Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 34

Sponsored links

Shiko da bai ma san sunayi ba da harshensa yay nasarar raba lips ɗinta da haƙoranta dage datse cikin na juna ya turashi cikin bakin nata, sai kuma ya kai yatsunsa biyu kan hancinta ya matse. Iskar bakinsa mai ƙarfi ya hura mata cike da salon ƙwarewarsa akan iya ruwa da ceton duk wanda ya samu accident a dalilinsa. Da wani irin ƙarfi ta zaburo ƙirjinta na ballaƙowa sai ruwan bakinta bulla a kan fuskarsa. Idanu ya lumshe a hankali yana mai sauke wata irin nannauyar ajiyar zuciya daga cikin maƙoshinsa da ɗan jan fuskarsa data wanke da ruwan bakinta.

Cikin sauri Ama. Ta miƙama Sayeed ƙaramin towel cikin wanda ke hanunta, amsa yay ya matsa kusa da Tajwar Eshaan kansa a rissine ya miƙa masa. Bai motsa ba idonsa a kanta tana cigaba da amayo ruwan saboda ɗan danna ƙirjinta da ya cigaba dayi har tsawon kusan mintuna biyu, kafin ya miƙama sayeed hannu batare da ya juyi ba ya amsa. Kan fuskarsa ya kai ya tsane ruwan da tuni yama gangagare har wuyansa har ya ɗan jiƙa jallabiyar jikinsa mai tsananin ƙyau da ɗaukar idanun kai kallo.

“Duvet”.

Ya faɗa a hankali ganin jikinta ya fara karkarwa har ɗan gadon agajin gaggawar da aka daurata na ɗan jijigawa. A cikin ƙanƙanin lokaci aka kawo, yanzu ma da kansa ya rufa mata. Sannan ya miƙe gaba ɗayansa yana ɗan duban Sayeed. “A maidata gareni”. Ya faɗa can ƙasan maƙoshi tamkar bashine yay maganar ba yana ƙoƙarin barin wajen. Sai yanzu ya lura da cikar garden ɗin da duk masu faɗa ajin masarautar a wajen. Idonsa ne ya sauka kan Malikat Bushirat da Malikat Haseenat da ke kusan tare da juna. Dan Daneen Ammarah da Malikat Ashwaq ne suka ɗan shiga tsakaninsu. Ɗauke idanun nasa yay ya cigaba da takunsa na bajimta. Dan kowa a wajen kansa a rissine yake har su Malikat Bushirat ɗin kansu domin tabbatar da girman da ALLAH ya bashi na shugabanci….

A gaban idon kowa aka wuce da Iffah sashen Tajwar Eshaan ɗin tare da Doctor da zata sake bata taimakon gaggawa, a hankali ƙus-ƙus ya fara tashi a wajen kowa na jimanta al’amarin da jinjina faruwarsa kasancewar duk wanda ya kwana ya tashi a gidan yasan Iffah na kurkuku ne, kuma a yau za’ai zaman shari’a ta biyu, hakama abinda ta faɗa a zaman waccan shari’ar kowa ya jisa. Sai dalilin faruwar al’amarin yau ya saka zukata fara rarrabuwa a kan al’amarin ta, masu ganin a wancan zaman shari’ar ta faɗi waɗan can kalamanne danta kuɓutar da kanta ko sharri, sai a yanzu suke ganinfa akwai ƙamshin gaskiya tunda a karo na biyu kenan ana yunƙurin kasheta. Idan babu rami to miya kawo rami? Wannan shine tambayarsu.

Samun gawar ɗaya daga cikin jami’an dake tsare da Iffah, da ɗaya daga cikin na sashen Tajwar Eshaan ya sake tabbatar da akwai ƙullalliya. Dan alamomi na bayyane sun nuna an fara kashe jam’in sashen Tajwar Eshaan ɗin ne akai amfani da kayansa zuwa kurkuku, sai kuma gawar jami’in dake cikin masu tsaron Iffah da bayanin sauran jami’an ya tabbatar da koma miye a lokacin da yace zaije ya binciko gaskiyar zuwan jami’in da yace yazo kawoma Zawjata-almilk kaya ne. Sarƙa-sarƙar ta ɗaure kan mutane matuƙa da yanda tama faru, sai dai jami’an sun tabbatar da sai sun gano koma wanene anan kusa cike kuma da alwashi…..

Tunda akace ta farfaɗo hankalin duk masu hannu akan al’amarin ke’a tashe musamman ta-ƙurya da hadimin da yay aikin. Tashin hankalin ta-ƙurya rashin mutuwar Iffah ne, dan tanada hanyoyin da zatabi na ɓatar da hadimin cikin sauƙi, kai koda ta barsa da rayuwarsa ma bai san ita wacece ba. Amma kasancewar cigaba da rayuwar Iffah na nufin MATSALARTA na nan har yau da gobe dama ranar da bata san iyaka ba. Idan har tace kuma zata sake wani yinƙuri a yanzu akwai matsala, mafitarta ɗaya ce sake komawa ga UWA ɗin da take hangen ta gaza a baya. Wasu irin zafafan hawaye ne masu raɗaɗi suka shiga bin kumatunta, ɗuminsu kawai taji batare da tasan ta farasu ba. Hakan ya ƙara ƙona ranta dan akan ƴar yarinyar data raina hawayenta na zuba a karo na babu adadi, abinda bai taɓa faruwa da ita ba kasancewarta mai nasara ga duk abinda ta sanya gaba. Shawarar da zuciyarta ta bata akan sake kiranyen uwa ya sata miƙewa. Surkullen jiya ta shiga fara maimaitawa. Tsahon lokaci har ta fidda rai a yanzu ma sautin mummunar dariyar uwa ta fara karaɗe ɗakin. Dariya ta tsaho lokaci babu alamar za’a daina kafin uwa ta bayyana a gabanta. “Ashe k! ƙaramar mara kunyace ta-ƙurya. Ashe baki shirya yaƙin ba kika yanki filin yinsa ba! Ashe b……”

“Tuba nake Uwa mai share kukan masu kuka. Nayi kuskure a gafarceni bazan sake ba. Ni mai biyayyace ga umarninki a koda yaushe. Wannan ma saɓanin fahimta aka samu”.

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button