Daudar Gora Book 2 Page 36
Kalaman wasiyyar mahaifinsa ne suka shiga dawo masa ɗaya bayan ɗaya. A yanzu kam idanun ya rumtse tare da kaiwa zaune cikin kujera. Zuciyarsa na gudu da sauri-sauri. Sosai yake jin ɗaci mai sosa zuciya. Hawayene suka cika masa ido domin shima mutum ne kamar kowa, zuciyarsa irin ta kowa ce, yanajin zafi, yanajin farin ciki. Sosai yake buƙatar son jinsa a jikin wani. Mahaifiya ko mata. Sai dai yasan hakan shine abu mafi wahala a gareshi bayan abubuwa masu yawa da ALLAH ya azurtashi da su. Yanada tarin dukiya daya nema da guminsa, mahaifinsa ya bar masa tarin dukiya da shi kansa bai san iyakarta ba. ALLAH ya bashi mulki, mulki mafi daraja sama da kowane shugaba da ke a ƙasar ruman. Ya azurtashi da ƙyawu irin wanda ko’a cikin ƙyawawa yasan zai zama abin kallo. Ya azurtashi da ilimi na boko dana addini da babu abinda zaice sai Alhamdullah. Sai dai ya tawaya ta ɓangaren mace, shi mutum ne mabuƙaci, ya daɗe da fahimtar hakan, amma ƙaddarorimsa sun nisanta shi da samun cikamakin waɗan nan ni’imomin da UBANGIJI ya mallaka masa. A hankali ya sauke lumsassun idanunsa kan Iffah zuciyarsa na kaikawo. (Abbie miyasa kace na kasance haka?) Ya ambata a zuciya cike da ƙunar da take masa mai raɗaɗi..
Jigum-jigum aka yini a masarautar cike da jimamin abinda ya faru. Al’amarin ya fara ɗaure zuciyar kowa a yanayin da yake da wahalar fassara. Sai dai a zahiri babu mai iya cewa komai sai ƴar ƙus-ƙus kai da abokin maganarka. Har yamma Tajwar Eshaan na tare da Iffah, duk da damunsa da na’urar ɗumama ɗakin da aka kunna saboda ita keyi haka ya cigaba da zama a ɗakin. Hatta da fada da akai zaman fadanci da tunanin zai fito yace wani abu akan abinda ya faru bai fitan ba. Sallama a ɗakin yayi ta yau. Hakan ya fara ankarar da mutanen masarautar kenan duk lokacin daya killace kansa yaƙi fita yana fushi ne ko cikin damuwa. Dan yau dai kusan kowa a haka ya fassara rashin fitowar tasa.
Su dai ke kiɗansu suna rawarsu, dan shi dai bai ce ba babu kuma alamar zai ce ɗin har yammaci. A hankali ta fara motsi dai-dai lokacin da yake zaune yana raira karatun Alkur’ani mai girma da wata irin sassanyar murya mai tsaushi da ratsa zuciyar mai saurare. A duk lokacin da ya samu kansa a irin wannan yanayi na damuwa mai ƙuna yafi buƙatar zama yayta karatun Alkur’ani sai ya samu nutsuwa. Da atshawa ta fara a jere har guda huɗu, hakan ya ankarar da shi farkawar tata. Amma tsabar ƙasaita da miskilanci baiko motsa ba ya cigaba da karatunsa har inda yaji zai tsaya dan kansa. Koda ya ajiye Alkur’anin ma bai juyo ɗin ba kai tsaye duk da atishawar da ta cigaba da jerawa a wahalce kuma a jajjere. A nutse ya miƙe babu alamar gaggawa ko garaje tattare da shi, sannu-sannu ya sauke manyan ƙyawawan fararen idanunsa kanta dai-dai ta sake yago tissue dake gefenta a bed side drawer ta toshe bakinta domin tare atshawan da ya sake taho mata. Kusan uku ta sake jerawa kafin ta ajiye tissue ɗin inda ta tara sauran cikin ƙanƙanin lokaci. Numfashi take saukewa a ɗan wahale kumburarrun idanunta na lumshewa da buɗewa…….
A haka idanun nata suka kai garesa, zuba masa su tai a yanayin kallo na ƙasan ido, har ranta take jin bugun zuciyarta na harbawa da sauri-sauri. Ba yau ta fara ganinsa cikin ƙananan kaya ba idan yana sashensa a keɓe, amma sai taga yau ɗin kamar special ne. Baƙaƙen kayan sun masa ƙyau matuƙa da sake bayyana haskensa da ƙuruciyarsa kamar wani matashin saurayin da bai taɓa mallakar ko budurwa ba.