Bakon Lamari 11
Sannu a hankali allurar da aka yi mata ta soma sakinta Cikin nutsuwa take buɗe idanunta waɗanda sukai mata nauyi daga sama kuma suka kumbura sosai.
Da farko razana tayi da taga jaririya a gabanta idanunta Buɗe tana tsotsar Hannunta sai da ta yunƙura don ta tashi taji ba zata iya ba.
Bin jaririyar take yi da kallo sannan ta ɗauke idanunta ta mayar saman rufin ɗakin tana tuna tsayin lokacin data ɗauka bata Numfashi wato rabon ta da sanin inda kanta yake tun agidanta a ɗazu da Imran yaso yi mata aika aika tun daga nan kuma bata sake Sanin Inda kanta yake ba sai a yanzu data farka taga jaririya ɗanyar haihuwa a gabanta.
Ina ta sami jaririya? dan ita a iya saninta ba Ciki ne da ita ba bare ace ta haihu.
Sautin Kukan yarinyar shine ya saka ta Juyo da sauri tana bin yarinyar da kallo yadda take Buɗe maƙogwaro tana kuka kamar wadda tai watanni.
Da sauri Nurse ta turo ɗakin ta shigo Ganin Amatullah ta Buɗe idanunta yasa Nurse ɗin tace.
“Ma sha Allah, Amman allurar nan tayi saurin sakin ki sannu Ga babyn ki nan In mai gidan yana kusa sai ya siyo muku madara kafin ruwan maman naki ya kawo”
Gaban Amatullah ya faɗi ta kuma Bin jaririyar da kallo wadda har tari take sabida Kuka! Bakin ta ya gaza furta komai sai dai kawai ido da ta saka tana kallon yarinyar.
Bata san lokacin da hawaye ya jiƙa mata Ƙuncin taba har yana sakkowa saman kirjinta.
Bata shirya haihuwa da Imran ba, Bata so haɗa tsatso dashi ba domin tabbas tasan gaba ita abar turkewa ce wajan ƴaƴanta akan irin uban data Zaɓa musu Saka kanta tayi a saman Cinyarta tana Kuka wiwi sai ɗakin ya kaure da kuka biyu ita nayi ƴar tata tana yi.
Ko kallon yarinyar batai ba wani irin tsanar yarinyar taji har cikin ranta saboda Duk abin da ya danganci Imran bata ƙaunar shi.
Kuma adaidai nan Ummah da Imran suka turo ƙofar suka shigo.
“Yawwa daman ina mata magana akan a sai wa jaririyar madara kafin ruwan mama ya sakko sai ta saka Min kuka koda yake haihuwar fari ce”
Cewar Nurse ɗin wadda take gayawa Imran da Ummah.
Amatullah cikin ranta tana kuma jin al’ajabin cikin da babu laulayi bare alamun shi, hana rantsuwa dai Tunda taje gidan bata ga al’adarta ba wannan Kuma ta ɗauka ko fargabar Imran ce ta saka Jinin ma ya ƙafe ya daina zuwa kwata kwata ( Amatullah kenan ai fargaba tsinkar da jini take ba ɗauke shiba kedai Kice bakya cikin kwanciyar hankalin da zaki fahimci kwanakin Jinin ki )
Maganar Ummah ce ta saka Amatullah ɗago wa da sauri.
“Rabu da ita likita akwai abin da ke ranta na baƙin hali shiyasa take wannan Kuka kya kashe kanki a banza”
Amatullah ta ƙure Ummah da idanu wannan wace irin Uwa Allah ya bata marar tausayi.
Da sauri wata zuciyar tace mata shine kema zaki gwadawa ƴarda bata ji ba bata gani ba zuwan ta Duniya kenan
Cikin azama ta ɗauke ƴarta ta ɗorata saman Kirjinta tare da saka baki tana hura mata kunnenta wanda nan da nan Babyn tayi shuru tana Mayar da ajiyar zuciya.
Dan a ɗazu da take zaune a waje ita take tambaye Nurse ɗin kota san ɗakin da aka kwantar da Amatullah shine Nurse Ɗin ta nuna mata tare da bata tabbacin Amatullah ɗin ta haihu wanda shine Umman taje ta shaidawa Imran da murnarta wadda take farin cikin sun haɗa iri da Imran zasu ƙara Cin dukiya dan ita asan samun tama Namiji Amatullah ta haifa ba mace ba
Koda taje sai Imran ya nuna mata bai ma san Amatullan ta haihu ba bayan Kuma ya sani ɗin.
Haka sukai zama kamar na kurame a ɗakin har sanda Imran ya dawo da kaya niƙi Niƙi kayan jaririyar kusan kala Goma sai auduga da su pampers tare da madara haka ya dire Ummah sai faman yi masa sannu take wanda bata ma Amatullah kamar hakan ba, Dan ita ko arziƙin sannun ma bata samu ba sabida takaicin Maganar da Imran ya gayawa Ummah a waya har yau bata saki zuciyarta ba.
Haka Amatullah ta miƙe tare da taimakon Nurse Ɗin ta shiga Toilet ta gyara jikinta ta fito Nurse ɗin ce ta gyara Babyn wajan azahar ya kawo musu abinci mai rai da lafiya ummah sai saka masa albarka ake Kuma babu wanda ta shaidawa Amatullah ta haihu daga Cikin Gidan har zuwa Danginta haka suka kwana a asibitin washe gari aka basu sallama.
Imran yaso Su wuce da ita gidansu amman Ummah taƙi tace tai zamanta a ɗakinta.