Daudar Gora Book 2 Page 136
A gefe kuwa wata Irin shakuwace ta shiga. tsakaninta da uwargidan Sultan. Mace hamshakiya ma’abociyar kyawawan halaye da nuna tsattattacen iko saman na kasa da ita. Nutsuwa sosai Iffah tai tana koyan abubuwa, yayinda itama bata tsaya boye-boye ba ta fito tana gyarama Iffah’r duk abinda zai bata martaba da kima a wajen mijinta da al’ummar da mijin nata ke shugabanta. Dan tayi dubi ne da karancin shekarun Iffah’r da ma labarin data bata na cewar ita iyayenta basu da alakan mulki. Ba halayyar Iffah da dabi’u ba hatta jikinta wani irin gyara yake samu na musamman ga uwargidan Sultan din.
Hadimanta kam tunda sukazo bata gamsu sun ganta sau cikakken biyar ba. Hakama duk dokinta da tsammanin zal hadata da su Babiy tunkan su taho babu alamar zai yi hakan. Har magana ta masa cikin hikima amma sai baice mata komai akan hakan ba. Dole ta hadiye komai ta nuts bisa shawarar uwargidan Sultan din.
Shanyewar tai kuwa, dan yanzu Iffah an koyi halin dattako da shanye abu a ral, sai dal fa à gaban Tajwar Eshaan bakin baya mutuwa, idan kin jita shiru barci take, a lokacine kawal zai huta da tsiwarta.
Alhamdulillah yau an kai azumi na ashirin da shida, a yau ne kuma su Iffah sukayi ziyarar bankwana cikin dakin ka’aba ita da Tajwar Eshaan da Sultan na saudiya, da uwargidansa, sai wasu manyan masarautar tasu. Iffah tasha kuka lokacin da taganta cikin tsakkiyar dakin ka’aba, Abune da bata taba zaion kasancewarga ba koda a cikin matarkinta. Kal ita ketare kasar ruman ma bata taba zaton tana da rabon yi ba a rayuwarta. Amma yau sai gata da kwanaki ashirin da biyar cikin kasar Saudiyya, tare da mijin aurenta shugaban kasarta. Hannunta kawai ya rife cikin nasa alamar lallashi har suka fito, suna shige mota kuwa ta fada jikinsa ta kankamesa. Murmushi yay mai sanyi da dagota yana mata yan harara tare da lakace mata hanci. “So kike ki karyamun azumi ne?”
Baki ta dan tura tana wan kikkitata Idanun dake cike da hawaye, a shagwabe tana war idanun da yanayin mamaki ta ce, “Dama maza azuminsu a karyewa ne?”. Murmushi kawal yay ya dauke kansa, sai kuma ya sake juyowa a yanayin wanda ya tuna wani abu, kallonta yay da ga sama har kasa kafin ya jeho mata tambayar data daure kanta da bata yar kunya-kunya. “Mrs Eshaan kin sha wani magani ne dan kar kisha azumi?”. Da kunya-kunya mamaki-mamaki ta dubesa, sai kuma ta girgiza kanta alamar a’a. Itama kuma sai kirjinta ya shiga harbawa da sauri-sauri. To al bama watan azumi kawal ba, idan bata manta ba rabonta da ganin proud din ta fa kamar tun wanda ta gama da kwanaki kadan ya ziyarceta bafa ta sake ba. Kai kodai ta sake ta manta, to idan ma ta sake din ai a watan nan ne na Ramadan ya kamata ta gani farkonsa, juya mata kanta ya fara yi saboda neman takurama kanta da tai na sai ta tunano. “Kinga relax karki takurama kanki”., Ya fada a hankali yana kwantar da ita a kujerar.Gaba daya jiyay yama kagara su koma cikin masarauta, suna isa kuwa masaukinsu aka zarce da su. Duk da an bude mata kamar yanda aka bude masa kofa shima sal ya fito da ita ta inda ya fita, basu fi zaman mintuna goma ba doctor din da ya bukaci gani ya iso tare da uwargidan Sultan da hankalinta ya tashi da tunanin ko kukan da Iffah tayi ne ya zame mata matsala,