Daudar Gora Book 1 Page 109
Hakane wlhy ɗan uwa hakane. Kaina ne ya kulle a ruɗani nake gaba ɗaya. Nagode nagode yanzu kam ka bani ƙwarin gwiwa, insha ALLAHU kuma sai na bada mamaki. Dan a wannan gaɓar sai su Abu Hanash sun fita da izinin UBANGIJI, zan kuma gano koma wanene da hannu a kan ɓoyesu”.
“ALLAH ya baka nasara. Ni bara naje kar wani ya fahimci ina anan har yanzu”.
Kai kawai Barrister ya ɗaga masa yana murmushi. Wannan tattaunawa ce ta bama Barrister duk wani ƙarfi da sabuwar himma na musamman, a yanzu kama baka iya ganin komai sai murmushi tare da shi, lokacin da aka kawo masa abincin rana ya buƙaci takarda da abin rubutu. Takardu aka kawo masa bama takarda ba, hakan ko ya masa daɗi, dan ya kwashe sauran wannan yinin da dare wajen tsara duk abinda ya dace. Washe gari har ya fisu zumuɗin son fita ma, sauran da basu san miya faru ba canjawar Barrister ɗin taita basu mamaki…..
Tun kammala bayanin Abu Zainab ga su Kaka jikkunansu duk yay sanyi, Ummu ma hawaye takeyi, Barrister shine hope ɗin su a yanzu bayan UBANGIJI masanin abinda ke fili da ɓoye. Gashi a dalilinsu an rasashi. Idan har aka cutar da shi ta dalilinsu bazasu yafema kawunansu ba.
Kaka dai jinjina kai kawai yake amma komai ya kasa cewa, sai Iyyani ce cikin ƙarfin hali da sharar ƙwalla ta dubi Abu Zainab da damuwa ke shimfiɗe a fuskarsa. “Zakariyya kuyi haƙuri dan ALLAH, mun jefa rayuwarku a haɗari, ya ALLAH ka bayyana Abdullahi da gaggawa”.
Ɗan murmushin yaƙe Abu Zainab yayi, cikin danne abinda ke masa kaikawo yace, “A’a mama ai mutum baya taɓa wuce ƙaddararsa, kuma har yanzu bamu tabbatar ba ko akan wannan case ɗin bane muka rasa shin, dan Barrister da kike ganinsa nan shima hatsabibin kansa ne, gaskiyarsa da tsayuwa akan ganin tabbatar da ita yasa yanada maƙiya da yawa akan cases daban-daban hatta a cikin abokan aikinsa ma. Kinga kuwa zama ta iya yiwuwa ba’akan wannan ɗin bane…..”
“Dole ya zama akan wannan ne”
Kaka ya faɗa cikin katse Abu Zainab. Duk kallonsu suka maida a kansa. Ya jinjina kai batare da ya kallesu ba. “Ban san gaibu ba, amma inaji a jikina akan su Muhammad Zayyanu ne, sai dai kuma tabbas koma a ina yake har yanzu yana raye insha ALLAHU. Inajin wannan ƙwarin gwiwar ne a zuciyata”.
Ba ƙaramin mamaki kalaman kakan suka basu ba, sai dai kowa ya gagara cewa komai sun dai zuba masa ido. Kusan mintuna biyu gidan shiru kafin kaka ya miƙe, babu jimawa ya dawo da jakka a hanunsa. Su dai duk suna kallonsa kawai. Takardar daya zaro ya miƙama Abu Zainab. “Ungo duba wannan”.
Da sauri Abu Zainab ya amsa ya fara karantawa. Bakinsa cike da magana ya ɗago yana duban kaka da ke kallonsa. “Baba wannan kuma fa?”.
Murmushi Kaka yayi da kauda kansa kamar bazaice komai ba. Sai kuma ya ɗan taɓe baki da fara basu labarin yanda duk a kai a randa zai dawo. Ya ɗora da faɗin, “Saurayin daya kawoni gidan nan zuciyata ta bani ba haka nan ya kawoni ba….”
“Amma baba shine ka amince harma da nuna masa gida?”.
Kaka yay ƴar dariyarsu ta manya. “Zakariyya kenan, to idan baka iya kama ɓarawo ba ai shi sai ya kamaka. Ka ganni nan barni kawai inda ka ganni. Idan na nuna nasan yanada manufa a kaina tun farko kamar yanda naso nuna masa a tasha ai bazan san sirrin zuciyarsa ba. Amma dana bashi dama fa? Yanzu a tafin hannuna yake, kuma jirace nake da zuwansa dan na tabbatar zai dawo, na masa talalar da tabbas sai ya dawo da izinin UBANGIJI”.
Abu Zainab kam a yau Kaka ya fara bashi tsoro. Sai dai ya danne bai yarda ya nuna ba. Kaka ma ya fahimci haka amma ya kanne, sai jakkar ya tura ma Abu Zainab yana faɗin, “Wannan sune kuɗin dake tare da takardar”.