Hausa Novels and Stories

Bakon Lamari 3

Sponsored links

Saukar ruwan zafin daya kunna bai kashe ba, Ajikinta shine ya bata damar farkawa daga doguwar suman data yi, A zabure ta miƙe tana dafe bangon Bathroom ɗin, Jikinta har lokacin rawa yake ga wani jiri da ciwon kai yana sake kamata.

A daddafe ta nufi falo, wanda yaci abinci aciki ya bar komai a wajan zaman sa, falon kaca kaca duk tokar Wiwi da kayan abincin daya ɓata, Raɓewa tayi ta nufi tsakar gida ta ɗauko tsintsiya da faka a tsugunne take sharar tana yi Jiri na ɗibarta Jini na zubo mata ta goshinta.

A haka ta kammala sharar takai ta zubar sannan ta koma Bedroom ɗinta ta kwanta hawaye na ɗiga daga cikin idanunta

Daga waje duk sallamar da Ameerah ƴar ƙanin mahaifinta ke yi Amatullahi bata jita ba da matiƙar mamaki Ameerah ta zauna a saman kujera tana tunanin ko Wanka Amatullahi ke yi ganin shurun tayi yawa yasa Ameerah tashi ta nufi hanyar Ɗakin Amatullahi sai da ta jima riƙe da handle ɗin ƙofa a hannunta ta kasa murɗawa ta shiga sabida gudun kada taje Ko Mijin Amatullahi na gidan, Sai dai rashin ganin motar shi da bata yiba yasa tai shahadar tura ƙofar.

Idanunta yayi mata tozali da Amatullah kwance kamar gawa a saman gado, da sauri Ameerah ta ƙarasa Gaban gadon tana kiran sunanta.

“Amatullah! Amatullah!!”

Jin shurun tayi yawa yasa Ameerah hawa gadon ta kamo Amatullah jikinta ta zaunar da ita a saman cinyarta tana mai saka hannu tana share mata hawayenta

“Subuhanallahi! Amatullah Lafiya meke damun ki naga jini a goshin ki?”

Ameerah ta faɗa cikin damuwa.

Tashi Amatullahi tai tare da nufar Hanyar falo gudun kada Imran ya shigo yagan su a ɗakin Baccinsu yayi cin mutuncin sa daya saba.

Zama sukai a falo duk A tsorace Amatullahi take, Amman hakan bai hana ta sakar ma Ameerah fuskarta sosai ba cikin jin daɗin ganin Ameeran Amatullahi tace mata.

“Ameerah daga gida kike kenan Yasu Ummammu dasu Anty?”

Ameerah ta tuɓe gyalanta tare da cewa.

“A,a daga makaranta nake, nace bara na biyo ta nan naji yaya Kukai Da Yayah Ahmad ɗin? kin kira shin kuwa?”

Jin sunan wanda Ameerah ta ambata yasa Amatullahi ta haɗe fuska tana ƙara jin takaici da baƙin cikin abin da yayi mata a ɗazu wanda a zuciyarta tai dana sani yafi cikin kwando na biyewa shawarar Ameerah data yi harta kira shi.

“Naji kin yi shuru? koba ki same shi ba?”

A zafafe Amatullahi ta kalli Ameerah tare da ce mata.

“Dallah malama rufe min baki daman wannan mai zuciyar mutanan farkon kina zaton zai dube ni, ne da fuskar tausayawa Wallahi Inda ban san Yaya Ahmad ba da sai nace Ba a jininmu yake ba riƙon sa yayi yawa bakiji yadda ya gasan magana ba, wai kada na kuma kiranshi ni matar aure ce bai ma bari yaji mai ke tafe dani ba ya kashe wayar shi”

Tana kaiwa nan ta sakawa Ameera kuka wiwi tana cewa.

“Shikenan yanzu ameerah kowa ya zuba min ido kamar bani da kowa hatta ga mahaifiyata data fi kowa kusanci dani amman ta kasa fahimtar halin da nake ciki acikin gidannan?”

Ameerah ta gyara zamanta sosai tana cewa Amatullahi.

“Maganar gaskiya duk wanda zai ganki cikin wannan daular babu mai kawowa kina cikin wata matsala, Ni kaina iya sanina kawai nasan Imran ɗan tijara ne amman zama da irin su yana da daɗi, Amatullahi ki haƙura duk da nasan Imran zaɓin Ummanki ne ba zaɓin ki ba dan Allah ki kwantar da hankalin ki kodan hidimar da yake da mahaifinki wallahi jiyannan ya ƙara Biyan wasu kuɗin da za’a ƙara duba Ƙafafun baba wanda nasan ita kanta Ummah hakan dataga yana musu ne yasa bata baki fuskar Zuwar mata da ƙarar Imran”

Wata wawiyar faɗuwar gaba Amatullahi taji yaya zata yi da kowa yaƙi fahimtar me take ciki burin su kawai daular da take ciki da kuma Kuɗin da Imran kewa mahaifanta ɓarin su.

Ita kaɗai tasan halin da take ciki ta fito fili tacewa Ameerah Imran na son nemanta ta baya ta daɓawa kanta wuƙa a ciki ta tonawa kanta asiri? Duk tsiya Imran Mijinta ne bazata so wani yaji halin da take ciki akan shiba Iyayenta kaɗai zata gayawa Wanda Ummanta idanunta ya rufe akan Imran bata saurara mata ita gani take kamar auranne bata so, Shi kuma mahaifinta ba lafiyar ƙafa ba Kullum sai an kwantar an tayar dashi Yayan mahaifinta da ƙannen shi da suke Gida ɗaya Ummanta tace musu Ƴan baƙin ciki wannan tasa suka tattara suka zuba musu idanu.

Ahmad datai tunanin zai taimaketa Shima ya bula mata tsakuwa a ido sam yaƙi Sauraranta, Tana gudun ta gayawa Ameerah duk da tasan Ameerah masoyiyarta ce ta haƙiƙa tare suka taso komai nasu tare yake amman Mahaifiyar Ameerah bata ƙaunarta ko kaɗan wanda Gudun ta ɗaya kada ta gayawa Ameerah halin da take ciki ita kuma ta kwashe ta gayawa mahaifiyarta magana ta watsu acikin gidansu wanda ya kasance Gidan yawa mai cike da faccalanci da Ƙyashi da baƙin ciki shi yasanya ko kaɗan bata yarda Ameerah tasan halin da take ciki ba idan ka cire Tijara da wahalarwa da Imran ke mata wannan sune kaɗai tabar ameeran ta sani.

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button