Daudar Gora Book 1 Page 106
Zabura Iffah tai jikinta na rawa. Sai dai ta kasa faɗin abinda ke son fita a bakinta. Ya ɗaga mata hannu da faɗin, “Kinga kwantar da hankalinki, amshi wannan ki kalla. Idan kin kammala sai ki yankema zancena hukunci. Amma ki sani tabbas ta hanyar da aka halaka iyayen nan naki da ita ake bi wajen halaka waɗan nan matan nasa shiyyasa likitoci basa gane komai na barki lafiya..”
Harya ɓacema ganinta Iffah bata iya ta motsa ba, sai dai rawar jikinta da karkarwa a bayyane take. Jin kamar motsin mutane ya sata ɗaukar flash ɗin daya ajiye mata ta sake ɓoye wa. Jami’in ɗazunne ya dawo ɗakin, a wannan karon sun ɗauka hotunan komai a ɗakin da ɗan sake bibbincikawa dan tare yake da yara biyu jami’ai suma. Dole Iffah ta sake lafewa har suka fice sannan itama ta fito.
★ A yanzu kam masarautar a harmutse take fiye da ɗazun, hakan ya sake bama Iffah damar komawa sashenta cikin matuƙar tashin hankalin abinda ya faru da zantukan wannan mutumi. Kulle kanta tai a ɗaku ido rufe ta saka flash ɗin a jikin laptop ɗinta da bawani amfani dake da shi ba. Abin tamkar wani film video ya fara da shigar Babiy riƙe da Abu Moosa cikin gidansu a waccan ranar, shimfiɗa tabarmar Ummu da bayanin Abu Moosa da bai kammala ba har mutuwarsa. Zuwan matar Abu Moosa da jami’an tsaro abinda Hanash yay mata da tafiya dasu. Daga nan ya yanke. Da sauri tai playing na gaba. A yanzu kam su Babiy ne a mawuyacin hali duk sun rame sunyi baƙi a cikin wani ɗaki. Kan Babiy a saman cinyar Hanash alamar babu lafiya tare da shi, Hanash nata faman shafa masa ruwa a fuska yana kuka. Sautin dariya ne ya fara tashi a ɗakin, kafin shigowar wani mutum da iya jikinsa kawai ake gani babu fuska. A take su Hanash suka zabura yayinda sautin dariya ke tashi da tafa hannayen mutumin. Bayan anyi dariyar mai tsawo aka tsagaita, ƙirjinta yay wata irin bugawa jin muryar Shahan-shan. “A tunaninku bayan samun tagomashi a jinin yaronku ƴan baiwa zan haƙura ne. Ina bazai yuwuba, dan a kaf yaran dana halaka jinin ƴaƴankune na farko daya bani fiye da nasarar da nake buƙata, shiyyasa na fara bibiyar ta uku daku kanku saboda bincikena ya nuna min daga jinin ubansu ne”. Hhhhhhh! Hhhhh!! Kune nasarata ahalin Zayyan. Kune nasarata dole ne kuma na samu hhhhhhh!!!”.
Kuka Hanash keyi da roƙonsa amma babu alamar zai sauraresa. Sai ma wani irin salon siddabaru da yakeyi da hanunsa a take ɗakin ya turniƙe da hayaƙi, sai kuma wata irin guguwa mai ƙarfi ta nannaɗe hayaƙin a tsakkiyar ɗakin. Su Babiy dai tuni sun maƙure a bango. Sai kuma suka shiga ihu ganin guguwar ta zama wani irin maciji daya kusa cinye kashi ɗaya bisa ukun ɗakin, sara ya fara kaima su Babiy da suka dunƙule waje ɗaya shi da Hanash, kafin macijin ya kafa kansa a wuyar Hanash dake ƙanƙama Babiy. Tuni duhu ya gama mamaye jikin Iffah dake karkarwa, ta rufe laptop dan zuwa yanzu ma kukan ya kafe ƙaf a idanunta. Sai wani irin mahaukacin ja da sukayi kai kace wuta aka haɗa a cikinsu. Tun tana iya jin surutan masarautar har ta daina jin komai. Daga haka sai farkawa tai ta ganta a gadon asibiti Daneen Ammarah tare da ita..
Gaba ɗaya ta tsani komai daya shafi Tajwar Eshaan. Dan haka tun buɗe idon farko da tai ta ga wadda ke tare da ita bata sake yarda ta buɗe ba. Hakan yasa Daneen Ammarah bata san ta farka ba. Dama itama kuma tayi matuƙar nisa ne a cikin tunani a kallo ɗaya ma zaka fahimci bata tare da nutsuwarta. Ga wata ƴar rama ta yini ɗaya sakamakon tashin hankalin da ake ciki tattare da ita. Dan tun kai gawar Zawjata-almilk da Sayeed Khairul-Bashar makwanci ba daular ruman kawai ba gaba ɗaya ƙasar ruman a harmutse take. Yau wasu a cikin talakawa sunyi ƙarfin halin fitowa zanga-zanga a wasu jahohin suna kiranyen Shahan-shan ya sauka ko su ɗauka doka a hanunsu.