari sun ɗinke, ƙiyayyar da sukema juna ta koma ta ƙarƙashin ƙasa. Wannan haɗin kai nasu kuwa ya samo asaline a dalilin kasancewar halinsu da yazo ɗaya. Awani lokacin bikin al’ada kamar yanda duk suka saba sun baza yaransu samo musu yara matasan ƴammata masu jini a jika da basu gaza sha bakwai zuwa ashirin ba. Karku ɗauka da yardar yaran wai ake kai musu su, ko ɗaya, ta karfin tsiya za’a ɗaukeki bayan an shaƙa miki abu ko an yaudareki, bazaki tashi tsintar kanki ba sai a ɓoyayyen gurin da in zaki kwana dubu ihu babu mai jinki. Idan sun gama lalata rayuwar yaran kuma a jefar da su. Alokacin da labarin yaje ga Tajwar Haysam hankalinsa ya tashi, dan a shekarar an samu gawar yara ƴammata kusan biyar da waɗan da aka jikata, iya bincike kuma na jami’an tsaro ba’a sami komai ba. Da shekara ta dawo kuwa yasa tsatstsauran tsaro akan kaikawon mata fiye da maza, aka kuma sake sabon tsarin yanda bikin al’ada zai kasance. Ransu Miran Jasim ya ɓaci matuƙa, dan ƙarshe sai a yaran masarauta suka huce haushinsu ƴaƴan talakawa sun gagara ɗauka. Duk da ba tare suke aikatawa ba sai shirunsu yazo ɗaya a lokacin, har ya kasance yaransu dake sato musu ƴammatan sunyi haɗaka akan yarinya rigima ta kaure, kowanne ya sanarma ogansa, a zafafe Miran Jasim da Miran Jasim suka buƙaci sanin juna kowanne da tunanin shike da ƙarfin iko, sunko haɗun a yanayin da hantar kowanne ta kaɗu dan mamaki, amma ƙwallafa rai da kowannensu yayi akan yarinyar ya sasu amincewa juna yin tarayya da ita a tare Wa’iyazubillah 😭🤦.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button