Daudar Gora Book 2 Page 77
Da wani irin zazzaɓi mai masifar zafi da ƙullewar ciki ya fito da ga bayin, amma kasancewar sa jarumin jarumai ya shanye komai yana cigaba da ƙoƙarin shanye wanda ma ke taso masa sabo. Babu kowa a ɗakin da alama Iffah ta gudu, dan rigarta da ya cire ce kawai yashe a ƙasa, sai dai babu after dress ɗin da alama ita ta saka ta fice. Samun kansa yay da ɗan sakin wani miskilin murmushi yana cije lips ɗinsa da azabar ƙarfi.
Duk yanda yake son dannewa hakan ya gagara, dan wannan shine karo na farko da ya iya nisan kiwo da mace kamar haka. Hakan na nufin ya tsokaloma kansa abinda ya fi ƙarfin jarumtarsa, dan yanda cikinsa ke cigaba da ƙullewa har numfashinsa ya ɗan fara fisga lokaci zuwa lokaci. Duk da sanyin da ya fara ji na ratsa shi bai iya ya canja bathrobe ɗin jikinsa ba ga sumarsa ma jiƙe take da ruwa ya kai kan gado da ƙyar ya zauna, zufa yake ga jikinsa na tsuma abun kamar wani tsafi. Addu’ar da duk tazo bakinsa ya fara ambato da damƙo fillon data runguma ɗazun ya matse cikin hannunsa da azabar ƙarfin da ke bayyana asalin gwarzantakarsa. Wannan ranar yake gudu, wannan ranar ya ɗauka tsahon shekaru yana kaucemawa. Amma duk da haka sai da ta zo masa a gaɓar da bai shirya amsarta ba. Gaɓar da bai shirya fuskantarta ba. Gaɓar da bai shirya komai na yanda zai fara gudanar da ita ba. “Ya arrahaman”. Ya furta a hankali komai na masa kaikawo cikin gizo. Ya tabbatar idan har aka cigaba a haka to tabbas yau aiki zai buɗe, dan babu shakka kwaɓarsace zatai ruwa. Da ƙyar ya iya miƙewa, maganin da ya jima da daina sha ya shiga nema a inda ya tabbatar ya killacesa, da ƙyar ya samosa dan yayi nisa kasancewar ya daɗe da kauda idanunsa a shansa saboda abinda ka iya zuwa ya dawo kamar yanda doctor ya sanar masa har yay sanadin ajiyewar. Kwalin ya buɗe ya ciro, sai dai a mamakinsa babu komai a ciki sai kwafsan ashe ya shanyesa ma a wancan lokacin, bashi da zaɓin daya wuce sakin kwalin a wajen ya kai kwance yana jan bargo jikinsa dan rawar sanyinsa ƙaruwa yake yi, ga wani irin sarawa da kansa kemasa. Da gaske abubuwa sun masa matuƙar yawa, har ma yakan rasa wane irin tunani zaiyi. Ammien sa da sharaɗinta? Ko Iffah da abubuwan ban tsoronta? Ko Uncle’s na sa da son zuciyarsu? Ko matsalolin talakawarsa da dogaransu kan jiran adalcinsa a koda yaushe? Ko…. Ko…. Ko…. Ɗin sun masa yawa, yawan da matsalar dake tattare da shi a yanzu kamar tana son nuna fin ƙarfinsu. Dan ya jima da fahimtar kansa, amma ya zama mayaƙi na gaske akan kansa da kare mutuncinsa da ga taɓa ƴar kowa. Babban fatansa a koda yaushe ALLAH ya bashi ikon riƙe kansa har zuwa ga halalinsa da zai iya bama sirrinsa, sirrin da yake fata bayan matar aurensa kar wani mahaluki ya taɓa koda kwatanta sani insha ALLAH. yana ganin ko yaƙi ko yaso lokacin yayi, sai dai lokacin yazo da wasu abubuwa masu nauyin gaske. nauyin da ya rasa ma ina ya kamata ya fara kamawa……
A ɓangaren Iffah data sulale ta gudu tun bayan shigarsa bayi duk yanda tayi domin ganin ƙamshinsa ya bar jikinta hakan ya gagara. Tayi wanka, ta shafa nau’in turarruka daban-daban sai dai ƙamshin jikinsan na nan daram a cikin hancinta da yaƙi bata damar jin kowane ƙamshi bayan shi. Kamar wadda aka zarema lakar jiki tai sakwat a jikin bango tana lumshe idanu. Ita kanta bata san ainahin mima take ji a kansa ba, abinda kawai ta sani komai kawai ya ƙwace mata, bata da wani ƙarfi a zuciya da jikinta a halin yanzun, abinda ya farun kuma yay mata tsaiwar sojan badakare a ƙahon zuciya babu alamar zai motsa. Hanunnta ta kai ta shafi lips ɗinta, sai kuma tai saurin janye yatsun biyu tana mai girgiza kanta kamar wadda akema magana a kunne.