Daudar Gora Book 1 Page 23
Kai Ummu ta shiga jujjuyawa hawaye na kwaranya a idanunta, “Ibnat…”
“Na roƙeki kar kice komai Ummuna, albarkarki itace mafi ƙololuwar buƙata ga ruhin daya daɗe da zama cikin tahin gawa. Ƙaddarata rubutacciya ce tun daga alƙalamin da idan yay rubutu babu wani duster dake iya gogesa”………..✍
ALLAH sarki Iffah, ALLAH ya baki damar yaƙi irin wanda ya dace da fatanki na alkairi🙏🏻😭
………Kalaman Iffah sun zama mafi ƙololuwar zama famin gyambo a zukatan Ummu da Babiy harma da Hanash. Sun zanu da zanen da zuciya ta killace koda tunasu zai zama mai raɗaɗi a cikinta. Sun karɓa domin karɓar ta zama tilas a garesu saboda rashin murya da ƙarfin iko da suka rasa a hannayensu. Sun cigaba da kuka saboda kukan shine kawai mafita a garesu. A haka kwanaki suka cigaba da tafiya da raunin zukatansu har zuwan ranar juma’ar da masu ƙarfin iko suka tsaida matsayin ranar ɗaurin auren ƴarsu. Bayyana ko misalta kasancewar wannan dare da wayewarsa ma ɓata lokacine game da halin da ahalin malam Zayyan suka tsinci kawunansu. Babu wani alamomin biki daga ɓangarensu sai ma zaman makoki. Dan bayan Iyyani da Kaka da wasu dattijai da basu gaza biyar ba a cikin zuri’arsu babu wanda ya halacci wannan makahon aure hatta da maƙwaftansu. Bisa tilastawar Kaka Babiy da Hanash sukai shirin halartar massallaci yin sallar juma’a da riskar abinda zuciyoyi ke tsananin ƙuna a kansa. Sun tafi sun bar Ummu da Iyyani da tazo itama a yanayi mai ban tausayi. Amarya Iffah kam idanunta ma babu wanda ya gani a wannan safiya abinci ma Iyyani ta bita da shi har ɗaki….
Bayan gushewar wasu awanni, masu tafiya da ƙarfin bugun zuciya busa irin ta sarakai da tashin tambura ya karaɗe cikin birnin Daular Ruman dake cike da manyan baƙi tako ina. Dan kuwa sarakuna goma cif na ƙasar Ruman duk sun halarta duk da suma akwai raɗaɗin rasa ƴaƴayensu a zukatansu har yanzu. Koda yake wasu a ciki sun bada ne da kwaɗayi na burin zamowar ƴaƴan nasu zama matan Shahanshan, suna ganin hakan wani ɗaukaka ce a garesu da samun wasu damammaki……
Iffah dake kwance a ɗaki zuciyarta a bushe, idanunta dake zubda hawaye a ɗazun a soye ta jiyo bayanin ɗaura aurenta da Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdull-Majieed daga bakin su Kaka. Wani irin dimmm taji a cikin kunnuwanta tamkar ɗaukewar wutar lantarki daga tashar gidan redio, ta koma ita ba wadda ta suma ba, ba kuma wadda ke a raye ba tsabar tsintar kai a wani hali. Ta jima a haka kafin ta dawo hankalinta kwakwalwata ta fara tantance abinda taji ɗin. Kenan abinda ya faru da yan uwanta a wasu watanni da suka shuɗe itama shine ya faru da ita yau? Itama zata mutu mutuwar rashin gata da ƴanci a hanun azzalumin mai mulkin Ruman da jama’ar cikinta. Daga yau za’a koma ƙirga mintuna da daƙiƙun mutuwarta da suka rage mata, daga yau tayi bankwana da Ummu, da Babiy, da Hanash Akhi da su Kaka. Anya kuwa zata iya? Anya kuwa sadaukarwar nan ta dace da rubutattun burukanta? Anya kuwa zata iya jurewa? Kai ina bazai yuwu ba. (Mizai hanasa yuwuwa? Bayan zakije inda ko kuwwa kikai babu maijin muryarki?) wata zuciya acan gefe ta ayyana mata. A karo na farko hawaye masu zafi da raɗaɗi suka silalo bisa kumatunta da gudu. “Dole ma na jure, jurewa irin wadda a duk faɗin duniya labarina zai karaɗesa a lokacin dana hukunta Tajwar Eshaan ibn Haysam ibn Abdul-majeed”. Ta faɗa cike da ƙwarin gwiwa na tabbatar da burin mai ɗaukar fansa.
Batare data goge hawayen dake cigaba da rige-rigen zubo mata ba ta sauka a gadon tana tangaɗin jiri. Wayar data maida ta ajiye da ƙudirin ta daina amfani da ita ta lalubo, haɗata tai ta kunna, sai dai tai ɗan jimm namai nazari kafin ta fara rubuta saƙo. Minti biyu bayan turawa kira ya shigo. Numfashi ta fesar, sai kuma ta saki murmushin takaici jin abinda aka faɗa daga can.
“Sir bamu da lokacin tattauna wannan a yanzu”.
“Na sani Fareedah, sai dai inajin matuƙar tsoro, tsoro irin wanda ko’a ido aka kalla an san tsoro ne. Nasan na rasaki na har abada a yanzu”.
Murmushin takaici ya suɓuce ma fuskarta, sai dai ta hana hawayen da suka ciko mata ido zubowa. “Wannan shine tsoron dana gudar maka fuskanta tun farko dama duk jama’ar Ruman. Amma bazan gajiya ba, plan A dama yaƙin sunƙuru ne, plan B mafi haɗari amma da yaƙinin nasara”.
“Ta yaya Fareedah? Kin san kuwa waye Shahanshan? Kin san minene girman ikonsa?…..”
“Na sani mana tunda nima a ƙasar aka haifeni. Sannan na zama cikin ahalin da sukafi ɗanɗana ɗacin girman ikon nasa da zalunci. Karka damu da haɗari sir, taimako ɗaya zakamun a wannan plan ɗin wanda babu wani abu da zai shafeka da iznin ALLAH”.