Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 94
“Ina nan ina jiran dawowarsa koma wani dan iska ne, aida ya tsaya danayi maganinsa!”….
Deen ya fada ransa na sosuwa da guduwar da meshi yayi, saidai ya shiga kokwanto sosai akan anya aljanunta ne wannan kuwa? Saboda bega alamun aljanu ba a abinda yaga tanayi saidai babu abinda is not possible a game da aljanu……
Dawo da ita tsakiyar su mami yayi sannan ya kunna karatun qur’ani a home theater ya kure volume din, nan da nan gidan ya dauka bakajin komai sai sautin daddadan kira’ar sheikh sudais……
A hankali fatima zainab taji tana samun nitsuwa sosai har wani daddadan bacci ya dauketa a kafadar Umm, gyara mata kwanciya sukayi Mami ta dawo da kanta kan cinyarta, Umm kuma ta daura kafafunta kan cinyarta tana mata tausa kadan kadan…….
Suna zaune a haka har aka kira sallar azahar Deen ya mike yace bari yaje yayi sallah ya dawo sai suma suje suyi dan bayaso a barta ita kadai.. Haka kuwa akayi har sallar la’asar shiya farayi kafin…..
Ganin karfe biyar tayine yasasu tashinta dan ba kyau baccin yamma, Mami da kanta ta kaita dakinta ta sata tayi wanka tayi alwala sannan ta bata kaya ta chanja ta tada sallah, ko nan da chan bata motsa ba harsaida taga ta idar da sallah sannan suka fito tare, sai a lokacin suka tuna ko abincin safe basuci ba ranar, wato cin abinci ma guri ya samu, wani tashin hankalin idan kashiga saika manta da wani abu wai shi abinci….
Dining ta nufa da ita suka tarar da Umm da Deen suna dan hirarsu ga abinci nan a jere kala kala sai kamshi ke tashi, ga tray din kayan fruits kala daban daban an ajye incase in yauma bazata iya cin abincin ba……
Da kanta ta zauna a gaban kayan fruit dan tasan bazata iya cin abinci ba, dan kallonta Deen yayi ganin ta zauna a chan gefe inda aka ajye fruit means bazata abinci ba kenan?…
Bece komai ba ya mike yana diban varieties na abincin dake gurin a cikin plate sannan ya nufi inda take…. Jan kujera yayi ya zauna a gefenta yana kallonta jajayen lebenta daketa sheki ya dibo abinci ya kai bakinta yana fadin;
“Open your mouth”…..
Dan karyar da wuyarta tayi alamun baza taci ba…..
“Kinsan abinda ake cewa dure? Like forcing someone to eat irin yanda akeyiwa babies a toshe musu hanci toh haka zan miki idan bakiyi wasa ba”..
“Gaskiya it can’t be, karya takeyi saidai in sunanta zainab dan banaso ta zama namesake dinki mami, she doesn’t deserve the name”…..
“Ikon Allah sai kallo niko inaso ta zama namesake dina, na rasa ganemaka akan lamarin yarinyarnan Saifuddeen, kace kana taimakonta amma sai kaita mata wulakanci da masifa?”……
Sosa keyarsa yayi yana mikewa yayi hanyar dakin Mami, dawo dashi tayi da fadin;
Ta kirashi da sunan mahaifinta ganin yanda yake basu instruction kamar wani ubansu, sudai sun rasa ina Saif ya dauko wannan authoritative halin nasa, tsabar san girma wani zubin idan ze musu magana kamar da ya’yansa yakeyi, insu ya musu haka toh inaga matarsa? Haka kawai yar mutane taje tana shan wahala dashi……..
“Allah ya shiryeka, ya maka albarka”….
Mami ta fada ganin ko ajikinsa yayi wucewarsa ya barsu a gurin…….
Kamar yanda ya fada ko haka akayi, suka sata a tsakiya shikuma yasa pillow a kasa ya kwanta a parlourn dan yasan in yace ze hau kujera babu wacce zata daukeshi kasancewarsa giant mutum…….
Su Mami da Umm na bacci sukaji shesshekan mutum, Mami ce ta fara farkawa taganta tana sallah tana kuka sannan Umm itama ta farka, sosai ta basu tausayi sunata tinanin abinda yake damunta haka, dan daga jin irin kukan da take kasan wani abu damunta sosai amma ba karamin burgesu tayi ba da take kaiwa Allah kukanta, so suke su tashi suma suyi sallar amma basa so su katseta, haka suka kasa bacci suna mata addu’a daga kwancen har akayi sallar asuba sallar asuba…..
Mikewa sukayi kowa da abinda yake rayawa a ransa akan abinda suka gani, a gaban idonsu tafi hour biyu tana sallah tana kuka a hakanma basusan tashinta ba……
Alwala suka dauro sukayi sallah suma sannan suka shiga lazimi har lokacin itama bata tashi daga kan sallaya ba….