Rabi Danja Hausa Novel Page 2
“Rabi zonan”, Baba ya ƙira ta, ta taga ta ƙyallo idanunta manya dasu sunyi zuru-zuru ta ce “Baba na gaji bacci zanyi, idan ma na fito zancen ɗaya ne zaku tambayeni ne mai nayi wa wannan mutumin, kuma ba haka kurum na zage shi ba, masifa naga yana yiwa wata mai saida Ƴar bagalaje shine na zage shi, kai wallahi na gaji bacci zan Baba na gaji”, tana gama faɗa tabar jikin tagar tayi kwanciyarta a kan gadon Innarta.
Fatan shiriya sukai mata dan lamarin Rabi yanzu ya fara sawa suna tunanin anya ba Aljanu ne a jikinta ba, dan idan tana abu kamar ifritu, bata ji ta addabi maƙota da mutanen gari, kullum ne Allah mai kullum sai an kawo ƙararta daga sassa daban-daban na wannan gari, shi yasa aka sa mata *RABI DANJA*, hatta baƙo yazo garin to indai ya haɗu da Rabi saita san yadda tayi ta nemi tarangahuma awajensa, Iyayenta har taimako suke nemowa Rabi amma abu kamar gaba-gaba yake, yanzu Addu’a kawai suke mata.
Saida taci baccinta hankali kwance ta farka da ƙiran sunan Allah a bakinta tare da Adduar tashi daga bacci, sunan Inna take ƙira, Inna dake Madafa tayi mata banza tana cigaba da sakin ɗanwake.
Gajiya tayi da ƙwallawa Inna ƙira ta buɗe ɗakin ta fito tana mitsitstsika ido, buta da ɗauka ta nufi bayan gida bata jima ba ta fito tayi Alwala tayi sallarta kamar ba ita ce wannan RABI DANJAR ba mai neman tashin hankali kullum, tana idarwa dama sallar la’asar ce, zuwa tayi ta gaida Inna da take madafa, amsawa tayi tare da nuna mata kwanon Abincin ta, kalla tayi ta ce “zan ci Inna bari naje gidan su Kattume na amso littafina yanzu zan dawo, kafin Innar tayi yunƙurin mata magana ta fice a guje, girgiza kai Inna tayi.
Tana fita tayi cikin unguwa, cincirindon mutane ta gani shiya ɗau hankalinta ta nufi wajen, ture mutane take a wajen tana kutsa kai wajen dan ba tsawo ne da ita ba balle ta gani daga baya, tana isa ta hango faɗa ake wasu mata sai dambe suke a bakin hanya kuma gasu kitika-kitika, sai yagar juna suke suna nishi, wata tsohuwa sai son raba su take ta kasa da take sai a bangajeta ta dawo baya, faɗi take “wallahi Biba da Baraka kun shiga uku a rayuwar ku, kishi hauka ne kunzo bakin hanya kuna saida hali, kamar balamomi, shashashun banza da wofi”, sosai take faɗa har jijiyoyin wuyanta suna fitowa sa bo da masifa.
Rabi tana tsaye ta gama haddar abinda wannan tsohuwar ta faɗa, ta matsa kusa da matan da taji ance kiahiyoyin juna ne basuyi aune ba suka ji idanuwan su cike da ƙasa rabuwa sukai da juna kowacce ta fara murza ido tana son ganin ta ya dawo, ɗayar ce ta ce “Kutmar ubancan Biba ni kika watsawa ƙasa dan kaza-kazan ki tsinanniya jaka, wallahi yau koni koke”, wadda aka kira Biba dake hidimar goge ƙasar da ta cika idanunta ta ce “Au ni zakiwa ɗiban albarka matsiyaciya ballagaza ki watsan ƙasar kice ni na watsa miki, to wallahi ni barkono zan watsa miki idan kika sake na buɗe ido na ganki”.
Rabi dake tsaye tana ta tintsira dariya jama’a suna kallon ta suna ganin ƙarfin halinta, Tsohuwar nan ma kallonta take ita a tunaninta ma Yarinyar taɓaɓɓiya ce, wasu a wajen suna Rabi ta birge su da tayi haka wasu kuma da suka san Rabi suke jin haushinta suka hau zagin ta, suna ai zata aika tayi wanda yafi haka ma.