Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 112

Sponsored links

Dukansu gumi suke na tashin hanakali, sai dai babu wanda ya iya cewa komai har zuwa wani tsahon lokaci. Sayeed Harun Al-rashid ya nisa yana mai share ɗan gumin daya taru masa a goshi. Ƙyaƙyƙyawar fuskarsa fara tas gaba ɗaya ta ƙwaɓe alamar rashin damuwa. “Zartar da hukunci bazai yuwu yanzu ba Barrister, amma kaje zuwa anjima zakaji komai ta waya”.

“Babu damuwa ranka ya daɗe”. Barrister ya faɗa cikin jimami shima, sai dai acan ƙasan ransa dariya yakeyi, yayinda wani gefe na zuciyarsa ke tabbatar masa akwai wani babba mai alaƙa da case ɗin bayan su, shiyyasa bazasu iya zartar da hukuncin ba kai tsaye. Yau ma dai an rakosa da kuɗi masu yawa har mota..

A kwanaki biyun nan abubuwa da yawa sun faru tako wane ɓangare, sai dai marasa daɗi sunfi masu daɗin rinjaye. Zuwa yanzu dai da gaske ƙasar ruman da jama’arta suke basa buƙatar Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed matsayin Shahan-shan. Dan tun tsirarun mutane na zanga-zanga a wasu jahohi takai yanzu ƙasar ma gaba ɗaya ta ɗauka. Abu mafi ban mamaki harda wasu a manyan ƙasar na nuna goyon baya ga talakawa, ciki kuwa harda wasu Tajwar na jihohi. Yayinda ta wani gefen kuma hankalin wasu manyan ƙasashen duniya ya fara dawowa kan zanga-zangar dama dalilin yinta.

 

Babban abinda ke tunzura jama’a shine biris daga Shahan-shan, yayinda kuma a cikin gida hankalin ƴan majalissar sa ya rabu kaso biyu, wasu na goyen bayan ya saukan wasu na buƙatar karya sauka dan shine kawai ya cancanta da kujerar a ganinsu. A talakawan ma bai rasa tsirarun masoya ba, sai dai basu da ƙarfin ja da masu boren shiyyasa suka koma gefe sukai shiru matsayin masu kallo da ido.

A kwanaki biyun nan yanda Daular ruman ke a hargitse haka Iffah ke a hargitse. Kuka kam idanunta har sun daina fidda ruwan hawaye. Cikin ƙanƙanin lokaci tayi wata irin rama mai ban tausayi. Haukan da iyalan Sayeed Khairul-Bashar keyi a masarautar da wanda jama’a keyi a waje sai ta ɗaukesa wasan yara. Idan su da suka rasa uba kawai zasu harmutsa masarautar haka ina ga ita data rasa ahalinta duka, a ganinta ita ya cancanci ta hargitse ƙasar ruman baki ɗaya ma ai. Sai dai yanda ƴan zanga-zanga ke daɗa ƙaruwa na saka mata farin ciki, dan abin ban mamaki har wasu a cikin Tajwar na jihohi suma sun ƙara tunzura wuta da bada goyon baya akan saukar Shahan-shan ɗin, hankalin ƙasashe kuma ya fara dawowa ƙasar ruman, da alama dai dama a jirace kowa yake da wannan damar. Hakan na sake tunzura ƙwarin gwiwar ƙudirinta.

Wutar wannan al’amari na ƙara ruruwane dalilin shirun Tajwar Eshaan. Babu shi babu cewarsa, harma wasu sun fara tunanin anya kuwa yana cikin masarautar ma ko?…. Duk wannan bai damu Iffah ba a yanzu, hankalinta gaba ɗaya ya tattara ne akan ta ina zata samo dafin maciji. Bata da wani amintacce a cikin masarautar, a waje kam sir Fawzan ne kawai, shima kuma zuwa yanzu ta fara shakku akansa saboda tana ganin ya ɓoye mata abinda ya faru da su Babiy ne bisa wata manufa. Idan tace zata fita a sulale daga masarautar taya kuma zata dawo cikinta? Wannan ƙalubalen keta faman mata kaikawo harya gagara samun mafita a kwanaki biyun nan. Tana a bangarenta bata ganin kowa kowa baya ganinta, waɗan da zasu iya ganinta hankalinsu a tashe yake dan kai tsaye su abin ya shafa, shirunsu kuma sai ya bama Iffah damar fassarashi da abinda zuciyarta ta gama tabbatar mata, dan haka itama a yanzu ta haƙƙaƙe bata da lokacinsu.

Kamar yanda ta tsara bayan sallar la’asar ta shirya tsaf cikin abaya data amshi jikinta, dan ma ta rame ga idanunta da suka ɗan kuklumburo amalar taci kuka bana wasa ba. Duk da masarautar a harmutse take haka ta keta cikinta hadimanta na take mata baya har sashen marigayi Sayeed Khairul-Bashar. Tayi matuƙar mamakin tarbar data samu dan batai zaton irinta ba, sai dai abinda bata sani ba shine su kallon tausayi suke mata da tabbatar da itama bawai ta tsira bane a hannun azzalumin. Dan malamin duba da matar Sayeed Khairul-Bashar ɗin ta ziyarta tun lokacin daya ɓata kafin aga gawarsa ya tabbatar mata akwai ƙulli mai girma da Shahan-shan keyi game da rayuwar Iffah shiyyasa itama bata mutu ba a sanda aka kaita sashenshi. A ranar bata ɓoyema ƴaƴanta komai akan zancen nan data jiyo ba, sun kuma yi niyyar samun Iffah har sashenta da batun washe gari aka tashi da wannan tashin hankali. Wannan shine dalilinsu na mata tarbar data bata mamaki.

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button