Nihad Chapter 14 Hausa Novel
Karfe biyu saura Nihad suka iso gida tare da farooq, yana kashe motar ta bude ta sauka, kallon direction din Mai gadi dake kulle gate tayi bata ga khalil ba, ta juya ta wuce cikin gida, direct part din Umma ta tafi, Umma dake parlonta tace “Oyoyo, har kun dawo?” Nihad tace “Ehh Umma, yau dai in gaya maki bata yi kuka ba da xa ku tafi” Umma tace “Toh ai gwara haka, kukan ba shi da amfani” Nihad ta xauna gefen Umma tace “Umma guess what?” Umma tace “Aa…
Umma tace “Toh ai gwara haka, kukan ba shi da amfani” Nihad ta xauna gefen Umma tace “Umma guess what?” Umma tace “Aa…
Karanta>>> Idan Ba Ke Complete Novel Document
ni kinsan i am not a good guesser, gaya min abinda ya faru daughter” Nihad na Murmushi tace “Umma Aliyu xai xo gidan nan yau” Shiru Umma tayi tana kallonta babu ko kiftawa, can tace “Wani Aliyu?” Nihad ta wara ido tace “Aliyu dai Umma” Umma tace “Amma ba kince min ya daina daga kiranki ba?” Nihad tace “Ehh wllh, kawai sai na ga kiransa jiya Umma, he called me him self” Umma ta girgiza kai tace “Nihad…. Nihad, bakya ji Nihad, baki jin magana wllh, na gaya maki ki raba kanki da Aliyun nan kin ki ji, ban san yanda xan yi da ke ba kuma, Aliyu ba komai xai yi ba illa ya yaudareki ya kama gabansa, nace ki daina hada kanki da ya yan masu kasar nan, Aliyu ya fi karfinki, ki kula dai dai ke amma kin ki ji, yaudarar ki kawai yake idan kin bibiya ma an sa masa rana, su da junansu suke aure basa auren kasa da su” Nihad tayi narai narai da ido tace “Umma wllh ba yaudarata yake ba, Aliyu yana so na, kuma yace min ina shiga level 3 xai turo iyayensa wajensu Abba, wllh haka yace min ranan nan Umma” Umma ta bude baki tace “Ehh Lallai ke shashasha ce mahaukaciya, shi Aliyun ne xai turo iyayensa gun Abbanku? Nihad nace ki daina kai kanki inda Allah ba kai ki ba, shi uban Aliyun ne xai bari ya aureki ko uwarsa?” Nihad ta hade rai tace “Ni dai kawai Umma ki gaya min abinda xan girka masa…” Umma tace “Girki? Shi yace ki yi masa girki?” Nihad tace “Aa, amma daga Abuja fa xai biyo flight ya xo, kin ga ai ya kamata in ajiye masa abinci” Umma tace “Aa babu wani abinci, a xuwan farkon ne xaki yi masa wani girki? Ai ba a girki sai in mutum ya xo ya fi sau biyar, kawai ruwa xaki ajiye masa da lemo…” Nihad tace “To snacks fa?” Umma tace “Toh shkkn xan maki small chops ki ajiye masa” Nihad tace “Toh Umma nagode, sai in taya ki?” Umma tace “Aa ba sai kin taya ni ba, kawai ke dai kije ki shirya” Nihad tace “Toh Umma, amma parlon visitors din Abba xan shigo da shi ko?” Umma tace “A wani dalili mutumin da babu wanda ya san sa a gidan xaki shigo da shi parlon baƙin Abbanku? Ai daga waje xaki ajiye masa kujera fari ya xauna” Nihad tace “Umma fa har na gaya ma Ya farooq shi yace in ajiyesa parlon baƙin Abba” Umma tace “Toh shi wannan wawan me yas ani?
A xuwa na biyu ko uku shine xa a shigo da shi cikin gida” Nihad dai tayi shiru, Umma tace “Yanxu dai tashi ki je ki shirya, nima xan tashi inje kitchen in yi abinda xan yi” Nihad tace “Toh” Daga haka ta mike ta fice daga parlon Umma ta bi ta da kallo, Nihad na komawa dakinta wanka tayi ta dauro alwala ta fito, tana xaune kan darduma bayan ta idar da sallah tana danna wayarta Mumy ta shigo dakin, Nihad ta ajiye wayar tana kallonta tace “Umma ina yini…” Sai kuma tayi saurin cewa “Au Mumy ina yini?” Mumy tace “Ban yini ba, dama jira kike in shigo in gaisheki da ku ka dawo?” Nihad ta xaro ido tace “Aa wllh Mumy, dama yanxu nake son idan na gama addu’a in je in gaisheki” Mumy tace “Toh yayi kyau, ai naha addu’ar kike yanxu” Nihad tayi Murmushi tace “Ya jikin su Sudais Mumy?” Mumy tace “Ban sani ba, kin shiga duba su ne da kike tambayata” Nihad ta marairaice tace “Umma wllh yanxu nake son in je” Mumy tace “Kika sake ce min Umma xan bata maki rai wllh Nihad” Rufe baki Nihad tayi, Mumy ta juya ta fita daga dakin, tashi Nihad tayi ta bi bayanta, suna komawa bangaren Mumy tace “Ina suke Mumy?” Mumy tace “Suna tsakar gida, hope Nihal bata yi kuka ba yau, na dai kirata daxu tace tun 11 ku ka ajiyeta” Nihad tace “Ehh Mumy bata yi kuka ba ta fara xama big girl, Mumy Kinsan me?” Mumy tace “Ina jin ki” Nihad tace “Mumy Aliyu xai zo yau” Mumy tace “Wani Aliyu?” Nihad tace “Lahh, Aliyu da nake baki labari mana” Mumy tace “Ohk, toh Allah ya kawosa lafiya” Nihad tace “Ameen” Mumy tace “Me xaki tanadar masa?” Nihad tace “Mun gama maganan wannan da Umma” Shiru Mumy tayi tana kallonta, Nihad tace “Bari in dubo su Fadil” Daga haka ta fita daga parlon, ganin basa main parlor din gidan kawai ta fita compound, nan ma ta bi compound din da kallo bata ga kowa ba sai Aminu a bakin gate, ta karasa tace “Kai Aminu ina su Fadil?” Aminu yace “Barka da dawowa Hajiya” Nihad tace “Su sudais nake tambayarka” Aminu yace “Ayyo suna can tare da khalil, da a nan ma suke” Ta wani yamutse fuska tace “Waye kuma haka?” Aminu dai yayi shiru yana sosa kansa, tace “Wai wannan driver din?” Aminu yace “Ehh Hajiya” Tace “Kan bala’i, me suka je yi wajensa” sai kuma ta juya da sauri ta bar wajen ta nufi chalet ai ko ta ga takalmansu a bakin kofa, nan da nan taji ranta ya baci, yanxu cikin kazantaccen wajen nan ya shiga da su salon su ki warkewa, k’in shiga parlon tayi ta xaga ta bayan windown dakin da tasan yake ciki, ai ko a bude ta tadda window din an dage labule, can ta hangosa xaune far end of the bed da waya karama kare a kunnensa, su kuma kannen nata suna kwance kan gadon ta jikin bango suna game, ƙafafuwan su kadai take hangowa, a fusace tace “Uban meye ku ke a nan Sudais?”
Da sauri Khalil ya juya yayi stretching hannunsa ya amshi wayar hannun Fadil keeping the phone under the bedsheet, duk kannin nata suka taso suna kallonta, Sudais yace “Aunty Mumy ce tace muje mu yi ball a waje” Tace “In fasa maka kai a wajen, ball din kenan? Kun shigo nan salon wari ya kashe ku ko? To wllh idan baku taso ba ku ka bari na shigo duk sai na xane ku a wajen nan, meye hadinku da shi?” Duk suka nufi kofa, ita ko ta dinga hararan khalil da ko kallon inda take bai sake yi ba, ta ja wani dogon tsaki ta juya ta bar wajen. A bakin kofar chalet din ta tarar da su suna sa takalmansu, ta ce “Uban meye ma ku ke yi a ciki? Waye yace ku shiga ciki?” Fadil yace “Game mu ke yi da wayarsa ya ba mu” Ta tafe hannu tace “Shi game din nokia phone din ne ya burge ku? Toh daga yau na sake ganin ƙafafuwan ku a hanyar wajen nan sai na xane ku da dorina” Tana gama fadin haka ta fixgo hannunsu suka bar wajen, Sudais yace “Aunty irin phone dinki yake da shi” Nihad ta kallesa tace “Wa xai basa irin phone dina?? Ai har ya mutu” Fadil yace “Irin naki da na Aunty Nihal ne, exactly the type of ur own…” Nihad tayi dariya tana jinjina shashancin kannen nata tace “He can neva have the type of my phone till he die Fadil, my phone is over a million, kasan kuma meye million?” Sudais yace “Har da Diary Milk chocolate ya ba mu each, Kuma Aunty yana da su da yawa a jaka, ni dai i want him to be my frnd…”
Muryar Umma ta ji tana kiranta ta sake kannin nata ta shiga parlor da sauri tace “Na’am Umma?” Umma tace “Yauwa nayi kokarin in ma Hafsah transfer taje kasuwa tayi min chefane babu network, ke idan kina da network ki mata ta je da sauri ta dawo yanxu” Nihad tace “Umma ba akwai abubuwan a freezer ba? Meye babu?” Umma tace “Aa ba komai bane akwai Nihad, ki mata transfer din in gaya mata abubuwan da xata siyo min” Nihad tace “Toh bari in dauko wayata” Daga haka ta wuce sama xuwa dakinta, tana dauko wayar ta tura ma Hafsah dubu sha biyar, tace “Umma na tura mata 15k” Umma tace “Toh shkkn, je ki ki shirya” Nihad ta koma sama. Tana fito da kayan da xata saka wayarta ya fara ring tana dubawa ta ga Aliyu ne, ta daga yace “Flight dinmu xai taso yanxu in sha Allah” Nihad ta wara ido tace “Toh sai ka iso, Allah ya tsare” Yace “Ameen” katse wayar yayi, nan ta hau shiryawa da sauri, kaya kawai ta saka bata shafa komai a fuskarta ba ta fito, tana sauka downstairs fridge ta fara dubawa taga wani drinks ne a ciki, duk yawancin drinks din Aliyu bai damu da su ba, his favourite drink is Can coke, sai kuma Hollandia milk, rufe fridge din tayi ta koma dakinta ta dauko Atm card dinta ta fito, ta gyara dankwalin dake kanta ta fita compound, gun Aminu ta nufa, yana xaune da Khalil a gefensa, ko kallon khalil bata yi ba tace “Aminu xan ɗan aikeka supermarket yanxu” Yace “Toh Hajiya”
Ta mika masa Atm card dinta tace “Pack din coke na gwangwani xaka siyo min ka bude kunnenka da kyau na gwangwani na aikeka ba na gora ba, sannan ka siyo pack din Hollandia milk, amma farin ba jan ba….. farin ba jan ba, tamm don kana min shirme sai ka shanyesu tass ka biyani kudina” Ya amshi Atm card din yace “Toh Hajiya, in sha Allahu” Tace “Ka tuna password din?” Yace “Aa ya kwanta min wllh” ta saci kallon khalil da ko inda take bai kalla ba, ta yatsine fuska tace “Mu je kofar gida in gaya maka” Yace “Toh” Da sauri ya fita gate din, ta wuce ta gaban khalil xata fita kofar gida ba tare da ta damu da cewa babu gyale a jikinta ba, sai a sannan Khalil ya bi ta da kallo, tana fita waje ta kulle gate din ruf, tana kallon Aminu ta gaya masa pin din tace “Saura kuma kaje ka min wasa da Atm a titi, dama kana dawowa ko tsayawa kar kayi a bakin gate ka kawo min Atm card dina kada aje a min sata” Yace “Toh Hajiya” Daga haka ta bude gate ta shigo gidan, tana tafiya kamar baxata taka kasa ba tana yi tana yatsine fuska ta wuce khalil, juyawa tayi xata kallesa suka hada ido ta galla masa wani shegen harara ta rike kugu tace “Da bashi ne?” Yace “Ke xan tambayi wannan” Buda baki tayi tana kallonsa da mamaki, can ta dawo fuska daure tace “Kace me???” Shiru yayi yaki cewa komai yana kallon sky, tace “Aa in ka isa da ka maimaita ai tunda kai baka da kunya fitsararre kawai” Ya kalleta yace “Me kike son in maimaita wai” Tace “Ban sani ba” Yace “Ohk, amma tunda har kika ga ban saci abubuwan ki masu muhimmanci dake jakarki shekaranjiya ba, ba kuma wani satan da zan maki, ko duk cikin muhimman kayanki akwai abinda kika nema kika rasa, har kwalban nan ban ta6a ba ai” Tayi masa wani kallo tace “Wani kwalba??” Tashi yayi, yayi mika ya nufi gate ya fita ya bar ta nan a tsaye, ta bi sa da wani irin kallo, sai kuma ta juya ta bar wajen. Xama tayi parlor ta jira har Aminu ya kawo mata sakonta da Atm card sannan ta xuba su a fridge ta wuce sama. Har bayan kusan minti talatin Hafsah bata dawo ba, Nihad da har ta gama kwalliya ta kashe dauri ta fito parlor ganin Umma a xaune tana kallon wani film tace “Umma ya fa kirani 30 mins ago yace xa su taso” Umma ta kalleta daga sama har kasa don ba karamin kyau tayi ba, kamar wata balarabiya, atamfar yayi mugun amsar jikinta, ga make up din tayi sa very light, she look so beautiful, Umma ta tabe baki tace “Toh gantalaliyar bata dawo daga kasuwan ba har yanzu, ni ma har na gaji da jira abinda ya sa na xauna parlon kenan ina jiran dawowarta, don ma ai ba wahala cikin lkci kankani xa a gama…”