Daudar Gora Book 2 Page 16
Ki fahimci Mammah ba fifita Fareedah take sama da abinda ta cancanci fuskanta bane, kariya take bata matsayinta na tamkar makamin da zai iya zama zaren da zai jamu ga duk ɓoyayyun masu laifin da muke fatan kamawa a cikin hannayenmu. Shin baki ji a ranki wanda suke aikata ta’asar baya nada nasaba da na yanzu ba? Baki ji a ranki yanke mata hukunci a kallonta ita kaɗai mai laifin tamkar basu ƙwarin gwiwar cigaba da aikatawar bane koda kuwa a yanzu basu da hannu kan abinda yarinyar ta aikata? Shin baki tunawa shi shugaba ne ba mai azaba ba?. Da yawan mutane gani suke sakacinsa da ƙin bama abu muhimmanci koda mai muhimmancin ne halayyarsa, sai dai yanda yake yi shine cikar zama cikakken duk wani shugaba. Shugaba da shanyewa aka sansa koda ɗacin na ƙona makoshinsa, da haɗiyewa aka sansa koda raɗaɗin na azabtar da hanjinsa, da ɓoyewa aka sansa koda girman al’amarin yafi girman zuciyarsa, da nazarta aka sansa koda ƙarfin yafi ƙarfin ɗaukar ƙwaƙwalwarsa. Ba ko yaushe yake ihu ba, ba ko yaushe ake gane ainahinsa ba, ba ko yaushe ake iya karantar zuciyarsa ba koda a ƙwayoyin idanunsa ne…..” ta ɗan ja numfashi ta fesar a hankali da cigaba da faɗin, “Idan har mu a karan kammu zamu kasa fahimtar kammu taya wanɗanda ke zagaye da mu zasu fahimcemu?. Idan har uwa zata iya shanye wa da daurewa akan halayyar ƴaƴanta da duk girman adadinsu bazasu haura ashirin ba mai zaisa shugaba mai mulkin ƙasa baki ɗaya kamar ruman za’a so ganin zahirinsa a dole dan kawai farin cikin wani ɓangare ko munanama wani ɓangare? Tayi laifi an yanke mata hukunci, daga baya gaskiya ta bayyana bata da laifi ko tursasata akayi ko wani dalili da zai iya wanketa koda ace ba shine yay hukuncin ba, to shi ne za’a kalla da tabon gazawa? Wa za’a munana? Wa za’a aibanta? Wa za’a munanama kima da mutunci? Amasar itace shugaban nan dai Umm-Jasrah. Dan ALLAH na roƙeki ki kwantar da hankalinki kar wasu su dinga amfani da fusata fushinki domin cikar nasu burin, ki cigaba da zama a yanda na sanki inba hakaba wasu zasuyi amfani da hannayenki wajen shafama kanki da kanki fentin da babu wani ruwan da zai wankeki ya wanke wanda ake son amfani da soyayyarsa a zuciyarki. Bayan ke uwa ce, kema ɗin shugaba ce…..”
Har cikin rai da ɓargo zantukan Daneen Ammarah sun matuƙar ratsata, sai dai basu ruguje kaso ashirin cikin ɗari ɗin matsayin da take kallon Iffah da shi ba har a yanzun, amma taji ta kuma amince zama mai haƙurin bin matakin da ya dace ɗin wajen hukuntata, hakanne kawai zai bata salama kasancewar ta wadda bata ɗaukar ƙiyayya da sauƙi ga duk wanda ya nuna mata, hakama soyayya. (Hakan kuskure ne Malikat Bushirat, karka zafafa ƙiyayya, kar kuma ka zafafa soyayya dan wataran duk zasu iya canja kansu a gurbin juna), sai kuma ƙudirinta na biyu babu gudu babu ja da baya zata tabbatar da shi koda babu yardar kowa a daular ruman har shi kansa Tajwar Eshaan ɗin……