Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 65

Sponsored links

Taku take a hankali kamar mai sanɗa ko wata budurwar hawainiya, babu abinda zuciyarta keyi sai dukan tamanin-tamanin. Idan yace ta biyasa kudinsa itako batama san yaya zatayi ba. Da ƙyar ta gano room two ɗin duk da bedrooms ɗin biyar ne kawai take tunani a wajen. Sauran ƙofofin bazata iya tabbatar dana minene ba tunda ba kowacce karambaninta ya taɓa kaita taɓawa ba bayan ta Gym a ɗazun. Taja wasu mintuna uku masu ƙyau a ƙofar kafin tai ƙundun balar ɗaura hanunnta a handle ɗin ta murɗa. Da sallama ciki-ciki ta shigo ɗakin da babu wani haske sosai, sai wani uban ƙamshi mai ratsa kwanya da uban sanyin ac kamar ba sanyi ake a garin ba. Hannunta na dama ta ɗan kai kan kafaɗarta ta haggu tana shafawa alamar sanyin ya ratsata. Can ta hangosa cikin ƙyaƙyƙyawar kujerar da ke gefe guda biyu, yana sanye cikin kayan barci farare tas da sukai masa ƙyau sosai, yanda hannun rigar ya kamashi sai ya fiddo murɗaɗɗen damtsensa da a kallo ɗaya zaka san yana samun isasshen motsa jiki. Lap-top ce a gabansa yana sarrafawa cike da ƙwarewa, sai butar shayi mai ƙyau da ƙaramin kofin da ke tabbatar da sha yake yi. Duk da motsin buɗe ƙofar tata da uban ƙamshin turarensa data bulbula ya zo hancinsa bai ko motsa ba balle ya nuna alamar yasan da zuwanta, aikinsa yake hankali kwance.

 

Idanunta data zuba masa ta janye, a karo na farko ta fara jin tana son sanin wai mi yake yi a laptop da a koda yaushe zaka gansa yana sarrafawa. Ko waya takan daɗe bata ganta a hannunsa ba. Amma computer in har yana zaune to baka rabashi da ita. Ganin har tazo gaf da inda yake bai nuna alamar yaji shigowarta ba tai tunanin ko bai jitan bane. Sallamar ta sake maimaitawa ƙasa-ƙasa. Idanu ya ɗan lumshe kaɗan ya sake buɗewa saboda yanda sassanyar muryarta ta wani ratsashi. Da ƙyar ya iya danne abinda ke taso masa ya buɗe idanun akan lap-top ɗin ya cigaba da aikinsa batare da ya motsa ɗin ba dai. Haushi ne ya kama Iffah a karo na farko, ta san dai in har baiji sallamar farko ba babu yanda za’ai ace baiji ta yanzu ba. Idanunta ta juya kamar zata ɓalla masa harara dan takaici, amma bazata iya ba, sai kuma tai tunanin koma ta juya ta koma, nan ma tasan ko giyar kokino ta sha bazata iya hakan ba dai. Tsaiwar ta cigaba da yi batare data sake motsawa ba itama, sai bin ɗakin dai take da kallo. Duka bedroom ɗin data taɓa shiga a sashen nasa tasan sun haɗu matuƙa, sai dai fa wannan ɗin na musamman ne gaskiya. Dan kamar ma duk yafi waɗancan girma. Ƙatone na gaske, bayan katafaren gadon da zai iya cinye mutane goma tsaf akwai wadrobe na glass kamar yanda gadon ma take ganin kamar glass ɗinne. Hakama mirror da duk sauran tarkacen furnitures ɗin sun haɗu. Sai wasu rukunin haɗaɗɗun kujeru suma pitch and gold ɗin kamar yanda gadon yake… Kai ita fa idan tace ma zata cigaba da lissafi sai ta gaji, kawai dai ɗakin ya haɗu, komai na cikinsa pitch and golden ne da suka dace da kansu….

“Kin koma soja ne?”.

Nutsatstsiyar muryarsa mai cike da kamewa da ƙasaita ta ratsa kunnuwanta a bazata. Kallonsa tai tana tunzura baki na haushi, yana a yanda yake tunda ta shigo, ɗan latsin ashe yasan da shigowar tata. A zahiri kam cikin muryar shagwaɓa-shagwaɓa haushi-haushi ta ce, “To ai ba’a bani wajen zaman ba”.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button