Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 4
“I need 5m today!” ta fada ba tareda tabashi amsar maganar wayar ba” zaro ido yayi yana mamakin me zatayi da kudin,shi ba kudin yakeji ba,aa me zatayi dashi……. “Okay amma saidai in turo miki 1m kinga baa mana salary ba yanzu,gashi nayi lots of things recently,but I promise you ana mana salary,you’re my first budget,kinsan I always put you first my reality”….. Tabe baki tayi tace “ka tambayi ubanka mana!”…..Sai yaji wani abu yadakeshi har cikin kwakwalwarsa,amma ya daure yace…“Oh yeah,your wish is my command ma’am,besides you promise to pay me a visit over here,yaushe zakizo?”…… “Duk sanda naga dama!”….. Ta fada a gadarance, badan sanyin murya da Allah ya mata ba da yace she’s the perfect definition of ‘if rude and arrogant was a person’!,amma waya isa ya fada to her face,besides he loves her flaws ma!……….
“Amma dai baa hotel dinnan zaki kwana ba ko habibty?” Ya fadi abinda ke ranshi tin dazu kamar me tsoron magana……. Ko kulashi batayi ba,ya kara cewa “kinsan people are so judgemental!”….. Kallon da bayaso ta mishi tace “Stop going through corners and say the hell that’s on your mind ,kaji na taba ce maka niba yar iska bace?,ko nayi denying shaye shayen da shima indirectly kace inayi?toh sai akayi yaya dan anyi judging dina,who cares?,just go to hell!”Ta fada tana cutting call din dan already taji idanunta sun fara giving up,dama tayi expecting hakan,tana cutting call din ko wani nannayyen bacci ya kwashe ta…… Shiko sai kiranta yake taki picking,chan ya fara jera mata messages,ko Allah zaisa tayi reply,still no reply,ajiyar zuciya ya dinga saukewa a jajjere,kuma mamakinta na kara kasheshi,be taba ganin mutum da abu kadan da baikai ya kawo ba yakesa shi zama so pissed off irinta,duk wayar da zasuyi ko haduwar da zasuyi saiya dinga lura da abinda ze fada kawai sbd karsuyi fada,amma ina dole saitayi picking offense….. Hannunsa ya dafe daidai saitin zuciyarshi yace”Allah dai yasa bakece ajalina ba Fatimah Zainab!”……
“Dad it’s so urgent!”…… “It’s alright,zan turo maka yanzu”…., “Thank you dad”….. Befi 5mins ko da sauke wayar ba yaji alert,murmushi yayi tina irin karyar daya gama masa yanzu……. A take ya tura mata,sai kuma ya kuma tura mata small msg saying “You make things hard,but I still love you hard!”……… Itako bata masan abunda akeba tanata baccinta abunta…..
A hankali ya fada duniyar tinaninta da abubuwan da har yau ya kasa samun amsa akai,wato “WACECE ITA?”,yana fatan Allah ya bashin aran rai haryasan wacece ita?,sai kuma ya koma tinanin ranar daya fara ganinta,ranar da baze taba mantawa ba……
A gajiye ya shigo gurin 1am na dare,dawowanshi kenan daga UK,ya kawo musu surprise visit,yanda kawai kowa saidai ya ganshi da safe,murda kofar main parlor yayi,by luck saiya samu kofar a bude duk da beyi expecting ba,karar shara yaji daga far end din parlour,bin ko ina ya farayi da kallo harya hango ta…… “Hasbunallahu wa ni’imal wakeel,fata barakallahu ahsanul khaliqin,tsarki ya tabbata ga ubangijin daya tsara wannan halitta!”ya fada yana binta da kallo,kamar yanda take binsa da kallo……Wayam kuma sai yaga ba kowa,kamar wacce ta bace,kalle kalle ya farayi yana neman inda tabi amma bega ko alamun giftawar mutum ba,sai kawai yaji wani tsoro ya kamashi,yace kodai gamo yayi ne sbd shidai yaga halittar da duk wani lafiyayyan namiji bazai mata kallo daya ya dauke kai ba,saiya faro karanto duk adduar da tazo ranshi,daga wannan rana,daga wannan lokacin kuma bai kara gane kanshi a duk wani abu daya shafeta ba,ya sadaukar mata da komai nashi,harda rayuwarshi,take janshi kamar rakumi da akala…… Girgiza kai yayi ya cigaba da tinanin abinda ya wakana a ranar, a tsorace ya karasa cikin bedroom still yana ganinta a idonsa,yana cigaba da addu’a inma gamon yayi toh……. Wayarshi ce tafara ringing ta katseshi daga duniyar tinanin daya lula