Daudar Gora Book 2 Page 124
Koda ya fito bayan tsahon lokaci da ya dauka a bayin bai nema Iffah ba dan yana bukatar kadaici saboda ya shiga bacin rai, shi mai kishi ne, tabbas yanada matukar kishin da yake ji akan yarinyar nan zai iya badda mutum. Wata irin tsanar Miran Jasim da Miran Arshaan yake ji irin wadda bai taba ji a kansu ba a dukkan abubuwan da suka aikata masa a baya, ga wani irin sara masa da kansa yake yi na ciwo. Jikin window ya karasa hannunsa goye a bayansa batare da ya cire ko bathrobe din jikinsa ba yana kallon sararin samaniya da ke hada was irin manyan bakaken giza-gizai na hadari, du da safiyar tayi sosai garin yaki washewa sai ma rinewa yake sake yi kamar za’ai wata sabuwar magriba. Kiran waya ne ya shigo, ya share kamar bai jiba, aka sake kira nan ma kamar zai share sai kuma ya nufi wayar a fusace ya daga. Sai dai yay shiru baice komai ba. Da ga can Sayeed Fayzul-haq ya gaishesa cike da girmamawa.Haushin kowa yake ji, duk da bashi yay lefin ba ya samu rabonsa. Dan maimakon amsa gaisuwa a dake ya ce, “Ya akai”. Dan rikicewa Sayeed Fayzul-haq yayi, amma sai cikin dauriya da sake kankan da kai ya shiga masa bayanin abinda ke faruwa tsakanin Miran Arshaan da Ameera Haifah tun a daren jiya. A zafafe ya ce, “Kaima jami’ai magana su kamashi a hadashi da dayan sakaran, a saka na’urar daukar magana cikin akin kurkukun kuma.Itama Haifah din Doctors su sallameta idan babu wata matsalar data shafi lafiayarta jami’an tsaro su rufeta”,. Daga haka ya ajiye kan wayar yana huci. Duk yanda yake kokarin rike kansa da bin komai a sannu ya fahimci ba haka makiyansa suke bukata. Fushinsa suke son gani, ainahinsa suke bukatar ya nuna musu. Ya barsu da yarinyar nan ne kawai domin shi din shugaba ne, shugaba kuma da hadiyewa aka sansa, amma tunda so suke shi ya fito musu a Eshaan In Haysam Abdul-majeed Aliy Qutb din sa to yanzu ne wasan zai fara..
A bangaren Iffah kam itama dai wanka tai ta gyara jikinta, yunwa ta hanata cigaba da zaman dakin ta fito neman abinci. A irin wannan lokacin. Babu kowa a falon sai daddadan kamshi da sanyin ac mai ratsa
bargon jiki, mamaki ya kamata, duk da dan sanyi-sany in garin na hadarin dake tasowa dan fitina sai an kunna na’urar sanyaya waje, baki ta tabe abinta ta nufi dining room din da glass ne kawai ya gitta tsakaninsa da falon dan komai a tsare yake.
Shayi tai kokarin fara sha dan shi take bukata, wani irin masifar sarawa kanta yay lokacin da hanunta ke sauka kan abinda aka zuba shayin. Janye hannun tayi da sauri ta kurama flaks din shayin ido, sake kai hannu tai a karo na biyu, nan ma kanta ya kara sarawa al’amarin kamar wata almara. Sake janyewar dai tayi tana kaiwa zaune jagwab idonta akan flaks din dai. Ta kwashe mintuna uku tana kallon sa sannan ta sake daurawa a karo na uku, yanzu kam duk da abinda takeji a jikinta na azaba bata cireba tsahon wasu mintuna. Idanunta sunyi jazur cikin kankanin lokaci, gaba daya kamanninta sun canja kamar ba Iffah’r ba. A wani irin fusace ta mike dauke da tray din da flaks din ke kai zuwa kitchen.
Taku take cikin nutsuwarta da kasaita ki tarwada ko budurwar hawainiya.
Kwarjininta da cikar kamalarta kan shafe karancin shekarunta musamman dan tana a cikin irin wannan yanayin. Kasancewarta a kitchen ba karamin rudani bane ga ma’aikatan cikinsa. Hannu kawai take daga musu da ga gaisuwar da suke mikowa gwiyawunsu kan kasa. Kwalayen gayen shayi uku da daya daga cikinsu ke kokarin fitarwa ta zubama idanunta da sukai jazur.