Wace Ce Ita Book 2 Chapter 53
Saddakarwa kawai tayi wani sabon zawon na zubo mata, hawaye ne suka shiga zubo mata kamar famfo, haka zawon shima yake tawo mata kamar ruwan famfo, giving up kawai tayi tayi relaxing a toilet seat dan ko tsarki bazata iyayi ba, toh ina taga ta tsarki bayan zawo be tsaya ba?……..
Abby daya tsaya a gefe yana wuce gajiyar faduwar daya kusayi da niyar ya dan samun kwarin jiki sannan yaje ya duba meke faruwa a cikin jirgin kawai sukaga an jewo khaleel ta window, inda Allah ya taimakesa anan su abby suke tsaye da securities dinsa da basu shiga cikin jirgin ba saboda Abby be basu umarni ba, shi kuma fadin daya kusayi ne ya sasa rikicewa, saura kadan khaleel ya dira akan Abby securities din Abby sukayi saurin tareshi kamar dan jariri lokacin ya riga ya sume, a mota aka sashi da niyar kaishi asibiti………
Sai a lokacin Abby ya basu umarnin zuwa su duba abinda yake faruwa saidai suna zuwa sukaga Deen yayi jaming entrance door din, hankalin Abby ne ya tashi ganin suna jin hargowa har lokacin ga khaleel an cillo shi it means fatima zainab ce kawai a ciki da deen gata mace kuma, the only option daya rage musu shine a shiga ta pilot route amma akayi rashin saa pilot din daya tuka jirgin harya tafi, haka Abby yasa a ka kirashi a waya akace ya dawo yanzu yanzu, ko kafin ya dawo su samu su shiga Deen ya kusa balla kofar toilet din da take ciki………
Hakuri securities din Abby suka hau bashi akan karya balla kofar sai kawai ya nemi ya koma kansu daga ya mari wannan sai ya naushi wanchan, ganin kamar baya cikin hayyacinsa yasa sukayi maza sukaje suka fadawa Abby……
“Karki damu babu abinda ze miki ai ina nan, just open the door, I promise you babu abinda ze same ki, kinga bayanan yanzu ma”…….
Sai a lokacin taji zata iya daurewa tayi tsarki, tsarkin tayi ta bude kofa a hankali tana dan leke taga ko yana nan har lokacin, kallonta abby yayi cike da tausayi ganin yanda tayi tsilli tsilli da ido kamar an jijjiga saurayin bera a buta, abin dariya kamar ace fitt ta fita a guje……
Girgiza kai Abby yayi yace mata;
“Muje babu abinda ze miki kinji ko?”….
Daga masa kai tayi tana makale dashi har suka sauka……
Suna sauka idonta ya sauka cikin na deen dake tsaye yana mazurai idanunannan nasa sunyi wani iri, kanta yayi a haukace tayi maza ta bar kusa da Abby da sauri tayi hanyar fita daga landing area din sai dai kash a rufe yake tin bayan an budema pilot din ya dawo aka sake rufewa, zagaye suka hau yi kamar wasu yara su abby na tsaye suna kallon ikon Allah…….