Daudar Gora Book 1 Page 105
“Exactly kisan irin na baya ne dai babu wani banbanci gaskiya, da alama kuma tayi ƙoƙarin kare kanta itama shine dalilin kasancewar ɗakin a haka harma da wannan jinin”.
“Wannan lamari daban mamaki yake, taya za’ai kisa amma babu wani alamar yanda akayisan, a wannan karon kodai za’a canja likita ne? Dan dole dole akwai abinda yake a ɓoye. Yarinyar nan itace ta goma sha biyar da aka rasa, kisan kuma iri ɗaya babu wani bambanci sai kace abun tsafi”.
“Haba haba wane irin kuma tsafi? Jasim Akh. Dole dai akwai abinda bamu sani ba ɗin kam gaskiya”.
“Zancena nakan hanya Ukhti Ammarah. Idan ba aikin tsafi ba mi zamu kira wannan al’amarin ne? Bagashi ita waccan da yake ta gagara ko kuma wani abu daban ta tsira babu abinda ya sameta ko ciwon kai ba”.
“Inaga yanzu duk ba lokacin yin wannan maganar bane, ayi abinda ya dace, a wannan karon kuma ya kamata Abni yace wani abu bawai ya cigaba da yin shiru ba kamar yanda ya saba”.
“Maganarka nakan hanya Miran Arshaan”. Miran Jasim ya faɗa cikin son sake tabbatar wa. Shiru Daneen Ammarah da Malikat Bushirat basu tanka ba, hakama jami’in yanata cigaba da zagaye ɗakin alamar nazari.. duk wannan al’amari Iffah na maƙure a maɓoyarta tana sauraren komai hannunta danne kan bakinta kar kukan da take ya fito har su farga da ita. Koda suka gama abinda suke bayan shigowar doctor da fitar da gawar kasa fitowa tai, sai dai ta zame ƙasa da sake fashewa da wani irin kuka mai ban tausayin dan mutuwar yayunta biyu ta dawo mata ne a rai sabu a yau ganin ta hanyar da suma suka rasasu a zahiri gabanta……
“Kuka bashi zai kuɓutar dake ba kema…”
A razane Iffah ta buɗe idanunta dake kaca-kaca da hawaye gasu jajur. Miran Jasim da tun ɗazun ya lura da ƙafar Iffah amma ya basar har sai da suka fice yayo sau da baya ne a gabanta. Duk da so ɗaya ta taɓa ganinsa ranar liyafar cin abinci da aka kawota nan hakan baisa ta shaida fuskarba a ɗan fisge.
Kai ya jinjina mata cikin ɗage kafaɗu “Yanda ya kashe na baya kema babu tantama hakance zata kasance. Karki ga ya ƙyaleki zata iya yuwuwa shirinki na musamman ne. Amma in har kin shirya kuɓuta daga tarkon sa ni mai iya taimaka miki ne”.
Iffah dai kallonsa take kamar gunkiya, sai hawayen da suka kasa tsaya mata ne kawai ke tabbatar da ita a mai numfashi. Bai nuna ya damu da yanayin nata ba ya cigaba da faɗin.
“Ni sunana Jasim Ibn Abdull-Majeed Aliy. Ƙani ga mahaifin mijikin kenan. Nasan kina buƙatar sanin abubuwa masu yawa akansa amma kinƙi samun kowacce irin dama saboda iyayensa dake zagaye da ke. Duk yanda kike zaton abin ko tsammani ya wuce nan, Malikat Haseena da Malikat Bushirat da kike gani sun san komai game da mutuwar matansa, hasalima da taimakonsu komai ke gudana, zaki iya lura da hakan a yanzu ta yanda duk muka nuna damuwa amma su ko’a jikinsu. Abinda zai tabbatar miki da sun sani kuwa duba da abinda kika ganema idonki ne, taya za’a kashe mutum amma a kasa gane hakan, sannan kuma a sake kawo masa gobe ta mutu hakan baisa an dakata ba. Waɗan nan likitoci da jami’an da kike gani duk an siyesu ne, shiyyasa suke pretending cewar basu san komai ba ko basu gane komai ba. Koda yake su a zahiri bazasuga komai ɗin ba, dan ana kashesu ne ta hanyar tsafi domin ƙarama ƙarfin mulkinsa iko…..” yaja numfashi tare da fesarwa idonsa a kanta yana nazartar yanayin tasirin da maganarsa ke samu a wajenta. Da alama akwai nasara dan haka ya cigaba da faɗin, “Mu ajiye wannan, dan bashi da amfanin cigaba da faɗa miki. Ko kin san mahaifinki da ɗan uwanki ma anyi amfani da jininsu a maimakon naki shiyyasa ke kika tsira saɓanin wannan”.