Daudar Gora Book 1 Page 103
Har waye war gari babu nutsuwata tattare da Iffah akan wannan al’amarin, dan ko barcin kirki batayi ba sam. Sai dai tuna a’a yau zata bar sashen ya saka mata ɗan jin sassauci ka ɗan a zuciyarta. Tana ko idar da sallar asubahi ta taattara kayanta waje guda tsaf tana jiran gari ya ƙara haske ta kama gabanta duk da kuwa wata zuciyar na bata shawarar take akan zuwa Tajwar Eshaan wai ko zata fahimci wata gaskiya saɓanin wadda zuciyarta ke tabbatar mata. Amma dai ta dake dan tana buƙatar damar keɓance kanta ko zata samu nutsuwa.
A bisa al’adar masarautar kamar yanda ake kai Zawjata-almilk turakar Shahan-shan haka ake zuwa a ɗakkota cikin tattali da giramamawa tare da manyan ƙyaututtuka a randa ta cika kwanaki bakwai cif. Kowa ya ɗauka tunda an kai Iffah ba bisa ƙa’ida ba baza’ai wannan al’ada ba gareta musamman yanda tama karya doka a kwana ɗaya ta fito. Ga kuma a yanda masarautar take harmutse kwana biyun nan. Amma sai Malikat Haseena ta bama kowa mamaki ta hanyar haɗa komai na al’ada da akeyi, tare da mukulllin zabgegiyar mota ƙirar zamani da masu hidima har guda goma, da tarin turarurruka na musamman, Daneen Ammarah da tsaffin dake da hurumin gudanar da al’adar a masarautar suka yima sashen Tajwar Eshaan tsinke cikin busar sarewa mai tabbatar da isar da saƙon manufar al’amarin.
Tofa wannan fa shine an tsokalo tsuliyar dodo. Dan kuma masu rajin faɗa aji tuni sun sake buɗe shafin caccakar Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed da kakar tasa Malikat Haseena kan basu damu da ɓatan Sayeed Khairul-Bashar ba. Ko kuma ma dai sun san komai ɗin da gaske. Wannan al’ada ta sake saka jikin Iffah mutuwa da shiga ɗunbin mamaki na gaske, har aka maidata sashinta babu alamar tana cikin cikakken tunaninta ma. Bin dai kowa take da ido tamkar gunkiyar da aka ƙirƙira domin tarihi…
★Ashe duk wan can ƙarami ne a abin mamaki da Malikat Haseena ta tanada a yau ɗin. Dan ƙarfe tara na dare da kanta kamar yanda tayi akan Iffah ta sake jagorantar rakiyar ɗaya cikin biyun Zawjata-almilk dake gidan tun kafin zuwan Iffah. Duk da bata haɗu da Tajwar Eshaan ba yau bata dawo da ita ba kuma dan acewarta zai ma gaji ne itama ya kulata idan ya gama zaman kulle kansa a ɗakin kamar yanda zukatansu ke basu sakamakon sanin hakan al’adarsa ce a duk sanda ransa ke ɓace.
A wannan gaɓar kam kowa ya saki jiki waccan matsalar ta shuɗe tunda ga Iffah tai kwanakinta lafiya ta fito. Maimakon shiga fargabar rasata itama sai kowa ya ɓige da ƙananun magana akan rashin dacewar hakan. Yau ɗin ma dai malikat Haseenat tayi kunnen uwar shegu da su, yayinda Malikat Bushirat da Daneen Ammarah suka shiga halin mamaki da hukuncin na Malikat Haseenat a karo na biyu saɓanin dukkan shirye-shiryen su. A wannan karon kam sun yanke ƙuirin tun kararta suji ba’asi, sai dai sun barma safiya komai….
Surutai akan ɗimuwar da aka wayi gari da shi a masarautar ne ya farkar da Iffah dake fashin salla ɗan barcin daya figeta, dama da ƙyar ta yisa sakamakon kwana da tai neman Sir Fawzan da Sir Ajmaal a waya amma bata samesu a online ba hakama a kira. Sai abinda ta karanta da yay matuƙar tada hankalinta a ɗaya daga cikin littafan da take nazarta akan Tajwar Eshaan. “Tabbas babu lafiya” ta faɗa a zahiri tana miƙewa zumbur. Har ta nufi ƙofa ta dawo da sauri, toilet ta shiga a gurguje ta watsa ruwa ta fito. Sama-sama ta kimtsa jikinta ta fito. Hadiman ta da alamun sanyin jiki ya bayyana a agaresu suka dinga zubewa gaisheta. Maimakon amsa ta jefa musu tambayar da ruɗani ya bayyana kansa a cikin idanunsu da jikkunansu lokaci ɗaya.
“Mike faruwa a masarautar nan? Da alama babu lafiya?”.
Duk sun rikice babu alamar wani zai amsa mata. Sai kaɗuwa suke kamar masu jin sanyi. Halin da take ciki ya assasa mata jin zafin hakan ta daka musu tsawa. Sake firgicewa sukai, sai dai wajibi ne a gare su bin umarninta, dan haka cikin ƙarfin hali wadda ke matsayin amintatta a gareta ta sanar mata cewar an wayi gari da rashin Zawjata-almilk ne ta farko da jiya ta kwana turakar Shahan-shan sai Sayeed Khairul-Bashar shima da aka samu gawarsa a wani ɗaki cikin masarautar. Iffah da bata san da hakan ba ta ƙame ƙam alamar sumar tsaye ta wucin gadi ce ta risketa. Sai kuma hajijiya ta fara juya mata falon da hadiman, a hankali duhu ya dinga lulluɓe idanunta data kafa musu tabbacin bata cikin hayyacinta….