Daudar Gora Book 1 Page 59
Knoking ƙofar daya wanzu a dai-dai lokacin ya sata jan numfashi a sauƙaƙe. Da ƙyar ta iya miƙewa daga zaman daɓaron da tayi ta buɗe. Daneen Ammarah ta sakar mata murmushi. Cikin yaƙe ta mayar mata da murtani da matsawa ta bata hanya. Rissinawa hadimar da suke tare tai ta gaisheta, hannu kawai ta ɗaga mata alamar amsawa tana bin ledar hanunta da kallo……
Kamar yanda aka sanar da Barrister kai tsaye station ɗin da akace su Babiy suke suka nufa. Kasancewarsa babba kuma sananne basusha wahalar ganin ogan station ɗin ba kai tsaye. Sunyi gaisuwa irin tasu ta manyan ma’aikata, su kai kuma gaisuwar girmama juna da su Kaka.
Barrister ya gabatar da kansa, ya kuma gabatar da abinda suke tafe da shi harda hoton su Babiy domin sauƙaƙawa. Jami’in yay shiru yana kallon hotunan kamar mai hasashe, sai kuma ya ɗago ya kalla Barrister “Gaskiya banajin akwai waɗan nan mutanen a wannan station ɗin Barrister”.
Barrister daya fahimci matsala ce ke neman shigowa yay ɗan murmushi da muskuta zamansa. “Yallaɓai adai sake dubawa, zata iya yuwuwa ko akwaisu ɗin baka da labarin hakan. Amma tabbas suna a wannan station ɗin. A matsayina na Barrister ba nazo nan dan a bani belinsu bane ba, duk da nasan basu da hannu a abinda ake zarginsu. Nazo ne dan na gana da su, sannan a miƙasu kotu saboda nasan dai ita matar data saka aka kawosu nan burinta a kwatar mata hakkin mijinta”.
“Iya gaskiyata nake faɗa maka Barrister babu waɗan nan mutanen a wannan station ɗin. Amma mizai hana ku sami ita matar na tabbata tunda tare da ita akaje tasan wane station ne”.
Barrister yay shiru yana kallonsa cike da nazari. Hakama Kaka da Abu Zainab. Kusan minti biyu shiru babu wanda ya motsa, kafin Barrister ya miƙe yana ɗan murmushi ya bashi hannu. Suma su Abu Zainab miƙewar sukai…
Da kallo ya bisu har suka gama ficewa, ya kai hannu kan wayarsa dake saman desk ɗin sa yana wani murmushi. A bugu biyu aka ɗauka wayar daya kira. Sallama kawai yay da faɗin, “Kamar yanda kai hasashe ranka ya daɗe yanzu suka bar office ɗina”.
Shiru yana sauraren mi’ake faɗa daga can, sai kuma yay murmushi da amsawa da “Angama ranka ya daɗe”. Daga haka ya ajiye wayar yana wata ƴar iskar dariya
Abu Zainab daya kasa fahimtar komai saɓanin Kaka da Barrister dake hangen wani abu dalilin kashedi da akai musu kafin zuwansu nan dama ya katse shirun da motar ta ɗauka ta hanyar nisawa. “Anya kuwa wannan jami’in akwai gaskiya a maganarsa Barrister. Kagafa yanda yake ƙyaf-ƙyaf da idanu kamar tsohon ɗan jari hujja. Nifa wannan al’amari ya fara bani tsoro wlhy”.
Barrister da zuciyarsa ke kai kawo ya fesar da huci, “Kana tunanin yaƙi faɗa mana gaskiya ne Zakariyya?”.
“Fuskarsa ta nuna hakan ai Barrister, ko kuwa Kaka?”.
Kaka da shima dai yake aune-aunensa a rai ya girgiza kansa. “Zata iya yuwuwa gaskiyar ya faɗa, sai dai kumin wani taimako ɗaya dazai warware mana gaskiyar tasa ko saɓaninta, bayan nan zan sanar muku abinda ya faru kafin zuwanmu nan”.
Barrister da shima abinda ke’a ransa kenan ya ɗan juyo ya kalla kaka ta madubi, “Muna jinka Baba”.
“Muyi gaggawar isa gidan Dawood”.
“Shawara mai ƙyau Baba”.
Barrister ya faɗa yana juya motar hanyar da zata kaisa gidan Abu Moosa.
“Mamy kuma duka wayar da lap-top ɗinne nawa?”.
Iffah ta faɗa da mamaki. Murmushi Daneen Ammarah tayi, “Ibnati wannan ai ba komai bane ba, sannan ko baki faɗa ba kina buƙatar su tare da ke kodan ki dinga jin motsin gida. Na biyu kuma wannan aikin da zaki fara kowa yasan mai haɗari ne, dolene ki kasance da waya a duk inda kike a masarautar nan. Da zarar Kinga abinda zuciyarki bata kwanta da shi ba a cikin mu huɗun zaki iya kiran kowa ki sanar masa. Lap-top kuwa ni naga ya dace na kawo miki ita domin ɗebe kewa. Amma kiyi taka tsantsan ki kuma kula sosai, dan samun waɗan nan na nufin zaki iya mu’amula da kowa musamman a yanar gizo batare da kin samu tabbacin wanene ɗin ba”.
“Haka ne Mamy, insha ALLAH zan kiyaye. Nagode sosai ALLAH ya saka da alkairi”.
“Karki damu kin cancanta ne ai”.