Daudar Gora Book 2 Page 139
Duk da saukar dare sukai tako ina a airport din zagaye yake da matakan tsaro. Kai da gani kasan mai kasar ruman dinne da kansa zai sauka. Ta bangaren masu tarbarsu kuwa manyan masarautar ne masu fada aji. Ga wasu lafiyayyun motoci ababen birgewa ga mai kallo. Sosa barcine a idon Iffah dan yanzu kam bata da aikin da yafi wannan. Hakan yasa ta kasance a kusan rabin jikinsa lokacin da suke fitowa, Dole duk wanda ke wajen yay kasa da kansa cikin jin nauyi. Shika gogan nasu ko’a kwallar rigarsa rungume yake da ita hankali kwance yana daga musu hannu daya alamar amsa gaisuwarsu har zuwa motar da aka ajiye domin su kawai. Sai da suka shiga har aka rufe sannan hadiman da sukal masu rakkiya ke fitowa a jirgi suma. A wannan tawaga musamman ta matan Diwa ce kawai zuciyarta ke a tsarkakake game da nado labari, amma sauran duk yan daukar rahoto ne. Sai dai kuma basu samo yanda suke so ba sam kasancewar su/Iffah’r sun musu wahalar ma gani ba kamar yanda su Uwa sukai tunani ba.
Tun daga airport har cikin masarauta jami’an tsaro ne, a cikin masarautar ma tarba suka samu da taima Iffah dadi, dan harda Malikat Haseenat da Daneen Ammarah da kanta. Sal wata da Iffahr bata sani ba amma suna kama da Daneen Ammarah sosai kuma tana kama da Jaddah. Haka kawai taji a ranta itace Daneen Waheeda da aketa fada. Lokacin da take dagowa da ga rungumar da taima Malikat Haseenat zata rungume Daneen Ammarah idanunta suka sauka kan wata kyakykyawar farar budurwa sol tana balla mata harara. Bata santa ba, dan haka ta dauke idanunta ta maida hankali ya Daneen Ammarah din cikin rashin damuwa. A hankali ta saketa ta nufi Daneen Waheeda da ke tsaye tana kallonsu kusa da Malikat Ashwaq fuskarta babu yabo babu fallasa. Gabanta ta rissina ta gaisheta tare da Malikat Ashwag din. Amsa mata tai da dan murmushin yake sakamakon kallon da Malikat Haseenat ta watso mata. Sai kuma ta nufi Malikat Bushirat ta rungume, itama dai gain kallon da ake musu ne yasata shafa kanta tana yake, Jasrah kam saita boye bayan Malikat Bushirat din dan da gaske kunyar Iffah take ji. Murmushi Iffah tai itama ta rungumeta, dan koba komai kafin faruwar hakan al ta nuna mata soyayya ta gaskiya..
Tuni shi Tajwar Eshaan ya shige ciki, dan haka itama Malikat Haseenat ta kama hanunta tana facin,”Kinga zomuje kema ki huta kunyi buda baki a jirgi babu nutsuwa”. Da ga haka ta nufi ainahin sashenta da ita dan an sake masa gyara na musamman. Bayan wucewarsu abubuwa da yawa sun faru a cikin masarautar, ciki hard jajircewar Malikat Bushirat akan komawar Iffah sashenta. A zahirance dai babu wanda ya kawo komai a ransa game da hakan, sai Malikat Haseenat ce ma take gain Malikat Bushirat din na son hakanne da tunanin Iffah ta kanainaye mata Eshaan, ta kuma san sai dai Bushirat din tayi ta gama Iffah da Tajwar Eshaan sun riga sun gama zama abu daya. Ga tabbaci nan ma a yau ta sake gani, dan duk mai hankali da zai kalli Iffah’r a yau yasan tana tare da juna biyu. Komai nata ya canja, ga kyau data kara da budewa. Yanzun ma Malikat Bushirat na gain sun nufi can ta saki wani lafiyayyen murmushi tana fadin, (yes) a zuciyarta alamar akwai abinda suka kulla a sashen kenan.
Ko dar Iffah bataji da komawarta sashenta ba. Sai ma farin ciki data tsinta kanta a ciki. Ga hadimanta duk an dawo mata da abinta, a ganinta ma ita wannan wata dama ce da zatai yakinta da kyau a yanzun. Wanka ta farayi bakinta dauke da addu’a, kasancewar duk tayi sallolinta tun a jirgi shirin kwanciya kawai tai ta haye gado abinta sai ko barci.