Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 13

Sponsored links

Gaba ɗaya suka fito a ɗakin da yake tasa jiyyar, shi yana gaba doctor na biye da shi, duk da a jikin ɗakin da yaken ne koma ace ɗakinne kawai aka raba da glass sai ya zam ƙofar shigar sai kayi kamar ɗan taku biyar zuwa shida ne. Anan ɗin ma ƙofar ta gilashi ce, doctor ya buɗe masa yana ɗan ja baya. Sai da ya fara shiga. Tsaye yay a bakin gadon batare da ya zauna a kujerar da Doctor ya gyara masa ba. Sai da ya fara kai dubansa kan na’urorin dake aiki a jikin nata, gadai bugun zuciyarta normal na’urar ta nuna, sai dai nunfashinta baya tare da ita a zahirance. Ɗauke idanun yay da ga na’urorin ya maida a kanta. Lumsassun idanunsa ya tsura mata. Har yanzu tana kwance a yanda yake hangota daga ɗakin jiyyarsa tun ɗazun, tayi wani irin fayau da ita ga uban haske data ƙara. Ƙoƙarin saita yanayinsa da ke neman fallasa kan fuskarsa yayi, batare da yace komai ba cike da basarwa yay wani irin shegen murmushin takaici mai nunin ma’anoni daban-daban da ya saka Doctor Afif yin suman tsaye dan mamaki. Shi baima san Dr Afif ɗin nayi ba, sai ma idanunsan da ya ɗan lumshe yana haɗiye murmushin ya taka a sannu gaban gadon sosai tamkar ba shi ba. Yatsunsa guda biyu ya kai kan jijiyar kanta da tai ruɗu-ruɗu kusan na minti ɗaya, kafin ya janye ransa a dagule ya dubi Doctor Afif. “A cire mata duk wata na’urar jikinta”.

A ɗan firgice Dr Afif ya waro manyan idanunsa. Har lips ɗinsa na rawa wajen faɗin, “Ranka ya daɗe na’urorin mam sune ke taimakamana ganin ɗan sauran abinda ya rage yana aiki a tattare da ita. Cirewar zata iya zama haɗari a gareta. A gafarceni idan na shiga hurumin da ba nawa ba”. Kamar ma bai fahimci bayanin doctor ɗin ba ya sake furta, “Nace a cire”.

 

Sake daburcewa Dr Afif yay, sai dai bashi da damar cigaba da jayayya duk da ya san bazai yuwu Iffah ta cigaba da rayuwa ba in har babu waɗannan na’urorin. Wayarsa ya ciro a aljihu yay kiran wata nurse da ke aiki a clinic ɗin masarautar, cikin ƙanƙanin lokaci sai gata tazo. Razana tai da ganin mai gayya mai aiki a ɗakin, tuni ta zube gwuyawunta a ƙasa tana kwasar gaisuwa cikin tsumar jiki. Da hannu yay ma Doctor nuni tai aikinta kawai batare da ko ya dubi sashen da take na. Cikin sauri Dr Afif ya ce ta miƙe, shine ya shiga nuna mata yanda zatai komai. Hannunta na ɗan rawa dan kasancewarsa a ɗakun kwarjininsa ya cika ko’ina. Abune kuma da zatace bai taɓa faruwa ba a rayuwarta duk da itama ɗin dai jinin gidan ce. Ta gama janye komai da ga jikin Iffah’r bisa umarnin Dr Afif batare da ya nemo Doctor ɗin da ke kula da ita ba. Shiko gogan na tsaye kamar wani soja idanunsa a kan duk yanda suke komai har aka kammala. Fita nurse ɗin tayi, shima doctor ya koma gefe yana son ganin ikon ALLAH.

Kanta ya ɗan rissino a hankali ya kama duvet ɗin gadon ya sake gyara mata, batare da ya dubi Doctor Afif ba ya nufi ƙofar fita yana faɗin, “Ina buƙatar ganin Sayyid Fayzul-haq yanzu nan”.

“Umarninka shine abin jirana”. Doctor ya faɗa da sauri yana buɗe masa ƙofa

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button