Daudar Gora Book 2 Page 125
“Ina bukatar ganinsa daga nan zuwa awa biyu”.Daga haka tai gaba tana kokarin hada sabon shayi da kanta. Sunyi kokarin ganin sun amsheta amma ta hana hakan, cikin kankanin lokaci ta kammala ta fice batare data sake bi takan kowa ba. Dai-dai kuma da fitowar Tajwar Eshaan cikin shiga mai sauki ta zaman gida alamar bazai fita ko’ina ba. Har yanzu fuskar cidin-cidin take babu alamar yasan minene murmushi. A sanyaye Iffah ta karasa cikin dining room din kamar yanda shima can din ya nufa kamar bai ganta ba.Kama kanta tai itama suka kai Zaune a tare tana dan satar kallonsa tai ta Kasan ido ganin ya kai hanunsa kan jug mar dauke da madara. Ta zubama madarar ido itama, wani irin kallo takema jug din na kurilla,sai kuma cikin dauke kai da cije lips muryarta a sanyaye da girmamawa ta ce, “Shi wannan madaran illane ga duk wanda ya sha shi, barinsa a inda aka gansa shi yafi alkairi”.
Shiru kamar bai jita ba, sai kuma ya waiwayo a hankali ya dubeta, fuska ta shagwabe tare da marairaiceta ta jinjina masa kai. “Dan ALLAH karka sha akwai matsala tare da madaran”.
(Ya arrahaman wai yarinyar nan mutum ce kuwa?) ya fada a zuciyarsa kaifafan idanunsa a kanta. A hankali ta daura hanunta kan nasa ta zare jug din madarar ta ajiye gefe. Shayin ta hada masa, tare da ajiyewa gabansa tana fadin “Zakaji dadin wanna shayin fiyema da madaran”.
Nan ma shiru babu alamar zaice wani abu, ya kumaki daukar shayin. Sai ma gani tai ya yunkura zai mike cike da izzar nan tasa ya taka zuwa kofar barin dining room din, Iffah ta bisa da kallo ta gefen ido zuciyarta na wata irin tafasa itama. Sai dai girmansa da kimarsa bazai barta ta nuna ba koda a fuska. Kanta kawai ta dukar, da karfi ta matse idanunta da cije lips dinta shima da karfi. Kadan ya dawo da jikinsa baya alamar dama bai fice daga dining room din ba ya kafeta da kallo.A karon farko ya saki kasaitaccen murmushin da ganinsa a fuskarsa ba karamin yaki bane. Dawo wa yay a hankali ya zauna ya dauka shayin ya fara sha. Sosai kam ya masa dadi, amma babu alamar hakan a fiskarsa. Itako ta dauke kanta gefe tama daina kallonsa. Cak taji anyi sama da ita batare da tasan sanda ya gama shan shayin ba ma.Wutsil-wutsil ta farayi da kafafu tana tura baki, bai kulata ba har sai da ya kaita bedroom ya dire a gado…
Cikin kankanin lokaci zartar da umarnin Tajwar Eshaan na rufe su Arshaan da Ameera Haifah ya zagaye masarautar. Nan fa aka fara yan kananun maganganu kamar yanda al’adar take.Yayinda kowa ke tambayar kansa mi yakai Haifah sashen Miran Arshaan din sanin babu wata alaka tsakaninsu ta zahiri face matar yayansa. Anya kuwa babu wani abu a kasa shr Tajwar Eshaan din ya shinshino dan kasancewar tasu tare kam dole akwai wani al’amari mai girma na boye. Wasu ma dai tuni suka fara fassara al’amarin da cewar akwai dai abinda suke aikatawa. In ba hakaba minene ya kaisu haduwa a irin tsohon daren nan ba mata ba, ba kanwa ba, ba uwa ba ko wata shakikiya, kuma har takaisa da neman kasheta irin haka. Labarin ya fara zama gaskiya lokacin da Jasrah ta farfado. Cikin kuka take sanarma Mammah da take dubata tare da Malikat Bushirat cewar dama ta taba zargin Haifah a wani lokaci da tai kiransa tsakar dare, ranar ta samu damar ganin kiranne dalilin manta wayarsa da yay ya fita wani kiran ujila da batasan wayayi masa ba. Tana dagawa Haifah ta yanke kiran, sai dai ta riga taji muryata, koda ta dauki number ta kira da wayarta ba’a daga ba, washe gari ta bada a mata bincike kan number din aka tabbatar mata bata akan waya.