Bakon Lamari 1
Lumshe Manyan idanunshi yayi yana shafo gemun shi a hankali yana jin sautin kukan ta yana tashi ta cikin wayar dake kare a saman kunnen shi.
Magana take masa wadda tsabar yadda take masa kuka, ya hana muryarta fitowa.
“Yaya dan Allah kazo kano, ina cikin matsala babu wanda zai fuskance ni sama da kai yaya, duk yadda kake tunanin matsala ta tawuce nan Yaya ka taimaka mini”
Shuru yayi mata tamkar bada shi take magana ba, sai da yaga dama dan kanshi sannan yace.
“Amatu! ki haƙuri da rayuwa kowa sai da ya fuskanci matsaloli kafin ya kai inda yake son kaiwa a rayuwa, Pls kada ki ƙara kirana kinga ke Matar aure ce”
Miƙewa tsaye yayi tare da yada wayar yana mai shiga cikin bedroom ɗinshi, Dogone sosai mai suffar ƙarfafan maza kasancewar sa Soja wanda yasha gwagwar mayar training duk wata halittar ƙarfi ta buɗe ajikinsa, fari ne tas mai manyan idanuwa tare da dogon hanci ga wani gemu daya aje wanda ya bawa kyawun fuskar shi damar ƙara bayyana daga saman goshin sa kuma ƙaton tabon abin sallah ne wanda har wani ƙurzunu, ƙurzunu yayi yay girma sosai, saman kanshi kwa ƙwalƙwal ne bai bar suma ko ɗaya ba, bashi da yawan sakin fuska bare ka saka ran ganin dariyar shi, ya mallaki hankalin kanshi dan a tsarin shekarunsa na haihuwa zai kai shekaru talatin da takwas ( 38 ).
wanka yayi tare da shiryawa cikin uniform ɗinsu na sojoji army green, ya fita waje tare da rufe ƙofar shi ya nufi filin dake cikin barrack ɗin wanda anan suke horar da ƙananun sojoji yadda zasu yi dabarun yaƙi.
Bai yarda ya saka tunanin ta ko kukanta cikin ran shiba haka ya mayar da hankalin shi wajan aikin dake gaban shi.
Ƙit! ya katse wayar yana mai fesar da zazzafan Huci ta cikin bakin shi.
Ta yada wayar tana mai rufe bakinta sabida tsabar kukan dake ƙara tawo mata.
A fili take furta.
“Ameerah kin cuce ni da kika samon Numbern Yaya kika ce, na kira shi nina san Koda yana da mafita baze min komai ba, Nina san Yaya baze taɓa taimakona ba a rayuwa, Zan cigaba da addu’a Allah ya kawon mafita acikin lamurana”
Ta faɗi tana mai kifewa a saman haɗaɗɗan carfet ɗin dake falon.
Tsawar da aka daka mata tasa ta ɗago da sauri nan da nan jikinta ya soma rawa sabida haɗa idanun da sukai da mijinta IMRAN!
“Bani wayar hannun ki, Uban wa kika kira macuciya shaiɗaniya?”
Jikinta yana rawa ta miƙa masa wayar sabida tsabar yadda take jin tsoron shi Ko muryar shi taji firgita take yi.
Hannun imran har karkarwa yake sabida zumuɗin yaga wata kira idanun shi ya sauka akan Numbern da tayi saved da Sunan Yayanmu.
Ya cilla wayar ta daki Tv stand sannan ya wani kwashe da dariya wadda har ta saka yana dafe cikinsa.
“Kar dai Har yanzu Zuciyarki bata haƙura da maitar son AHMAD ALI Ba? to kima jini da kyau Ahmad yayi miki nisa duk da yana Ɗan uwanki jininki yayanki Amman a yanzu yayi miki nisan da har abada bazaki kamo shiba”
A gigice Amatullah ta ɗago idanunta fal hawaye bakin ta har rawa yake wajan furta masa.
“Tir da irin munanan kalaman ka Imran Allah ya kiyashe ni yin soyayyah da Aure na aka, Inma ƙazamar zuciyarka tana raya maka hakan maza ka kawar wallahil Azim Ni Amatullah Shu’aib Makama! ban taɓa jin son Yayah Ahmad cikin zuciyata ba………
Bai jira ta ƙarashe maganar tata ba ya janyota ya haɗeta da bango ya shaƙe mata wuya yana faman zare idanu kamar mai taɓin kwakwalwa.
“Nine zan miki ƙarya in ba son shiba mai ya kaiki ki masa waya dan ubanki ƴar matsiyata”
Yakai maganar yana tofa mata yawu a fuskarta, Hannu ta sanya ta dafe Wuyanta tana kakarin Amai sam bata damu da yawun sa ba, face Kokawar da take numfashinta ya dawo.
Zubewa tai saman kujera tana hawaye hannunta har lokacin yana wuyanta.
Ya koma da baya ya zauna saman kujerar dake kallonta, Yana mai laluba aljihunshi wiwi ɗauri guda ya ɗauko ya kunna ta yana sha nan da nan hayaƙinta da warinta suka cika mata ɗaki ƙoƙarin yin amai take yaƙi bata dama sabida matsawar da yayi gabanta yana watsa mata hayaƙin yana lumshe mata idanunshi da sukai fici fici suka koma jajir babu ko kyawun gani.
Bakinta fal da yawun data kasa haɗiya sabida Warin wiwin daya tokare mata maƙoshi.
“Imran ka matsa kada nai maka amai ajikinka wai kai wani irin azzalumi ne in Allah ya yarda sai Allah yayi maka abin da yafi wanda ka min dan shi adalin sarki ne baya zalunci kuma ya hana a zaluntar”
Ta faɗa tana miƙewa daga wajan.