Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 44

Sponsored links

Tabbas sun gama yarda cewar Tajwar Eshaan tsohon makirin kansa ne. Sannan hatsabibancin da suke jifansa da shi fa sun tabbatar da shi ɗin a tattare da shi yau. Rai ɓace kusan kowa ya fita a falon bayan fitarsa, kowa bakinsa fal da magana sai dai babu damar yinta anan kuma gudun abinda zaije ya dawo…

Sam Iffah bata san wainar da ake toyawa ba, dan tun fita sallar la’asar da yay a ɗakin bayan ya tsareta ta ɗanci abincin da aka kawo bata sake ganinsa ba. Sai ma wani wahalallen zazzaɓi ne ya rufeta ruf. Da ƙyar ta iya tashi sallar magrib. Tayi ta a daddafe ta sake komawa saman gadon ta kwanta dan rawar sanyi jikinta ke mata. Bata iya tashi sallar isha’i ba tana cikin bargo. Sosai jikin nata ya ɗauka matsanancin zafi ga ciwon kai ga sanyi tana ji. Tun bata damu da ƙin shigowar tasa ba har ta fara addu’ar hakan, a haka wani wahalallen barci ya ɗauketa…

Har ya kammala shirin barcinsa zai kwanta zuciyarsa taƙi bashi haɗin kan hakan. Fuska ya ɗan yamutse kai kace bashi da ra’ayin abinda zuciyar tasa ke so. Sai dai a kallo ɗaya zaka fahimci tsabar miskilanci ke cinsa da ƙasaitar mulki. Cike da izzar dake bayyana takunsa a matsayinsa ya nufi ɗakin.

A hankali ya tura ƙofan ya shiga bakinsa da sallama ƙasa-ƙasa. Kallon mamaki yake mata ganinta naɗe a cikin bargo, ga alamar ɗan rawa-rawa da jikinta ke mata da yake gani. Hannu ya kai ya ɗan janye bargon daga saman fuskarta. Aiko ta wani zabura, caraf ta damƙe hannunsa idanunta rufe ruf da alamar tana cikin mayen barcin dai bakinta na motsi cikin faɗa-faɗa take faɗin abinda baya ji.

(Fitinatu har a cikin barcin ma ba’a kadata) ya faɗa a zuciyarsa yana lumshe ido da riƙota ganin da gaske fa faɗan take ga zafin hanunta dake kan nasa na ratsa fatar shi. Jikinta rawa yake sosai, dan mafarkin da tai ya matuƙar firgitata, ta daɗe batai irin mafarkan nan ba. Da farko mamakin yanda take ɗinne ya shiga, sai dai ganin abinfa na gaske ne sai hankalinsa ya tashi. Amma bazaka taɓa tantancewa ba a face ɗin sa. Kaɗan ya girgizata muryarsa a ƙasan maƙoshi ya furta “K!”.

Ina batama san yanai ba, sai ƙoƙarin fisge jikinta da take kamar dai yanayin da takan shiga a duk lokacin da tai irin mafarkan. Jikinsa ya jawota sosai yana ɗan bubbuga fuskarta kaɗan-kaɗan, sai kuma ya sake faɗin, “Open your eyes. Iffah k!”.

 

Karan farko daya taɓa ambatar sunanta, duk da bata a hayyacinta sai da taji fitar sautin sunan. Buɗe idanun tai a hankali jikinta na ɗan tsuma ta sauke a kansa, sai kuma taja nannauyan numfashi tana ɗan ƙara warosu domin tabbatar da shi ɗinne a zahiri ko har yanzu a mafarkin ne dai. A hankali ya mannata da ƙirjinsa ya rungume. Wani ajiyar zuciya ta sake ja mai ƴar shashshekar data saka tsigar jikinsa tashi. Sai kuma ta maida idanunta ta lumshe sannu a hankali ganin yanda ya tsareta da kaifafan nasa idanun. Lafewa tai a jikin nasa kamar wata mage, dan kanta ciwo yake matuƙa. Ba ƙaramin dauriya yay ba na zamanta jikinsa har tsahon mintuna uku, cikin son danne yanayin da ke neman halaka shi ya buɗe idanunsa da suka canja kala akan ƙyaƙyƙyawar fuskarta. Wani irin kallo yake binta da shi tun daga fuskarta har zuwa ƙafafunta, gaba ɗayanta naɗe take a jikinsa. Yanda ta naɗe ɗin ya bama abayarta mai sanyi damar lafewa a jikin nata ya fidda mata suranta da ƙyau. A kasalance ya lumshe idanunsa yana kauda kansa jin numfashinsa na wata rawa-rawa. Ga ɗumin jikinta na matuƙar ratsa nasa jikin.

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button