Daudar Gora Book 1 Page 65
A mataki na biyu shine zagayawa da Zawjata-almilk takai gaisuwa ga duk wanda ke wajen, kasancewar kakanni ne makusanta da iyaye, da yayye. A yanzu dai kam da taimakon Jasrah ta motsa, bayan ta janye hular rigar alkyabbar jikinta data hana kowa kallon ainahinta a tun farko. Duk da Iffah taji ta takura, hakan wata damace a gareta na sanin dukkan masu faɗa ajin, zai kuma zama jagoran abinda zai taimakawa nata ƙudirin. Idanunta suka cika da hawaye, a lokacin da take durƙushe gaban Malikat Haseena matsayin bankwana. Tanajin tsohuwar a ranta, ta kuma samu wani kebantaccen ilimin zamantakewa da ita. Ta saka mata albarka tare da yaba ƙyawawan halayenta da jinjinama iyayenta tarbiyyar da sukai mata. Ta ƙare da fatan alkairi da samun zuri’a mai albarka tsakaninta da Shahan-shan. Waɗan nan zantika sun zama abin kaiwa da komawa a zukatan manyan masarauta. Dan kowa na ganin kamar wata isharace Malikat Haseena ta isar cewar ta karɓi Iffah ɗari bisa ɗari matsayin Zawjata-almilk fiye dana baya da suka gabata. Iffah a karan kanta taji tausayin tsohuwar bisa ƙudirinta na shigowa daular ruman data tabbatar yasha banban da fatan da Malikat Haseena tayi gareta a yau gaban duk wanda ya isa a ƙasar ruman ma ba daular ruman ɗin kawai ba. Har yanzu har gobe da jibi tana akan bakanta na ɗaukar fansar rasa ƴan uwanta. Abin harinta kuma ɗaya ne tal shine Tajwar Eshaan, inma da wanda zasu biyo bayansa sai ta gama da babban dodon nasu. Ta samu ƙwarin gwiwar hakanne da tabbacin jin sai an kai matan turakarsa ake fiddosu babu rai. Sai kuma bincike da shaƙiƙansa guda huɗu sukai yunƙurin ɗaurata a yanzu haka. Kenan babu buƙatar wasi-wasi koma minene shike ƙullasa…
Malikat Bushirat ma tayi irin makamancin addu’ar Malikat Haseena ne ga surukar tata. Ta ƙara da faɗin ita ɗiya takejin ta samu ba Suruka kawai ba, tana kuma fatan ta kasance kibiyar ajali ga masu ƙudirin sharri a ciki da wajen daular ruman. Tabbas maganar Malikat Bushirat tafi ta Malikat Haseena ɗumama zukatan wasu, yayinda mugun ƙudirinsu akan Iffah ya ƙara hauhawar farashi a zukatansu, amma duk sai suka ɓoye suma sukai mata irin tarbar data ɓoye dukkan ainahinsu. Dan Miran Jasim ma da akazo kansa har ƙyauta ta musamman ya gabatar ga Zawjata-almilk.
Iffah data kasance cikin ladabi da ƙawata harshenta gaban kowa yayin miƙa gaisuwarta duk da ƙarancin shekarunta kaifin basirarta da wayonta ya bata damar nazari da adana cewar kowa a wajen da fuskar daya tarbeta ta hanyar kallonsu a ƙyalkyalin jikin rigarta datai matuƙar taimaka mata harta ambata godiya ga Malikat Haseena data zaɓa mata rigar domin sakawa a yanzun. Ba kalaman kawai ta riƙe ba da fuskokinsu da suka fita tartar bisa taimakon hasken kwayayen wutar lantarki. Harda sunayensu sun kasance kamar wani zane akan dutse cikin ƙwaƙwalwarta da zuciyarta.
Ƙarfe goma da kusan mintuna talatin taron ya tashi na dare, aka fara fita da Zawjata-almilk da kowa ke tunanin sashenta za’a kaita kai tsaye. Sai kuma hakan ya bambanta da tunaninsu a lokacin da Malikat Haseena tabi bayansu akan wheelchair ɗinta matsayin maiyin wannan rakkiya. Abu ne da ba’a taɓa gani ba a masarautar. Dan hatta Malikat Bushirat da Daneen Ammarah sun sake jinjina wannan soyayya mai ƙarfi data shiga tsakanin Malikat Haseena da Iffah. Sai dai hakan ya musu daɗi, musamman Malikat Bushirat da take ganin hakan matsayin ƙarin sanin wanene Shahan-shan a zuciyar Malikat Haseena ga maƙiyanta.
A lokacin da kowa ke fitowa daga falon da walimar ta gudana bayan gama sallamar sai da safe gagarumin labari da ɗumi-ɗuminsa shine cin karo da motar data ɗauka Malikat Haseena da Iffah a ciki ƙofar sashen Shahan-shan. A wannan karo hatta da Malikat Bushirat da Daneen Ammarah sai da sukai turus dan shirine da sam basu san da shi ba. A take suka koma ƴar kallo a tsakaninsu, cikin tambayar juna yaya akai haka kuma? Da idanu. Rashin amsa da mai basu amsar ya sasu shanye komai……