Hausa Novels and Stories

Zafin Kai 19

Sponsored links

Sumayyah data dan samu kanta sai alokacin ta maida kallanta da hankalinta kan Benazir da zama abin tausayi cikin awanninsu a asibitin,

Magana takeson yi mata amma ganin gabaki daya Benazir na wani yanayi yasa ta kasa mata maganar ta dan dawo da kallanta kan Bilal da shima tin dazun ita yake kalla cikin tsananin tausayi da kulawa dan bayajin zai iya gangancin yimata abortion sbd tsoron abinda zai iya samunta kuma cikin ba laifinsa ne ba qaddara ce ta samar dashi wadda suma suke cikin nadama da neman yafiyar ubangiji tun ranar ra tsautsayin ya afka musu har yanzu kuma bazasu dena neman yafiyar Allah ba har qarshen rayuwarsu sbd shedan da kaddarar wannan samun ya afka musu.

Sabon zaman makokin da bana mutuwa ba suka dasa babu mai iya magana acikinsu kowa da tashin hankalin dayake tada zaman lafiyar zuciyarsa.

Benazir data rasa tinanin kamawa miqewa tayi jiri na neman dibanta tace gida zasu tafi kawai.

Kallanta Bilal yayi yana dago wayarsa da kira ya shigo yaga sunan dd babba ne kuma baa qin daga wayarsa idan ba babban dalili ba dan haka ya daga cikin tattaro nutsuwarsa datake kokarin barin jikinsa sbd komawan sumayyah gida da wannan cikin a yanxu babban hadari ne ga rayuwarta sbd komai ma zai iya faruwa idan Ababa ya sani.

dd babba dake babban lafiyayyan office dinsa na gida yanajin Bilal ya daga wayar kai tsaye yace yazo yanzu yanzu yana nemansa.

Rintse idanuwansa yayi cikin damuwarsa dake bayyana yana kallan su Benazir data miqar da sumayyah har sun kusa kofa yana jin kansa na sarawa da ya biyo bayansu ya bude musu mota yana kallan Benazir da idanuwanta sukai jajir cikin kulawa da sanyin jiki tareda kunyar kansa yace mata gobe da safe zasuyi magana idan ya taho daukansu amma ta kula da Sumayyan kafin goben.

Kai kawai ta iya gyada masa sbd bazata iya magana ba kuma bazata iya dagowa ta kallesaba.

 

 

 

A motar ma babu mai iya magana hankalinsa yayi mummunan tashi zuwansu gida da abinda zai iya biyowa kafin safiyar gashi dd babba na masa neman gaggawa wanda bai taba jin hankalinsa ya rabu biyu akan zuwan kiran dd babba ba sai yau din.

Yana ji yana gani dukkaninsu sukai shahadar rabuwa ya ajesu ya wuce yana sake jin fargaba na shigarsa na barinsu ya nufi gida.

Suna shiga gida suma kai tsaye dakinsu suka nufa sbd ba kowa tsakar gidan Annensu na bangaren dabbobinsa tana shara batasan dawowarsu ba,hande kuma tana daki tana baccin rana.

Kwantar da sumayyah tayi har lokacin bata ce mata komaiba sbd batasan me zata fada din ba sbd zuciyarta data kasa dawowa da bugawa daidai.

Zubewa tayi gefen sumayyar tareda rafka wani mummunan tagumi nauyin idanuwanta na qaruwa,

Sumayyah datake kallanta cikin nauyin idanuwan itama tashi tayi zaune tana kallan Benazir din da damuwa ta bude baki cikin taushin murya mara karfi tace

“Bena meya faru?

Meyasa kike cikin yanayin nan?

Wani abin ya faru ne?

Juyowa Benazir tayi da jajayen idanuwanta ta zubawa Sumayyahn sai alokacin taji hawaye na ciko idanuwanta.

Cikin mutuwar jiki da damuwa mai tsanani sumayyah ta dafa hannun Benazir din dake rawa muryarta na shiga tashin hankalin ganin hawayen dake ciko idanuwan Benazir tace

“Meya faru Bena?

Dan Allah fadamun meya faru,

Meya sameki?

Wani irin kuka mai ciwo da radadi ne ya kufcewa Benazir din mai qarfi da rshin sauti ta sunkuyar da kanta tana kasa magana.

Kukanta ya saka jikin Sumayyah daukan rawa sosai cikin tsoro da fargaba mai girma sbd duk abinda ya saka Benazir hawaye babba ne bare kuka mai qarfi irin haka.

Annensu data shigo dakin tayo alwalar sallar laasar zatayi tana ganinsu ta qaraso tana kallan Benazir datake kuka mai ciwo da radadin rai.

A tare cikin rudewa suka sake jefa mata tambayar abinda ya faru.

 

 

 

Annensu ta dago ta kalla tausayinta ya kamata saidai babu abinda zasu tare daga qaddarar da ubangiji ya doro musu saidai tasan wannan qaddarar mai nauyi ce garesu musamman Annensu da bazata iya daukan wata azabar ba da ciwon lamarin a matsayinta na uwa kuma mahaifiyar sumayyah.

“Menene Benazir ki fada mana,meya faru?”

Takardar da aka basu a asibitin ta cikin Sumayyah ta ciro daga cikik rigarta ta miqawa sumayyah sbd Anne bazata iya karantawaba, taja wani numfashi mai zafi da mutuwar jiki Muryarta a sanyaye ta bude baki tace

“Anne ciki ne kaman yanda kikai tinani……

 

 

 

Kasa qarasa bude takardar Sumayyah tayi ta tsaya cak tareda dagowa tana kallan Benazir datake hana kukanta dawowa tana kallan Annensu data dauke wuta.

“Anne, Anne, Anne” tafada hankali tashe tana taro Annen jikinta sbd yankewan da jikinta ne neman yi.

Tashi tayi hankali tashe koina jikinta na rawa ta taro Annen tana sake kiran sunanta cikin sabon tashin Hankali murya qasa qasa sbd ba daman daga muryar kada a jisu.

Sumayyah da itama tayi mutuwar zaune ta juyo ta kalla cikin tashin hankali tace kawo ruwa Anne zata siqe.

Sumayyahn bata san me Benazir take fada ba sbd suman datayi a zaunen itama.

Tashi Benazir tayi da sauri ko gabanta bata gani tana kimfewa ta sake tashi da sauri ta fice ta debo ruwa tana zuwa ta zubawa Annensu kofin ruwan gabaki daya kafin ta sake fita qafafunta na hardewa ta debo wasu ta zubawa sumayyah ta wurgar da kofin tayi kan Annensu dake jan numfashi daqyar tana dafe kirjinta dake toshewa.

Cikin tashin hankali da tsoro mai tsanani Benazir take shafa mata bayanta tana karanto mata adduoi tana kiran sunanta a hankali.

Sumayyah data dawo hayyacinta kuwa wasu hawayen tashin hankalin da baa saka masa rana bane suka tsinke mata tana jin tsoron da bata taba jinsa ba a rayuwarta yana shigarta sbd tabbas lokacinta yayi.

A hankali Anne ta dawo daidai ta dago ta kalli Benazir da idanuwanta sukai jajir ta maida kallanta kan sumayyah take suka fashe da wani irin kuka mai tsananin ciwo da tashin hankali duka su ukun a lokaci daya.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button