Daudar Gora Book 2 Page 160
Karan farko Tajwar Eshaan ya saki wani dan murmushi mai ban mamaki, ji yake wata irin kimar Ummu da darajarta ta karu a ransa. Murmushinsa ya matukar birgesu, ya kuma sake sanyasu a farin ciki, sai dai kuma bai sake cewa komai ba…..
Daga kotu da kyar ta iya fitowa zuwa mota, suna isa sashenta dakinta ta shige ta kulle kanta. Jiri take ji da wani irin mahaukacin ciwon kai ga bugun zuciyarta kara hauhawa yake. Shin mike shirin faruwa da ita ne haka, mike tunkaro rayuwarta. Danta Eshaan, Eshaan dai data sha wahala kafin samunsa ne yake auren yar Daneen Ammarah. Mai tambarin tawadar ALLAH a jiki, yarinyar da ke cikin lissafin ayyukansu. Mai tambari dai irin wanda Uwa ta shardanta mata a cikin sharudanta. Mike faruwa haka? Ta yaya hakan zai kasance? _(Ina tayaki murna da albishir din insha ALLAHU kafin mu dawo daga hutun in amarcinmu da iznin UBANGIJI zamu dawo da jikanki a wannan babbar garkuwar, dan haka kibar wahal da kanki akan sai Maleek ya auro wadda kike son ta haifa miki shi dole ko nisanta shakuwar iyayensa da zata zama sanadin samar da shi ta hanyar madara. Da ga kuma randa kika tabbatar da samuwarsa, ki fara irga kwanakin nadamarki da dana sani har zuwa ranar haihuwarsa. Hukunci da karfin ikon Iffah a saman naki, yanzun ne zai fara Mother in-law)_ kalaman Iffah suka shiga mata kaikawo da amsa kuwwa a cikin kunne kamar yanzu ne take fada mata su. _(Ammie na yarda ke Zakanya ce, sai dai ki sani duk karfin bajintarki da iya farauta a saman kowa watarana tsufa kan ¡ya sa ki rissina jikar bayanki ta zama sarauniya bisa karfin ikon naki, Ni bance nafi karfin kaddara ba, sai dai ki sani a tafin hannunna kike ke da komanki….)_. Kuka ta fashe da shi, cikin karaji ta furta “Bazai yiwu ba, bazan dauki faduwaba, wihy Uwa bazan dauka ba sai dai duk mu fadi tare, sai dai ai mutuwar kasko mu dukanmu baki daya” wani irin kuka ya sarketa, wasu kalaman Iffar ne suka sake shiga dawo mata…. _(Ammie wihy inada abubuwan ban mamaki da daga labulen sirrinki sau daya kawai sai ya hana wannan idanun naki barci…..)_ wani irin naushi ta kaina mirror din akin da sake kwala kiran sunan uwa_(…..……To wai nikam wane buri ne kike son cimmawa mai alaka da makiyi a tsakaninki da shi? Kin ko san da ace yasha ganyen shayin nan ko madarar nan illar da zatama rayuwarsa sai tafi wadda zatama tawa rayuwar? Sannan ke da kanki sai kin dawo kina kuka da dana sani. Idan ma wani ke baki wadan nan abubuwan matsayin wani kariya washi ko gurbata tawa rayuwar to tabbas ki farka. Ki farka why tunkan guri ya kure miki ki rasa kofofin fita a wannan masarautar.…)_ “Har abada! Har abadan abada bazan taba faduwa kasa ba, bazan rasa komai ba a lokacin da komai ya zama nawa ba….
“Dole ki rasa! Dole kirasa!! Dole kirasa ta-kurya!!Hahahahaha!!!!”. Uwa ta fada cikin karaji da amsa kuwwar mummunar muryarta alokacin da take bayyana. A kallo daya zaka fahimci itama a birkice take. Dan idanun nata sun sake jajur, fuskarta ta sake muni matuka. Da wani irin karsashin wutar bala’i Malikat Bushirat ta fiskanceta, a yau babu wani tsoro ko shakku tare da ita balle girmamawar da ta saba ga uwar. Gabanta taje ta tsaya tana mai nuna ta da yatsa.
“Sai dai mu rasa gaba dayanmu, amma ba Malikat Bushirat kawai ba. Miyasa kika yaudareni?..
“Ke kika yaudari kanki, domin a yarjejeniyar mu akwai sharadin kin auren yarinyar data fito a wannan zuri’ar musamman mai tambarin na hakika”.
“Amma da umarninki ta zama matar Saiful-malik, shin bokancin naki ya fara raunine ko dama ke din mayaudariyace kamar yanda yarinyar ta fada?!!!”.