Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 79

Sponsored links

Idanunsa dake a wani irin yanayin da ya tilasta mishi saka gilashin ya ɗan lumshe yana sake buɗewa a kanta. Cikin dakewar muryarsa dake ɗan shaƙe fiye da koda yaushe data sani kamar wanda akaima tilas acan ƙasan maƙoshi ya furta, “After Isha ki sameni”. Idanunta ta buɗe a firgice, sai dai shi tuni ma har yayi gaba abinsa. Dai-dai yana ƙoƙarin ficewa taji kamar ta fasa kuka, amma sai ta haɗiyesa tana ƙoƙarin aro jarumta. A hankali ta furta, “Zanje na ga Ammie to kafin sannan Please”.

Cak ya dakata sai dai bai juyo ba har na wasu sakkani. Kin san dai kina a ƙarƙashin umarnin shari’a ne ko?”.

Kanta ta jinjina kamar yana kallonta, kafin ta ce, “Eh na sani, alfarma kawai nake nema. Jiya ranta ya ɓaci, matsayinta na mahaifiyata bai kamata na kwanta cikin nutsuwa ba tana fushi da ni. Ina son naje gareta domin neman afuwa”.

Gaba ɗaya jijiyoyin jikinsa ne suka ƙarasa saki, wani sanyi na ratsa masa tun daga kan yatsun ƙafa har tsakkiyar kansa. A sannu ya waiwayo ya zuba mata idanunsa. Kallo yake mata irin na kin mamaye komai da komai ɗin nan, a zahiri kam baka isa tantance komai bai tattare da shi, dan fuskar na’a yanda taken nan tsuke tamau. “Ki jira ni”.

Ya faɗa kai tsaye dai-dai yana ficewa. Numfashi ta sauke a hankali da yin ɗan baya kamar maijin jiri ta manne da bango, mamaki takeyi, mamakin kanta da komai ma, ta wani gefen kuma ta fara tsoron abubuwan da ke neman cigaba da wajabta kansu a ƙarƙashin mafarkinta, toso ture wannan amma zuciyarta nata ingizata akai, abu mafi ɗaure kai kamar yanda tai mafarkin ta tambayesa zuwan a mafarkin a zahirin amsar da ya bata acan ne anan ma, mi hakan ke nufi? Tayaya ma kanta zai cigaba da ɗauka, gaba ɗaya sai kewar iyayenta ta sake dawo mata sabuwa a zuciya, ta shiga jan ajiyar zuciya hawaye na ciko mata idanu. Iska ta ƙara fesarwa ta buɗe idanunta tana sakin murmushi, murmushi mai ciwo da ita kaɗai ta barma kanta sani sai ALLAH. Sai kuma ta taɓe baki kaɗan da tuno furucinsa. _Wai ta sameshi, to ta sameshi kamar ya? Itakam wace ƙaddara ce ma ta sata amincewa auren mutumin nan? Jibafa yanda yake wani ɗacin rai da ɗa duniya bashi ya gama murje mata lips da jikinta ɗazun ba, halan ma wai ya manta tsiyar da ya aikata ne. (Ko zaki tambayosa) zuciyarta ta ayyana mata. Zabura tai cikin masifa da tsiwa kamar zuciyar tata mutum ce, sai dai kuma batace komai ba aka dai cuna bakin gaba. (😂Gwara dai kiyi shirun ta gidana)…..

Zuwa yanzu labarin abinda ke faruwa da iyalan Miran Jasim ya gama kewaye cikin masarautar. Hasalima babu wani ka-ce-na-ce dake kai kawo sama da zancen. Musamman da ya kasance Umm Husam na ƙarƙashin kulawar likitoci har yanzu, duk da dai Alhamdullah sun sami nasarar mata ɗorin karayar data samu a cinyarta. Amma taji

mummunan ciwo a ƙashin bayanta da bama a saka ran zata iya ƙara cigaba da takawa da ƙafafunta. Malikat Haseenat ta fita dubasu a asibitin har shi Miran Jasim ɗin dan shima dai ya jigatu a hannun Husam ƙwarai da gaske. Lokacin da take fitowa bisa rakkiyar Daneen Ammarah da hadimanta amintattu irin su Banou tawagar Tajwar Eshaan ke gabato Clinic ɗin shima. Malikat Haseenat ta kafeshi da idanu na tsahon lokaci, yanda yake tafiya ɗaɗɗaya cike da ƙasaita da izza, ga wani mayataccen ƙamshinsa da tun kafin ya iso shi ya iso hancinansu. Sai dai fuskar ciɗin-ciɗin fiye da kullum alamar akwai ɓoyayyar damuwa tattare da shi. Idanu ta ɗan lumshe tana ɗan murmushi da jin tarin ƙaunarsa na sake mamaye zuciyarta. Tana ma jikan nan nata so mai ƙarfin gaske da itama bata san adadinsa ba. Zubewar Hadimanta bisa gwiwunsu ya fargar da ita isowarsa gab da su. Itama ƙasa tai da kanta alamar girmamawa garesa. Tun kusantowarsu wajen idanunsa shima na’a kanta, sai dai bashi da damar tsayawa gareta kasancewar a Shahan-shan ɗin sa ya fito ba jikanta ba. Har cikin ransa yana ƙaunar wannan baiwar, ƙauna irin wadda shi kaɗai ya barma zuciyarsa sani.

Sai da suka shige sannan ta dubi Daneen Ammarah tana murmushi. Itama murmushin tai mata sai dai batace komai ba suka nufi motar da suka zo Clinic ɗin a ciki.

 

 

 

Fuskar nan a matuƙar tsuke cike da barazanar da ke sake fidda ainahin kwarjininsa yake duban Miran Jasim da gaba ɗaya yake jin ya ruɗe bazai iya ma haɗa ko ido da shi ba. Gaba ɗaya yaron ya sake masa wani kwarjini mai ban mamaki fiye da da. Duk da ya tako zuwa Clinic ɗin ko uffan bai furta ba sai kaifafan idanunsa da ke sakaye a gilashin nan dan ɓoye yanayinsa da ya zuba masa. Sai su Sayeed Fayzul-haq ne ke tambayar lafiyar tasa da yawun Tajwar Eshaan ɗin. Shiko ko sau ɗaya ma bai motsa lips ɗinsa ba a wajen, hasalima shi hankalinsa kamar rabi da rabi ne a tare da su nan kawai. Basu wuce tsaiwar mintuna biyar ba suka nufi ɗakin da Umm Husam take itama. Itako ganin Tajwar Eshaan da kansa yazo dubata sai ta fashe da kuka. Idanunsa ya ɗan lumshe kawai, sai Sayeed Fayzul-haq ne ke bata haƙuri. Nan ɗin ma dai basu wuce mintuna biyar ɗin ba suka fice.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button