Daudar Gora Book 2 Page 150
Boka Barbushi ya tabbatar mana da lallai akwai matsala, sannan bayan mu akwai wasu masu kudirirrika sosai a cikin masarautar zagaye da rayuwar Eshaan. A yanzu hakama bayan wadan nan matan nasa biyu da suka rasu wasu zasu sake. mutuwa da shima bai san adadi ba. Sai dai akwai gabar da abubuwa zasu canja kansu dalilin auro wata yarinya da bata cika ashirin ba. Wannan yarinya akwai al’amari mai girman gaske tare da ita, sannan tana tare da manyan sirrika, a cikinsu ma harda babba daya kasance sirrin wanna masarauta. Idan kuma har ta shigo gidan burinmu bazai taba cika ba na mulkar kasar ruman. Mun tashi hankalinmu amma sai ya dakatar da mu da cewar mu kwantar da hankalinmu, munada hanya daya ta bullewa. Hanyar itace bibiyar duk matan da Eshaan zai aura, zamu gano wanna yarinya ne kawai ta hanyar auren yara biyu da ga gidansu itace cikon ta uku, biyun zasu mutu bayan suma sun shigo masarautar. Sai muyi kokarin shafe ahalin wanna yarinya gaba daya ita kuma muyi amfani da ita ta karasa halaka mana Eshaan shike nan zata kare rayuwarta a kurkuku koma a tsireta Jasim ya hau karagar mulki ni kuma na zama magajinsa batare da wancan sirrin ya bude ba. Komai ya mana, sai dai mu burinmu sanin wanene zai dinga kashe matan nasa? Ya sanar mana shima bai iya gano su wanene ba gaskiya. Amma sunada hadari sosai, kuma a cikin gidan nan suke suma, bai kuma kamata mu damu da abinda zasu aikata ba dan zasu mana aikinmu ne cikin sauki muma, Eshaan bazai samu soyayyar mutane ba a dalilin wanna kashe-kashen, dan kowa zai kallesa a mai kashe matansa.
Shi kuma zai maida hankalinsa ne a neman wanda ke kashe masa mata mu kuma muna aikinmu a kansa cikin sauki, Mun gamsu mun kuma dawo gida cikin farin ciki. Tun daga nan abubuwa suka cigaba da gudana, muma muka dage, bama sanya waien kokarin shiga da fita da gain an aurama Eshaan mace bayan mutuwar wasu. Ga kuma abinda duk boka Barbushi ya fada yanata faruwa daki-daki, tako ina zaginsa ake da la’antar mulkinsa har mutane na kiransa da Fir’auna. Hakan a mana dad, shiyyasa ma muka baza yaranmu tako ina suna gano mana kyawawan matan da za’a aurama masa, da munzo muka kalame Mammah da zance musamman ni sai ta amine da fatan ALLAH yasa karshen al’amarin kenan. A haka har lissafinmu ya kai ga wasu yara da mahaifinsu ke kawo zuma masarautar nan. Wani kuma yaronmu dake mana aikine ya kawo mana zindensu ashe abokinsa ne. Mun tabbatar da auren ta farko kamar yanda aka saba itama ta mutu, kasancewar munga biyu bayanta muka sake shigewa gaba aka auro ta biyu. Itama dai ta rasun, dan haka muka dira akan ta uku. Shekarun yarinyar da wanda Barbushi ya fada ne ya samu farin cikin da fahimtar itace wadda muke nema, dan haka bayan an aurota muka fara shirya yanda zamu tarwatsa ahalinta. A wanna ranarce wanda yay mana hanyar sanin gidan yaji hirarmu (abokin nasa kenan), bamu nuna masa mun sani ba, sai muka bibiyi rayuwarsa ta hanyar matarsa. Kudi muka bata mai uban yawa da firgita mata rayuwa, harma Jasim yay amtan da ita sannan muka bata gubar data bama mijin nata sannan muka wuce.
Washe gari bamu san miya faru ba ta kiramu a rikice wai mijinta ya tafi sanarma iyayen yarinyar nan komal amma ta bashi gubar da muka bata. Hankalinmu ya tashi, babu sanya muka samar da yan sanda suka je gareta da ga nan tai musu jagora zuwan gidan. Anan ne muka saka aka kama mai gidan da babban dansa. (Nasan dal baku manta kama babiy da Hanash ba?)”.
Arshaan yaja numfashi ya fesar cikin kunar zuciya, sai kuma ya cigaba da fadin, “Makwafcinsa da wani tsoho da akace mahaifin matarsa ne sun cigaba da fadi tashin gain sun san inda suke, sai dai hakan ya gagaresu, a da burinmu kawai mu kashesu a lokaci daya, sai dai yanda Barrister Abdallah Aas ya shiga zance sai mukai sha’awar cigaba da buga wasan. Dan haka muka cigaba da wasa da hankalinsu, mun shirya kawo karshen rayuwarsu a gabar da muka gama shirya kawo karshen rayuwar Eshaan. Sai dai su bamu maida hankali kansu ba sosai dan a ranar muka damka madara mai duke da gubar dafin macizai ga yarsu, dan haka tunaninmu ya karkata kan yarsu gaba daya da kuma aikin da muka sakata. Da ga baya aka sanar mana suma an kashe mana su.