Daudar Gora Book 2 Page 66
Shiru kamar bazai tanka ba, sai kuma ya ɗago kamar wani mai ciwon wuya ya sauke idanun nasa masu haske da kaifi a kanta. Ƙasa tai da nata fuskarta har yanzu a ɗan shagwaɓe, bata sake gigin ɗagowa ba sum-sum taje kujerar gabansa ta zauna tai gefe da fuska. Ɗauke idanunsa kawai yay da ga kanta ya cigaba da abinda yake yi, sai da ya sake kwashe wasu cikakkun mintuna huɗun sannan ya ɗago a hankali yana ɗan firzar da iska. Ɗahowar tasa sai tai dai-dai da fara ring na landline ɗin gefensa. Ganin yay kamar baiji wayar ba ta ɗago ta kallesa, bashi da niyyar ɗaga wayar har ta tsinke, sai da a kira na biyu ya kai hannu ya ɗauka. Bayansa ya kwantar a jikin kujerar da kai wayar kunnensa yana lumshe ido. Maimakon amintaccensa da yay tunanin ji sai yaji muryar Malikat Bushirat tana sanar masa gata a falonsa.. kansa ya jinjina tamkar yana a gabanta, sai kuma ya buɗe baki da ƙyar yace, “To”. Daga haka ya miƙe yana kallon Iffah da ke binsa da kallo. “Muje” ya faɗa a taƙaice nan ma. Bata da zaɓin da ya wuce bin umarninsa, bakuma tada hurumin tambayar ina zasuje ko miya faru. Ta ɗaga kafa kawai a bazata taji lallausan hannunsa cikin nata, da sauri ta ɗago ta dubesa, sai dai shi sam bama ita ɗin ya ke kallo ba.
Suna kusantar falon bugun zuciyarta na ƙara hauhawa. Da masifar sauri taja wani irin bahagon burki lokacin da suke ƙarasowa tsakkiyar falon tai ido biyu da Malikat Bushirat da ke zaune hakimce fuskar nan tata babu alamar ta taɓa sanin minene ma murmushi a duniya. Hannun nata ta zare a cikin nasa ta fara ja da baya-baya, cak ya tsaya a wajen tamkar wanda aka dasa, sai kuma ya basar batare da ya ko waiwaya ba ya cigaba da tafiyar nan tasa ta ƙasaita.
Da sauri Malikat Bushirat da sam bata lura da Iffah ba ta miƙe, kafin ya ƙarasa isowa inda take ita ta miƙe zuwa garesa ta wani rungumesa. Idanunsa ya lumshe a hankali da sakin sassanyar ajiyar zuciya, dan abune da ya jima yana buƙata amma bai samu ba. Kusan sakan ashirin tana rungume da shi kafin ta ɗagoshi tana share hawaye, kallonsa ta ke cike da son tabbatar da babu abinda ya taɓa mata shi, dan duk duniya babu abinda take so da ƙauna sama da shi. Tana masa wani irin makahon so da ya zarta hankalin duk wani mai tunani…
“Ammie”.
Ya faɗa a hankali yana riƙo hanunta cikin nashi. Ɗayan kuma ya kaisa kan ƙyaƙyƙyawar fuskarta ya share mata hawaye hankalinsa duk a tashe, dan ganin hawaye a fuskar Ammien sa abune da bazai kasance ƙarami ba. Ya santa ya san mahaifiyarsa jaruma ce da ko’a cikin dubu zai faɗa babu wani ɗar.
Sake rungumesa tai tana magana cikin ɗacin murya. “Wlhy da yau wani abu ya sameka kamar wancan karon babu abinda zai hanani ɗaukar mataki akan koma wanene, dan bazan yafe musu ba, na baya ma ba yafe musu nai ba Eshaan” sai kuma ta sake ɗagosa da sauri, takarda da biron data ajiye a kujerar data zauna ta ɗauka, ta kamo hanunsa shi dai yana binta da kallo, a cikin tafin hannun ta saka masa, babu alamar wasa ko sassauci akan fuskarta ta furta, “A matsayina na UWA mahaifiya a gareka bin Haysam Abdul-majeed, ina baka umarnin ka saki yarinyar nan, ka kuma janye duk wata garkuwar da kai mata…”