Hausa Novels and Stories

Bakon Lamari 9

Sponsored links

Gumi duk ya wanke mata jikinta duk da sanyin fankar dake kaɗawa acikin ɗakin.

Muryarta a dashe irin ta mai bacci ta dube shi tana mai zare manyan idanuwanta tace masa.

“Imran meye haka dan Allah ka rabu dani, nace dan Allah ka rabu dani wallahi Allah koda duniya zaka bani bazan taɓa Kaucewa Umarnin Ubangijina akan taka buƙatar ba”

Batai aune ba taji saukar Danshin bakinsa cikin nata wanda shine ya dakatar da ita daga ƙarashe maganar data keyi a haukace yake yamutsa Dukkan sassan Jikinta yana ƙara ribatarta zuwa Cimma muradin Zuciyar s

Wani tsallan albarka tayi tare da bangaje shi tayi hanyar falo har Rigar Jikinta na zamewa ta faɗi ƙasa.

A haukace ya bita yana cewa

“Dan matsiyatan iyayenki yau babu mai rabani da ke sai Allah, an gaya miki a banza zan ke, kashewa iyayen ki kuɗi to maitar Biyan buƙatar kaina ita ke ingizani zuwa ga aikata koma meye akan mayun iyayen ki, wallahi Tun ranar dana fara ɗora idanuna a bayanki naji ina maitar Jin ɗanɗanon shi”

Ya faɗi a lokacin daya cimmata ya saka ƙafa ya taɗeta ta maku a ƙasan tiles.

Wata ƙara ta saki kafin Numfashinta ya ɗauke tsaf sai kuma Jini ya soma biyowa ta ƙafafunta.

Wanda ganin wannan yawan Jini shiya tsorata Imran yayi saurin ɗauko jallabiyar shi ya sanya ita ma ya zira mata riga da hijabi, ya ɗagata cak sukai mota ya shiga mazaunin driver yaja motar suka Nufi Asibitin kuɗi mafi kusa dasu.

Lokacin da suka ƙarasa ƙarfe Ɗayan dare amman kaman rana sai karɓar marasa lafiya ake, Abin ka da asibitin Kuɗi.

Duk wani cuku cuku yayi nan da nan aka sakata a emergency room wanda Babban likitan asibitin ya duƙufa akanta dan Ceto rayuwarta har asuba Likitan yana tare da Amatullah wadda take a tsakanin Rai kokai Mutu kokai Inji bahaushe.

Likitan ya fita yayi sallah a hanya suka haɗu da Imran wanda har ya Ɗan faɗa sabida fargabar Kada Amatullah ta rasu bai sami cikakkiyar amsa wajan likitan ba.

Sabida haka ya raɓe jikin motar shi, Shikuma likitan ya koma bakin daga.

Wayar shi ya ciro ya kira Umman Amatullah.

Idar da sallar Ummah kenan taji kiran wayarta Nana ta ɗauko mata tana ce mata Yaya Imran ne Mijin Anty.

Jikin Ummah yana rawa ta ɗaga bayan sun gaisa Imran ya sosa kai cike da makirci yace wa Ummah.

“Ummah Muna asibiti fa tun Jiya Amatullah ta faɗi take zubar Jini”

Salati Ummah ta saki tana cewa wani asibitinne gata nan bara ta gyarawa Baba jikinsa ta fito ta barwa Nana girkin Gidan.

Kwatance yayi mata sannan ya ƙara yin ƙasa da murya sosai yana cewa.

“Ummah ina ganin kamar na haƙura da Auren Amatullahi, Ummah tunda mukai aure sau ɗaya kaɗai ta bani haƙƙina Kullum nazo mata da buƙata sai Munyi dambe ganin bata so nake haƙura dan kawai Jiya nace ta tausayamin ta bani shine ta ɗauki wuƙa tace Koni ko ita to a garin na karɓi wuƙar ne yasa ta faɗi Jini ya ɓalle mata”

Yakai maganar yana dariya ta yadda Ummah ba zata ji ba.

Ummah ta kuma jan salati tana tafa Hannu tana cewa.

“Haka tai maka Imirana To bara nazo dan ubanta Shegiyar yarinya mai ƙashin tsiya tafi son na dauwa ma acikin gadarar faccaloli to wallahi ta kaso auren ta badai wannan gidan ba sai dai ta nemi wani Gidan Uban”

Imran dariya yake har yana ƙwalla Tunda yake bai taɓa ganin mayyar Kuɗi kamar surukar tashi ba haka ya kashe wayar yana ƙarasawa cikin asibitin.

Nurse ce tazo ta kira shi akan Likitan nasan ganin shi bayan ya shiga Office ɗin Likitan suka kuma gaisawa sannan Likitan ya tura masa takarda gaban shi yana mai cewa.

“Muna son ka saka hannu nan da Awa Uku za’a mata C’S don a ceci rayuwarta ita da Bebyn ta don faɗuwar data yi Jiya ya haddasa wa ɗan da ke cikinta juyawa ya koma wani ɓarin Mun samu mun dakatar da zubar Jinin da take yanzu kawai Hannu zaka saka a mata aiki A rabata da Abin da ke cikinta Duk da cikin yana wata takwas ne da kwana bakwai”

Har Likitan ya gama maganar Imran bai iya motsi mai kyau ba Ta yaya tai Ciki har ya isa haihuwa bai sani ba daga kusantarta sau ɗaya shine har zata ɗauki ciki kamar wata akuya.

“Ranka ya daɗe kabar takarda a gabanka kuma kaƙi magana”

Muryar likitan ta katse masa tunanin sa.

“Nifa likita ban gane inda ka dosa ba, wai anyi gabas da kare, yarinyar nan sau ɗaya tak na kusanceta a wata taran data yi agidana sannan kawai a wani zo ace zata haihu ni gaskiya bazan wani saka hannu ba ta Mutu kawai dan ni a yanzu bana buƙatar Wani ɗa a rayuwata”

Likitan ya dubi Imran sanda ya ƙarasa maganar Cikin gadara.

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button